Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Na tsallake mutuwa': Yadda rikicin Kamaru ya ɗaiɗaita al'umma cikin shekaru 10
- Marubuci, Paul Njie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Ogoja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 10
Median Bah tana da shekara 15 kacal lokacin da rayuwarta ta sauya har abada.
Har yanzu tana iya tuna ranar da abin ya faru dalla-dalla, wato 7 ga Afrilun 2018. Ba ta da lafiya, kuma tana kwance a gadonta.
Wasu 'yan bindiga sun kutsa cikin gidansu da ke yankin Kudu maso Yammacin Kamaru, ɗaya daga cikin yankuna biyu na ƙasar da ake magana da Ingilishi, waɗanda suka kasance cibiyar rikicin neman ballewa daga ƙasar.
Median, wadda yanzu take da shekara 23, ta ce tana cikin barci mai nauyi lokacin da ɗan'uwanta ya tashe ta, cikin firgici sakamakon ganin yadda wasu gungun 'yan bindiga ke tunkararsu tare da harbi barkatai.
Ɗan'uwanta ya samu damar tserewa ta taga, amma ba ta kasancewa da sauƙi ga Median ba.
"Saboda ba ni da lafiya, ba ni da ƙarfin tsalle ta taga tare da shi. Don haka sai na bi ta ƙofa," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Sai dai wannan mataki ya jawo mata mummunan sakamako.
Ta ce ta yi ido biyu da wasu biyu daga cikin maharan a bayan gidan, waɗanda suka buɗe mata wuta.
Da farko sun harbe ta a cinyarta, kafin su ƙara harbe-harbe da dama, waɗanda suka yi wa fuskarta mummunar illa.
"Na ci gaba da roƙonsu kada su kashe ni, ina gaya musu cewa ba ni da lafiya. Amma sai na tsinci kaina a kwance a ƙasa," in ji ta.
Komai ya dusashe a gabanta. Ta suma, ta rasa gani da kuma ikon magana.
Da farko Median ta yi zaton mafarki take yi.
"Amma abin mamaki, sai na gane cewa gaskiya ne."
Harin ya janyo mata munanan raunuka a fuska. Ƙashin muƙamuƙinta ya lalace, yawancin haƙoranta sun farfashe, sannan wani babban ɓangare na bakinta ya samu mummunar illa.
A cikin shekaru takwas da suka gabata, an yi wa Median tiyatar gyaran fuska aƙalla sau huɗu a Kamaru, Ghana da Indiya, kuma ana sa ran za a ƙara yi mata wasu tiyatar a shekara mai zuwa.
An sake inganta sassan fuskarta ta amfani da ƙwayoyin nama da aka ɗauko daga wasu sassan jikinta.
Haka kuma, ta rasa ikon yin numfashi yadda ya kamata ta hanci da baki. Daga baya aka yi mata tiyatar buɗe wata kafa a wuyanta domin samun damar shigar iska zuwa bututun numfashi.
Tsawon shekaru takwas, ta dogara da wani bututu domin yin numfashi. Sai a kwanan nan aka cire bututun, wanda ya ba ta damar komawa yin numfashi yadda ya kamata.
Wata matashiya da aka yi wa mummunar illa a fuska, wata uwa da aka tilasta wa barin gidanta, da kuma wani ɗalibi da rikicin ya kawo cikas ga karatunsa. Kusan shekaru goma na faɗace-faɗace a Kamaru sun tarwatsa rayuwar mutane da dama.
Rikicin ya fara ne a watan Oktoban 2016, lokacin da lauyoyi da malamai a yankunan Kamaru masu magana da Ingilishi suka shiga yajin aiki, saboda zargin nuna wariya ga al'ummomin masu magana da Ingilishi daga gwamnatin ƙasar da masu magana da Faransanci suka mamaye.
Sun nuna damuwa kan naɗa alƙalai da malamai masu magana da Faransanci a kotuna da makarantu da ke yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma, waɗanda masu magana da Ingilishi suka fi yawa.
Da farko, zanga-zangar ta kasance cikin lumana, inda dubban mutane suka buƙaci a ƙara bai wa tsirarun masu magana da Ingilishi matsayi da kulawar da ta dace.
Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun zargi jami'an tsaro da amfani da ƙarfin da ya wuce kima wajen murƙushe zanga-zangar. Masu suka sun ce matakin da jami'an tsaro suka ɗauka ya taimaka wajen ruruta wutar ƙungiyoyin masu fafutukar ballewa da makamai.
A shekarar 2017, ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai guda 12 sun ɓullo, a cewar Ƙungiyar Rikice-rikicen Ƙasashen Duniya (International Crisis Group). Ƙungiyoyin na fafutukar samun 'yancin kai ga yankunan biyu masu magana da Ingilishi da kuma kafa sabuwar ƙasa mai zaman kanta da aka sanya wa suna Ambazonia.
Tun daga lokacin, mayaƙan masu neman ballewa sun shafe tsawon lokaci suna fafatawa da dakarun gwamnatin Kamaru, a wani rikici da ya yi ta'azzara a lokuta da dama.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun tattara bayanan take haƙƙin bil Adama da suka yi muni, waɗanda ɓangarorin biyu suka aikata.
An zargi mayaƙan masu neman ballewa da kashe mutane bisa zaɓe, yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, azabtarwa da kuma kai hare-hare kan makarantu da sauran kadarorin gwamnati da na masu zaman kansu.
A nasu ɓangaren kuma, an zargi jami'an gwamnatin Kamaru da kama mutane ba bisa ƙa'ida ba, tsare su, azabtarwa da kuma kashe mutane ba bisa doka ba.
Duk ɓangarorin biyu sun musanta zarge-zargen, duk da cewa a wasu lokuta sun amince da alhakin aikata wasu laifuka.
Rikicin ya yi mummunar illa ga al'ummomi, tare da tilasta wa mutane kusan rabin miliyan barin gidajensu, bisa bayanan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta wallafa a bana.
Aƙalla mutane 6,000 ne aka kashe tun bayan ɓarkewar rikicin, a cewar ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Human Rights Watch.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta ce sama da 'yan Kamaru 70,000 ne suka nemi mafaka a ƙasar Najeriya da ke maƙwabtaka da su.
Glory Akom, mai shekara 44, na fama da nakasa bayan ta tsira daga mummunan ƙunar da ta yi a wani lamari da ba shi da alaƙa da rikicin.
Matar mai 'ya'ya biyu yanzu tana zaune ne a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Ogoja, wani gari a jihar Cross River da ke kudu maso gabashin Najeriya, kusa da iyakar Kamaru.
Richard Effiong, na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR), ya shaida wa BBC cewa Ogoja na ɗauke da 'yan gudun hijira kusan 15,000 a sansanoni uku.
UNHCR ta samar wa 'yan gudun hijirar gidaje da aka gina da bulo, tare da rufin kwano.
Sai dai duk da haka, da dama daga cikinsu ba su san lokacin da za su koma gida ba, ko ma ko za su taɓa komawa.
Glory ta ce rayuwarta a Kamaru ta fi yadda take a yanzu. Tana gudanar da sana'arta, kuma tana iya ɗaukar nauyin iyalinta.
Amma komai ya sauya lokacin da faɗace-faɗacen suka tsananta a shekarar 2017.
Ta ce sojojin da aka tura yankin da take zaune a Kudu maso Yammacin ƙasar sun riƙa farautar mazauna yankin har cikin daji, lamarin da ya tilasta musu barin gidajensu da tserewa zuwa Najeriya.
"Mun kasance muna kwana a cikin daji, saboda kullum gudu muke yi," in ji ta.
"Idan ka kwana a gidanka, za su iya kashe ka a wurin."
Da farko ta zauna a wani ƙauye da ke maƙwabtaka da yankin, kafin daga bisani ta koma Ogoja, inda daga ƙarshe aka ware mata gida na dindindin.
Kamar sauran 'yan gudun hijira da dama, Glory ta dogara ne da tallafin kuɗi na dala 67, kwatankwacin fam 51, da UNHCR ke ba ta duk wata domin kula da 'ya'yanta. Ɗaya daga cikinsu na fama da cutar sikila, kuma yana buƙatar kulawar likitoci akai-akai.
Ta ce kuɗin ba su isa su biya bukatun abinci, kuɗin jinya da sauran abubuwan buƙata ba.
Baƙin cikin da Glory ke ji na barin gidanta ya yi daidai da na sauran 'yan gudun hijirar Kamaru da ke Ogoja waɗanda suka zanta da BBC.
Maurine Mangha, mai shekara 21, ta ce ita da wasu mutum biyar daga cikin iyalinta sun tsere daga Akwaya da ke yankin Kudu maso Yammacin Kamaru, bayan mayaƙan masu neman ballewa sun buɗe wuta a lokacin bikin murnar abin da suka kira samun 'yancin kansu, a ranar 1 ga Oktoban 2017.
"Sun harbi mutane da yawa, kuma ba mu da wani zaɓi illa mu tsere zuwa cikin daji," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Maurine ta daina zuwa makaranta watanni da dama kafin hakan, sakamakon dokar kauracewa karatu da 'yan aware suka kakaba.
Gangamin kauracewa karatu da aka fara a shekarar 2017 domin matsa wa gwamnati lamba, ya haɗa da barazana da kai hare-hare kan makarantu da kuma waɗanda suka bijire wa umarnin hana zuwa makaranta.
Hakan ya yi mummunar illa ga yara.
A halin yanzu, yara sama da 200,000 ba sa zuwa makaranta a yankunan da rikicin ya shafa, yayin da kusan makarantu 2,500 suka daina aiki a yankunan biyu, a cewar hukumar kula da yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), wadda ta samo alkaluman daga hukumomin ilimi na Kamaru.
Duk da wannan cikas, Maurine ta samu tallafin karatu ta wani shirin bayar da ilimin manyan makarantu ga 'yan gudun hijira da UNHCR ke gudanarwa.
Yanzu tana karatun kimiyyar ƙwayoyin halitta a wata makarantar kimiyya da fasaha da ke yankin.
Sai dai Maurine ta ce ba ta iya daina tunanin abokan karatunta da suka rage a Kamaru.
"Abokan nawa suna ba ni tausayi sosai saboda ba su samu damar ci gaba da karatunsu ba sakamakon rikicin," in ji ta.
Bayan kusan shekaru goma ana gwabza faɗa, gwamnatin Kamaru na son mayaƙan neman ballewa su ajiye makamansu.
A watan Satumba, hukumomi sun ƙaddamar da wani shirin tattaunawa da al'umma domin nemo hanyoyin warware rikicin daga tushe.
Firaminista Joseph Dion Ngute ya ce yayin ƙaddamar da shirin a Buea, babban birnin yankin Kudu maso Yamma: "Ku ne, dukkanmu da muke zaune a nan, za ku iya shirya tattaunawa da waɗannan samarin [mayaƙan neman ballewa], ku gaya musu cewa lokaci ya yi da za su ajiye makamansu."
Ya sake yin irin wannan kira a Bamenda, babban birnin yankin Arewa maso Yamma kuma ɗaya daga cikin wuraren da rikicin ya fi kamari.
A wajen tarukan biyu, an gabatar da kusan mutum 60 da aka bayyana a matsayin tsoffin mayaƙan neman ballewa, waɗanda suka ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga gwamnati.
Wani jami'in Kamaru da ke kula da shirin ya shaida wa BBC cewa, ya zuwa watan Nuwamban 2026, kusan tsoffin mayaƙa 1,500 ne ke samun horo da tallafin sake shiga cikin al'umma a cibiyoyin DDR da ke yankunan biyu masu magana da Turanci.
Duk da cewa irin wannan shiri da aka ƙaddamar a 2019 bai yi nasarar kawo ƙarshen faɗan ba, gwamnati na fatan shawo kan ƙarin mayaƙa su ajiye makamansu su daina fafutukar neman 'yancin kai.
"An kashe mayaƙan Amba da dama, wasu sun miƙa wuya, yayin da da yawa suka yi watsi da akidar neman 'yancin kai," in ji Clovis Naseri, wani tsohon kwamandan 'yan aware.
Clovis ya shafe kusan shekara biyu tare da ƙungiyar mayaƙan White Tigers of Ribbons, wadda ke aiki a yankin Kudu maso Yamma, kafin ya fice daga cikinta a 2019.
Daga nan aka kai shi wata cibiya ta sake shigar da tsoffin mayaƙa cikin al'umma, inda ya kwashe shekaru yana samun kulawar gyaran hali.
A yanzu, ya zama mai sukar ƙungiyoyin neman ballewa, kuma yana kira da a samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Duk da ficewar wasu mayaƙa daga ƙungiyoyin da kuma ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa su su miƙa wuya, ƙungiyoyin masu neman ballewar na ci gaba da kai hare-hare a yankunan biyu.
Wasu manazarta na ganin cewa rikicin ya daɗe saboda, a wani ɓangare, gazawar gwamnati wajen magance korafe-korafen da suka haddasa shi.
Roland Fru, wani mai bincike kan rikicin yankunan masu magana da Turanci, ya ce har yanzu hukumomi ba su nuna cewa sun fahimci ainihin matsalolin da ke haddasa rikicin ba.
"Ban taɓa jin gwamnati ta yi bayani ko sau ɗaya ta yadda zai nuna mini cewa ita ma ta fahimci matsalar ba," in ji shi.
BBC ta tuntuɓi jami'an gwamnati da dama domin jin ta bakinsu, amma ba ta samu amsa ba.
Hukumomin Kamaru sun sha yin watsi da sukar da ake yi wa yadda suke tafiyar da rikicin.
A watan Nuwamban bara, Shugaba Paul Biya ya ce ƙoƙarin sake gina yankunan da rikicin ya shafa, tare da taimakon ƙasashen duniya, na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya.
"Za mu ci gaba da waɗannan ƙoƙarin a kai a kai," in ji shi a lokacin bikin rantsar da shi, inda ya kuma yaba wa jami'an tsaro kan "ingantattun matakan da suke ɗauka" da kuma "ƙwarewarsu" wajen inganta yanayin tsaro.
Sai dai ga waɗanda suka tsira daga rikicin kamar Median, Glory da Maurine, dawwamammen zaman lafiya na iya ci gaba da zama abu mai nisa matuƙar ba a kawo ƙarshen faɗan gaba ɗaya ba.
Yayin da suke ƙoƙarin sake gina rayuwarsu da kuma riƙe fata, Median, wadda har yanzu take zaune a Kamaru, ta ce tana godiya da ta tsira.
"Na yi nasara a kan mutuwa," in ji ta cikin ƙarfin gwiwa. "Ba na tunanin akwai abin da zai iya dakatar da ni."
Ƙarin rahoto daga Michel Mvondo