"Mutuwar masu haƙar ma’adinai 33 a Neja abu ne da za a iya kauce wa" - Kwamitin bincike
Kwamitin da aka kafa domin bincikar mutuwar masu haƙar ma'adinai 33 da aka tsare a jihar Neja, ya ce sun mutu ne sakamakon cunkoso da rashin isasshiyar iska da kuma gazawar jami'an tsaro wajen kai musu agaji, kuma mutuwarsu musiba ce da za a iya kauce wa.
Shugaban kwamitin ya ce gwaje-gwajen likitoci sun nuna cewa mutanen sun mutu ne sakamakon sarƙewar numfashi bayan an kwashe lokaci ana tsare da su a cikin yanayi mara kyau, kuma tsananin zafi da rashin ruwa sun ƙara ta'azzara yanayin.
Ya ce binciken bai samu wata hujja da ke nuna cewa mutuwar ta samo asali ne daga wata annoba ko barkewar cuta ba.
Kwamitin ya gano cewa an tsare maza 50 a cikin ɗaki mai faɗin murabba'in mita 20 kacal, ba tare da ruwa mai gudana ko bayan gida mai aiki ba.
Haka kuma akwai ƙarancin abinci, ruwan sha da kuma iskar shaƙa.
Rahoton ya ce jami'an tsaro sun yi ta biris da kiraye-kirayen neman taimako da aka yi ta yi, duk da cewa wani ma'aikacin lafiya ya gargaɗe su kan mummunan yanayin da mutanen ke ciki.
Shugaban kwamitin ya bayyana tsare mutanen a matsayin cin zarafi, da wulakanci da ya saɓa wa haƙƙokin ɗan Adam.
Binciken ya kuma gano cewa wuraren haƙar ma'adinan da aka kai samame a kansu na da lasisin aiki, sannan an gudanar da samamen ba tare da umarnin ba.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Satumban 2026 lokacin da wasu da ake zargin masu haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba suka mutu a hannun Hukumar NSCDC a jihar Neja.