Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashen Afirka 10 mafiya zaman lafiya a 2026
Yayin da rikici, kashe-kashe da kungiyoyin masu dauke da makami da kuma rikicin siyasa ke ci gaba da zagon kasa ga zaman lafiya a fadin duniya, wasu kasashen Afirka sun samu nasarar shiga cikin jerin kasashen duniya da suka fi zaman lafiya a duniya.
Zaman lafiya na kara yin karanci a duniya, inda yake ci gaba da raguwa a shekara 15 a jere cikin shekara 18, kamar yadda rahoton zaman lafiya na duniya na shekara ta 2026 ya nuna, wanda cibiyar Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki da zaman Lafiya ta duniya ta wallafa.
Rahoton ya gano cewa zaman lafiya ya yi kasa da gwargwadon kashi 0.7% a cikin shekara daya da ta gabata, wanda hakan ya nuna cewa zaman lafiyar duniya ya ragu karo na 12 a jere.
Yakin da ake fama da shi a Sudan da Ukraine da Myanmar da kuma yankin Sahel da yadda ake samun zaman tankiya tsakanin kasashen duniya da kuma makudan kudade da ake kashewa a fannin tsaro na ci gaba da kawo cikas ga zaman lafiya a duniya.
A 2025 kawai, an kashe mutum sama da 181,000 a rikice-rikicen da ake fama da su a fadin duniya, yayin da mutanen da rikici ya tarwatsa daga muhallansu sun zarce miliyan 117.
Kisan mutane sanadiyyar rikice-rikicen cikin gida a kasashen duniya ya yi karuwar da ba a taba samu ba tun bayan fara fitar da rahoton, bisa la’akari da kazamin rikicin da ake fama da shi a Sudan da wasu yankunan.
A nahiyar Afirka ana cikin yanayi na tir-madalla.
Yayin da wani bangare ke ci gaba da fama da matsalar ta’addanci, da kungiyoyin ‘yan tayar da kayar baya da kuma rikici mai nasaba da siyasa, wasu kasashen na ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya.
Lokacin da ya tattauna da mujallar Business Insider Africa, Thomas Morgan, jami’i a Cibiyar nazarin tattalin arziki da zaman lafiya kuma daya daga cikin mutanen da suka fitar da jerin Kasashen da suka fi zaman lafiya a duniya, ya ce ya kamata mahukunta a yankin Sahel su sanya ido sosai kan tasirin yakin Iran ga harkar tsaro a yankin, maimakon mayar da hankali kawai kan ayyukan ta’addanci.
”Akwai wani abu guda daya da bai riga ya bayyana ba, kuma za mu sanya ido cikin wata uku zuwa wata shida masu zuwa, wato tasirin da yakin Iran zai yi,” kamar yadda Morgan ya sanar da mujallar Business Insider Africa.
“Nan da wata shida za mu ga cikakken tasirin yakin Iran, za a fara ganin tasirin ne a Afirka.” In ji shi.
Wane hali zaman lafiya ke ciki a Afirka?
Yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara ya fuskanci tabarbarewar zaman lafiya a 2026, inda zaman lafiya ya ragu da kashi 0.2%.
Yanzu haka yankin ya kunshi kasashe 8 cikin 20 wadanda suka fi fama da rikici a duniya, wanda hakan kari ne idan aka kwatanta da kasashe 5 marasa zaman lafiya a yankin a shekara ta 2008, wanda hakan ke nuni da tasirin rikice-rikice, musamman ma a kasashen da ke tsakiyar Sahel.
Sai dai duk da wannan kalubale, wasu kasashen na ci gaba da kokarin ganin an tabbatar da zaman lafiya fiye da wasu, inda suke cin gajiyar daidaiton harkokin siyasa, rashin yawaitan aikata laifuka, gwamnati mai inganci da kuma karancin ayyukan masu dauke da makamai.
Mauritius ta kare kambinta na kasancewa kasa mafi zaman lafiya a Afirka, kuma ita ce ta 18 cikin jerin kasashe mafiya zaman lafiya a duniya, inda take gaba da dukkanin kasashen Afirka,
Kasar wadda ta kasance tsibiri, na cin gajiyar kwakkwaran shugabanci da hukumomi masu aiki yadda ya kamata da kuma rashin tashe-tashen hankali a cikin gida.
Equatorial Guinea ce kasa ta biyu mafi zaman lafiya a Afirka, kuma ita ce ta 38 a jerin kasashe mafiya zaman lafiya a duniya.
Botswana ma ta kare martabarta ta kasancewa kasa mai cike da zaman lafiya da kyakkyawan jagoranci, inda ta zama kasa ta uku mafi zaman lafiya a Afirka.
A yammacin Afirka akwai kasashe kamar:
- Gambia
- Saliyo
- Senegal
- Ghana
Wadannan kasashe sun samu kasancewa cikin 10 mafiya zaman lafiya a Afirka duk kuwa da matsalolin tsaro da ke fuskantar yankin kudancin na Afirka.
Matsalar tsaro a Afirka
Morgan ya ce duk da cewa a karon farko cikin shekaru da dama, mutanen da ke mutuwa sanadiyyar ayyukan ta’addanci ya ragu a Sahel a shekara ta 2025, amma har yanzu yankin shi ne ke da rabin adadin mutanen da ke mutuwa sanadiyyar ayyukan ta’addanci a duniya.
A yankin, kungiyoyi irin su JNIM na rikidewa daga ‘yan tayar da kayar baya zuwa masu iko da maka-makan yankuna tare da kakaba takunkumai.
“Alamu na nuna cewa a yanzu JNIM na da isasshen fili a karkashin ikonta wanda zai ba ta damar sauya dabarar yaki da kakaba takunkuman tattalin arziki da kuma hana shigar da man fetur zuwa kasar Mali,” in ji Morgan.
Morgan ya ce kasashen Sahel sun kaurace wa kawayensu na asali a bangaren tsaro, kamar Amurka da Faransa, inda suka karkata zuwa ga Rasha, wadda ta fi mayar da hankali wajen kare gwamnati a maimakon yaki da ta’addanci, wani abu da masana ke ganin cewa ya taimaka wajen karuwar ayyukan masu tsattsauran ra’ayi a Jamhuriyar Nijar.
Morgan ya ce dakarun da ke samun goyon bayan Rasha sun fi mayar da hankali wajen kare gwamnati a maimakon yaki da kungiyoyi masu dauke da makamai.
Jerin kasashen ya nuna cewa yayin da rikice-rikice da rashin tsaro ke ci gaba da zamewa babbar matsala a kasashen Afirka da dama, kasashen da ke cike da zaman lafiya na ci gaba da zama kyakkyawan misalin jagoranci nagari da juriya a duniya mai cike da rashin tabbas.