Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka yi jana'izar mutum 50 da suka mutu a harin ƴanbindiga a Taraba
Al'ummar Binnari da ke yankin ƙaramar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da bayyana alhininsu kan mutuwar fiye da mutum 50 sakamakon wani harin da ƴanbindiga suka kai garin a makon da ya gabata.
Ƴanbindiga sun kai hari hari ƙauyen ne jim kaɗan bayan sallar Juma'a, suna harbin kan mai uwa da wabi, tare da sace kayayyakin abinci da kuma ƙona shaguna da babura.
Ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen da BBC ta zanta da shi ya shaida cewa lamarin ya haifar da firgici da tashin hankali ga mazauna ƙauyen.
''Ba mu taɓa ganin tashin hankali da firgita irin wannan ba'', in ji mutumin da BBC ta zanta da shi ta wayar tarho.
Yadda lamarin ya faru
Mutumin ƙauyen ya shaida wa BBC cewa maharan sun zo garin ne a kan babura inda suka zarce kasuwar garin.
''Sun zo a kan babura aƙalla 150, inda kuma suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya firgita mutane'', in ji shi.
''Muna tsaka da cin kasuwa kwatsam, sai muka ji ƙarar harbe-harbe, nan take mutane suka figice inda wasu da dama suka riƙa faɗa wa cikin ruwan wani tafki da ke fegen kasuwar'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ci gaba da cewa maharan sun yi wa kasuwar ƙawanya ne kafin su fara auka da harbe-harben.
''Sun zagaye kasuwar ta kowace kusurwa, gabas da yamma, kudu da arewa ta ko'ina shiga kasuwar suke yi'', kamar yadda ya bayyana.
Mutumin ya ce da farko ya yi tsammanin cewa maharan za su tashi garin.
Mutum nawa aka kashe a harin?
Rundunar ƴansandan jihar ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin ya kai 48.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Victor Mshelizah, ya shaida wa BBC cewa adadin ya ƙaru ne biyo bayan gano ƙarin gawawwaki 23 a jiya Lahadi.
Ya ce binciken ƴan sanda ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su sun nutse ne a ruwa yayin da suke ƙoƙarin tsere wa maharan, yayin da aka kashe wasu a cikin dazukan da ke kusa da yankin.
To amma mazauna ƙauyen sun ce mutanen da suka mutu sakamakon harin ya zarta 50.
Mutumin ƙauyen da BBC ta zanta da shi ya ce mutanen da suka mutu a harin sun kai 52.
Zuwa yanzu dai babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin harin.
Jihar Taraba da sauran jihohin Najeriya na fama da hare haren ƴan bindiga da sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Yadda aka yi jana'izar waɗanda suka mutu
Tuni dai mazauna ƙauyen suka ce sun yi jana'izar gawarwakin da aka gano ya zuwa yanzu.
''Mun gabatar da jana'izar gaban jami'an tsaro bayan kammala tattara gawarwakin'', in ji shi.
Ya ce yanzu haka al'ummar ƙauyen an cikin jimami da alhinin abubuwan da suka faru.
''Wannan al'amari ya kaɗa mana hankali, tashin hankali ne da ba mu taɓa gani ba, kuma ba za mu taɓa mantawa da wannan al'amari ba'', in ji shi.
Ya ce yanzu suna zaune suna alhini, yayin da komai ya yi tsit, shiru ba kowa a garin.
''Yadda na shiga tashin hankali sakamakon harin har ta kai ina ganin abin cikin mafarkina'', in ji shi.