An kama jami’an gwamnatin Iraq 47 bisa zargin rashawa
Hukumomin tsaro a ƙasar Iraq sun kama jami’an gwamnati da ƴan siyasa 47, ciki har da ‘yan majalisar dokoki, a wani samame da suka kai domin yaƙi da rashawa.
An gudanar da wannan farmaki ne a yankin Green Zone da ke Baghdad, wurin da ake tsaurara tsaro sosai a babban birnin ƙasar.
Rahotanni sun ce wannan mataki na daga cikin sabuwar ƙudirin yaƙi da rashawa da firaministan ƙasar Iraq na yanzu, Ali Zaidi ke jagoranta.
Tun da farko ma an kama mataimakin ministan man fetur, Adnan Jalili.
Wani jami’i a gwamnatin Iraq da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa ana zargin waɗanda aka kama da laifuka ciki har da wawure dukiyar gwamnati da safarar dala da kuma man fetur ba bisa ƙa’ida ba.