Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin za a iya kauce wa rikicin siyasa gabanin zaɓen Najeriya na 2027?
Yayin da Najeriya ke shirin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027, ana ƙara nuna damuwa kan yadda rikicin siyasa, barazana da hare-hare kan 'yan takara da magoya bayansu ke ƙara zama abin fargaba a wasu sassan ƙasar.
Daga kai wa motocin 'yan takara hari zuwa tarwatsa tarukan siyasa da amfani da makamai wajen tsoratar da magoya bayan jam'iyyun hamayya, abubuwan da ke faruwa na sake jawo tambayoyi kan ko ƙasar za ta iya gudanar da zaɓe cikin lumana.
A cikin hare-haren da suka jawo hankalin jama'a akwai wanda aka kai wa tawagar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege, a jihar Delta, inda rahotanni suka ce mutane huɗu sun mutu, wasu kuma suka jikkata.
Omo-Agege ya yi zargin cewa maharan sun riƙa ambaton sunansa tare da bayyana cewa suna son kashe shi, yayin da suka buɗe wuta kan tawagarsa.
Sai dai, shin mene ne ke haddasa rikicin siyasa a Najeriya? Wace rawa hukumomin tsaro za su taka wajen dakile matsalar? Kuma shin akwai yiwuwar hana aukuwar irin waɗannan hare-hare kafin ranar zaɓe?
Menene tushen matsalar?
Rikicin siyasa ba sabon abu ba ne a Najeriya. A tsawon shekarun da ƙasar ke gudanar da zaɓe a ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya, an sha samun rahotannin tashin hankali, barazana da hare-hare da suka shafi 'yan takara da magoya bayan jam'iyyun siyasa.
Masu nazarin harkokin siyasa na danganta matsalar da abubuwa da dama, ciki har da yadda ake fafatawa wajen neman mulki, da raunin tsarin shari'a, da amfani da kuɗi wajen siyasa da kuma yadda wasu 'yan siyasa ke amfani da matasa wajen cimma burinsu.
Wannan yanayi na iya ƙara tsananta idan 'yan siyasa suka ɗauki abokan hamayyarsu a matsayin maƙiya, maimakon abokan fafatawa a tsarin dimokuraɗiyya.
Haka kuma, amfani da matasa wajen tayar da rikici na daga cikin abubuwan da ke ƙara dagula harkokin siyasa. Wasu daga cikin matasan kan shiga irin waɗannan ayyuka saboda matsalar rashin aikin yi, talauci ko kuma samun kuɗi daga waɗanda ke amfani da su.
''Abu ne mai yiwuwa idan kowa ya ba da gudummawa''
Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting kuma masani kan harkokin tsaro, ya ce akwai yiwuwar hana rikicin siyasa gabanin zaɓen 2027, matuƙar gwamnati, da 'yan siyasa da hukumomin tsaro suka haɗa kai wajen ɗaukar matakan da suka dace.
A wata hira da BBC, Adamu ya jaddada cewa tabbatar da tsaron zaɓe ba nauyin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro kaɗai ba ne, sai dai yana buƙatar gudummawar dukkan masu ruwa da tsaki.
''Akwai buƙatar su ƴansiyasa su iya bakinsu, su kuma magoya baya su daida iza wuta, sannan idan an saɓa doka ya kamata su kuma jami'an tsaro su yi nasu aikin don tabbatar da doka da oda''
Ya bayyana cewa sahihancin zaɓe yana da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron ƙasa, da ƙarfafa amincewar jama'a ga hukumomi da kuma tabbatar da halaccin gwamnati.
Dangane da shirye-shiryen zaɓen 2027, Adamu ya yi gargaɗin cewa dole ne hukumomin tsaro su yi la'akari da bambancin matsalolin tsaro da ake fuskanta a sassan Najeriya.
''Dole ne 'yan siyasa su iya bakinsu''
A nasa ra'ayin, Farfesa Abubakar Kari, masanin harkokin siyasa a Jami'ar Abuja, ya ce akwai buƙatar 'yan siyasa su taka muhimmiyar rawa wajen hana rikicin siyasa gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027, musamman ta hanyar taka-tsantsan wajen furta kalamai da kuma yadda suke gudanar da fafatawar neman mulki.
Ya bayyana cewa dole ne 'yan siyasa su fahimci irin tasirin kalamansu ga magoya bayansu, domin wasu kalamai na iya tunzura jama'a, ƙara rura wutar rikici da kuma haifar da gaba tsakanin masu goyon bayan jam'iyyun siyasa daban-daban.
A cewarsa, ya kamata shugabannin siyasa su guji kalaman batanci, da barazana da kuma furucin da zai iya sa magoya bayansu kallon abokan hamayya a matsayin maƙiya.
Ya kuma bayyana muhimmancin ƴan siyasa su riƙa jan hankalin magoya bayansu, musamman matasan da ake yawan amfani da su a lokacin yaƙin neman zaɓe wajen tayar da hankali, da tarwatsa tarukan siyasa ko tsoratar da abokan hamayya.
Farfesan ya nuna cewa alhakin tabbatar da zaman lafiya bai rataya a wuyan jami'an tsaro kaɗai ba, domin shugabannin siyasa ma suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da cewa fafatawar neman mulki ba ta rikide zuwa tashin hankali ba.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata 'yan siyasa su koyi mutunta ra'ayoyin abokan hamayyarsu, tare da fahimtar cewa neman mulki ta hanyar dimokuraɗiyya na nufin karɓar cewa za a iya yin nasara ko rashin nasara.
A cewarsa, idan shugabannin siyasa suka nuna kishin zaman lafiya ta hanyar kalamansu da ayyukansu, hakan zai taimaka wajen rage tunzura magoya baya da kuma samar da yanayin da kowa zai iya shiga harkokin siyasa cikin aminci.