Abin da ya sa gwamnatin Zamfara ta hana al'umma sulhu da 'yanbindiga

Asalin hoton, Dauda Lawal/Instagram
A Najeriya, gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin kasar ta gargadi al'ummar jihar game da yin sulhu da yanbindiga masu garkuwa da mutane.
Gwamnatin ta ce duk wanda ya yi sulhu da yanbindiga ya yi gaban kansa tare da nanata cewa ba za ta yi sulhu da yan fashin daji da suka addabi jihar ba.
Gwamnatin ta kara jaddada hakan ne bayan wasu dattawa a yankin Maradun kusan 40 sun kubuta daga hannun yanbindiga bayan sun je yin sulhu da yanbindigan.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban karamar hukumar Talatar Mafara, Yahaya Abubakar Yari, ya ce: Sulhu ana yinsa ne da mutanen da misali suka yi tawaye saboda wasu bukatu nasu na neman 'yanci wanda hakan har ya kai su ga daukar makami.
''To wadannan idan an je an yi sulhu da su cewa su ajiye makami. Mene ne aka yi musu? Da me da me suke so a yi musu? Kuma idan an yi musu, an wuce wurin, za a ci gaba da zama lafiya da su, to irin wadannan mutanen su ne ake sulhu da su.''
Ya kara da cewa: ''Misali kamar 'yan tawayen kasar Kolombiya. Ai ka ga suna fada ne a kan yanki da kuma wasu bukatu na ayyuka da gwamnati ba ta yi a yankinsu. To tun lokacin da aka zauna aka yi sulhu da su, kuma gwamnati ta biya bukatun, ai ka ga sun ajiye makaman.''
Alhaji Abubakar, ya ce da a ce su ma 'yanbindigan na Zamfara da suna da wata manufa da bukata wadda suke son gwamnati ta yi musu, kuma idan aka yi musu an wuce matsalar, ya ce to da sai a yi sulhu da su.
Shugaban ya ce: ''Su wadannan ba su da wata manufa illa a kona gidaje, a kashe mutane, a kwashi dukiya, a kwashi dabbobi shikenan. To ya za ka yi sulhu da wanda yake da irin wannan?''
Dangane da yadda ake ganin gwamnati ta kasa magance matsalar tare da bayar da kariya ga al'umma, sai shugaban karamar hukumar, ya ce, ai idan gwamnati ta saka ka'ida, domin su jama'ar ba su ke shugabantar kansu ba to ya kamata su bi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya yi nuni da yadda, ya ce a baya idan aka yi rigima da barayin dajin, sukan kai hari har su tashi kauyuka duka, ko kuma 'yanbindigan su kame hakiman garuruwan su daure, amma yanzu ya ce barayin ba sa iya haka.
''To yanzu kuma gwamnati ta ce, a'a, na yarda ku fito ku kare kanku idan sun zo wurinku. Kuma ni ba zan yi sulhu da su ba. To da wannan dama da gwamnati ta bayar, ai ta magance rabin matsalar,'' in ji shi.
Kan yadda ake ganin an yi sulhu da 'yanbindigan a wasu jihohi makwabta irin su Katsina, Alhaji Yahaya ya ce ai wannan sulhu da aka yi ba abin da ya haifar na magance matsalar.
''A inda aka yi sulhun da su, me sulhun ya haifar? Ba sun kashe Janaral ba, suka kawo gawarshi tsakiyar gari, duk kuma da an yi sulhun?''
''Ba suna daukar mutane a kauyuka ba har yanzu? Ba a kan hanya suka dauki Janaral suka tadfi da shi jeji ba? A Katsina ne fa aka yi sulhun, kuma ga abin da ya haifar a sulhun Katsina din.''
Shugaban na karamar hukumar ta Mafara, ya ce gwamnan jihar ya ce shi ba zai yi sulhu ba kuma baiyarda a yi sulhu da 'yanbindigan ba, sannan duk wanda ya yi sulhu da su to ya yi gaban kansa ne.
''Mai girma gwamna ya ce shi tsakaninsa da 'yanbindiga sai yaki kawai kuma mu ma shugabannin kananan hukumomi a kan haka muke, kuma a kan haka za mu tafi, in sha Allah.''
Sai dai dangane da yadda ake ganin manoma ba sa iya zuwa gonakinsu, ya ce, a'a manoma na zuwa gonakinsu aiki a wasu sassan jihar lami lafiya, illa dai ba za a iya cewa ko'ina ana zaune lafiya ba, ba kuma za a ce ko'ina ana yaki ba.











