Milan na gogayya da 'yan Firemiya kan Summerville, Madrid za ta sayi Dumfries

Asalin hoton, Getty Images
AC Milan ta zama kungiyar da ke kan gaba wajen neman sayen danwasan gaba na gefe na West Ham Crysencio Summerville, mai shekara 24, duk da cewa kungiyoyin Firemiya - Tottenham da Aston Villa su ma suna son danwasan na Holland. (Teamtalk)
Ana sa ran Real Madrid za ta bayyana bukatarta ta neman sayen dan baya na gefen dama na Inter Milan, Denzel Dumfries, dan kasar Holland mai shekara 30, wanda kwantiraginsa ya tanadi duk kungiyar da ke son sayenshi sai ta biya fam miliyan 17.3 (Sky Sports)
Newcastle ta gabatar da tayin yuro miliyan 24 (fam miliyan 20.7) domin sayen matashin dan gaba na gefe dan Najeriya, Zadok Yohanna mai shekara 18 na kungiyar AIK Stockholm ta Sweden (Expressen)
Atletico Madrid na sha'awar sayen danwasan tsakiya na Manchester City da Holland Tijjani Reijnders, mai shekara 27. (Fichajes)
Kieran McKenna da Thomas Frank su ne kan gaba a masu horar da 'yanwasa da ake ganin za a zaba domin maye gurbin kociyan Fulham Marco Silva, wanda shi kuma zai tafi domin maye gurbin Jose Mourinho a Benfica, idan Mourinho din ya tafi Real Madrid. (Talksport)
Manchester United ta dakatar da tattaunawa kan kwantiragi da Bruno Fernandes, mai shekara 31, bayan da kungiyar ta samu tabbacin cewa danwasan na tsakiya dan Portugal kuma kyaftin dinta yana son ci gaba da zama a Old Trafford zuwa wani dogon lokaci. (Mirror)
Atletico Madrid ka iya amfani da makudan kudaden da za ta iya samu idan ta sayar da dan gabanta na Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, ta sayi dan gaban Marseille da Ingila Mason Greenwood, mai shekara 24. (Fichajes)
Ita ma Roma tana da son Greenwood, wanda tsohuwar kungiyarsa - Manchester United za ta amfana da cinikin da ya kai shi Faransa. (Teamtalk)
Everton na son sayen danwasan gaba na Arsenal Gabriel Jesus, na Brazil, mai shekara 29, amma kuma tana son zakarun na Firemiya su rage farashin da suka yi masa na fam miliyan 20. (Football Insider)
Sunderland na fatan ganin ta yi galaba a kan Marseille, wajen sayen danwasan tsakiya na kungiyar Charleroi ta Belgium, Yassine Titraoui, dan Algeria mai shekara 22. (FootSur7 )
Paris St-Germain na son yuro miliyan 30 (fam miliyan 25.9) daga Juventus, a kan dan wasan gaba na Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 27. (La Gazzetta dello Sport )











