Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohi 7 da APC ke fama da rikicin cikin gida gabanin zaɓen 2027
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci shugabannin jam'iyyar APC mai mulki da su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, su yafewa juna tare da rungumar sulhu, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Kiran na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke fama da rikice-rikicen cikin gida a wasu jihohin ƙasar, waɗanda suka haɗa da rikicin shugabanci, takarar gwamna, zaɓen fidda gwani da fafatawar neman ikon tafiyar da jam'iyyar.
Tinubu ya yi wannan kira ne yayin wani zaman addu'a na musamman da 'yan uwansa suka shirya masa a ƙungiyar Yoruba Tennis Club da ke Legas.
Shugaban ƙasar ya umarci mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Masari, da tsohon Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, da su jagoranci ƙoƙarin sulhunta shugabannin jam'iyyar da ke da saɓani.
Sai dai waɗanne jihohi ne APC ke fuskantar irin waɗannan matsaloli, kuma mene ne tushen rikice-rikicen?
1. Katsina: Rikicin Dikko Radda da Ibrahim Masari
A jihar Katsina, rikicin cikin gida na APC ya fi bayyana tsakanin Gwamna Dikko Umaru Radda da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya ta'allaka ne kan fafatawar neman tasiri da ikon tafiyar da jam'iyyar a jihar, inda aka samu ɓangarori biyu masu biyayya ga Radda da Masari.
Wannan rikici ne ya sa Tinubu ya umarci Masari da ya koma jiharsa domin sulhunta dukkan masu saɓani.
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa dole ne a kawar da duk wani fushi da ke tsakanin 'yan jam'iyyar domin su haɗa kai gabanin zaɓen 2027.
2. Jigawa: Rikicin Namadi da Badaru
A jihar Jigawa ma, ana ganin akwai saɓani tsakanin Gwamna Umar Namadi da wanda ya gada, tsohon gwamna kuma tsohon Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, duk da cewa dukansu 'yan jam'iyyar APC ne.
Rikicin ya kai ga korar wasu jami'an gwamnati da ake zargin amintattun tsohon gwamnan, Badaru, ne, domin kauce wa abin da gwamnan ya kira "kitso da kwarkwata".
Magoya bayan ɓangarorin biyu sun sha yin musayar kalamai da sukar juna, abin da ke ƙara nuna yadda saɓanin ke shafar haɗin kan jam'iyyar.
Sai dai umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Badaru na jagorantar ƙoƙarin sasanta 'yan APC da ke da saɓani ya sake jawo hankali kan halin da jam'iyyar ke ciki a Jigawa.
3. Neja: Rikicin Bago da Abubakar Sani Bello
A jihar Neja, rikicin cikin gida na APC ya shafi rashin jituwa tsakanin Gwamna Mohammed Umaru Bago da wasu jiga-jigan jam'iyyar, ciki har da wanda ya gada, tsohon gwamna Abubakar Sani Bello.
Tun bayan da Bago ya karɓi mulki a shekarar 2023, ana ta samun rahotannin saɓani tsakanin magoya bayan gwamnan da na tsohon gwamnan, musamman kan yadda ake tafiyar da harkokin jam'iyyar a jihar da kuma tasirin siyasa.
Wannan saɓani ya haifar da rashin gamsuwa tsakanin wasu mambobin jam'iyyar, inda wasu suka nuna fushinsu tare da barazanar sauya sheƙa.
A ƙoƙarin shawo kan matsalar, Bago ya gana da wasu jiga-jigan APC daga ƙananan hukumomi 25 na jihar domin lalubo bakin zaren rikicin da kuma ƙarfafa haɗin kan jam'iyyar.
4. Osun: Rikicin APC bayan rashin nasara a zaɓen gwamna
A jihar Osun, jam'iyyar APC na fuskantar rikicin cikin gida bayan kayen da ta sha a zaɓen gwamnan jihar na ranar 15 ga Agustan 2026, inda Gwamna Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord ya samu ƙuri'u 511,067, yayin da ɗan takarar APC, Bola
Rashin nasarar ya sake fito da saɓanin da ke tsakanin manyan jiga-jigan jam'iyyar, musamman tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, Sakataren APC na ƙasa, Ajibola Basiru, da tsohon mataimakin gwamna, Iyiola Omisore.
Wasu daga cikin mambobin jam'iyyar sun zargi Oyetola da mamaye harkokin APC a jihar, musamman wajen zaɓen 'yan takara da rabon muƙaman siyasa, lamarin da suka ce ya jawo wasu jiga-jigai da magoya bayansu suka nuna rashin gamsuwa.
Shugaba Bola Tinubu ya sha ganawa da jagororin jam'iyyar a jihar, inda ya ke kira ga shugabannin APC na Osun da su ajiye saɓaninsu tare da haɗa kai.
5. Benue: Rikicin Alia da Akume kan ikon tafiyar da APC
A jihar Benue, rikicin cikin gida na APC ya fi bayyana tsakanin Gwamna Hyacinth Alia da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, wanda ya taɓa zama gwamnan jihar.
Rikicin ya kai ga gudanar da zaɓukan shugabannin APC na jiha daban-daban a watan Maris na 2026. Ɓangaren Alia ya zaɓi Benjamin Omale a matsayin shugaban jam'iyyar na jiha, yayin da ɓangaren Akume ya sake tabbatar da Austin Agada a wannan muƙami. Hakan ya haifar da shugabancin jam'iyya iri biyu da kuma gudanar da harkokinta daga ofisoshi daban-daban a Makurdi.
Gwamna Alia ma ya zargi wasu shugabannin jam'iyyar da son mayar da jihar tamkar kadararsu ta kashin kai, yana mai cewa rikicin ya samo asali ne daga ƙin amincewarsa da rabon kuɗaɗen gwamnati ga wasu jiga-jigan APC. Sai dai bai ambaci sunayensu ko ya gabatar da cikakkun bayanai kan zargin ba.
6. Oyo: Saɓani kan ɗan takarar gwamna
A jihar Oyo, rikicin ya samo asali ne daga rashin gamsuwar wasu jiga-jigan APC da sakamakon zaɓen fidda gwani na takarar gwamna.
Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da magoya bayansa sun nuna rashin amincewa da yadda Sharafadeen Alli ya samu tikitin takarar gwamnan jihar na 2027.
Sai dai jam'iyyar ta fara ƙoƙarin sasanta ɓangarorin, inda a watan Agustan 2026 aka sanar da cewa an yi sulhu tsakanin Alli da wasu 'yan takara huɗu da suka nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen.
7. Nasarawa: Rikicin gwamna Sule da masu neman takara
A jihar Nasarawa, APC na fuskantar saɓani tsakanin Gwamna Abdullahi Sule da wasu jiga-jigan jam'iyyar da ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani ba.
Ɗaya daga cikin manyan dalilan rikice-rikicen shi ne takarar gwamna, inda wasu 'yan takara suka nuna rashina mincewarsu da yadda aka gudanar da zaɓen da ya samar da Sanata Ahmed Wadada a matsayin ɗan takarar da Gwamna Sule ya fi goyon baya.
Gwamna Sule da kansa ya amince cewa APC na fuskantar ƙalubalen rashin haɗin kai a Nasarawa, Benue da Kwara, yana mai cewa saɓanin kan 'yan takara na iya shafar goyon bayan jam'iyyar a zaɓen 2027.