Yadda ƴan fashin daji suka halaka mutane 18 a jihar Zamfara

'Yan fashin daji

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, 'Yan fashin daji
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Jama'a a garin Goro-Namaye da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, na ci gaba da alhinin mutuwar wasu mutane goma shatakwas da 'yan fashin daji suka halaka yayin wani mummunan farmaki da suka kai a ranar Juma'a da safe.

Bayanai sun ce yan fashin dajin sun so shiga garin ne da duku-dukun safiya amma sai jama'a suka tare su, lamarin da ya sa suka koma dazukan da ke kewaye da garin, kana suka farwa manoma da ke aikin gona.

Shugaban karamar hukumar ta Maradun Sunusi Ahmad Dosara ya shaida wa BBC Hausa cewa yawancin mutanen manoma ne da mata da kananan yara.

Ya kara da cewa dama jama'ar garin sun jima suna takun-saka da 'yan fashin dajin sakamakon hana su shiga garin a duk lokacin da suka so kai farmaki.

''A halin da ake ciki yanzu mutanen wannan gari suna cikin shirinsu, kuma ko da muka je wajen Jana'iza sun dage kan cewa lallai in dai suna raye ba za su bar 'yan fashin daji su shiga garinsu ba'' inji shi.

Shugaban karamar hukumar ya jaddada yin kira ga mahukunta su tashi tsaye wajen tunkarar yan fashin dajin a inda suke maimakon jiran sai sun kai hari sannan a tare su.

''Mafita guda daya ce, suna da mafaka barayin nan kuma an san mafakarsu, don haka muddin ba mafakar nan ta su aka tarwatsa ba, to ina tabbatar maka da cewa wannan abu sai dai kullum a ce gwamma jiya da yau, domin ko da za a zo sun kara gaba sun yi abun da za su yi sun gudu, kuma yanzu lokaci ne na aikin gona, suna zuwa farwa mutane suke yi da harbin kan mai-uwa-da-wabi''

A Najeriya dai ana ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman a yankin Arewa maso Yamma, inda hare-haren 'yan fashin daji suka zama ruwan dare a wasu jihohi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jihohin Zamfara da Sakkwato da Katsina da ke makwabtaka da juna na daga cikin yankunan da suka fi fuskantar irin waɗannan hare-hare, inda maharan ke kai farmaki kan ƙauyuka da garuruwa, tare da kashe mutane ko yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

A wasu lokutan kuma, maharan kan farmaki manoma a gonakinsu ko matafiya a kan manyan hanyoyi, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi tare da haddasa fargaba a tsakanin al'umma.

Matsalar ta yi tasiri sosai kan harkokin noma da kasuwanci, musamman a yankunan karkara da ke dogaro da noma a matsayin babbar hanyar samun abin rayuwa. A lokuta da dama, manoma kan kasa zuwa gonakinsu saboda tsoron hare-hare, abin da ke haifar da fargabar ƙarancin amfanin gona da kuma ƙarin matsin tattalin arziki ga mazauna yankunan.

Duk da cewa gwamnati da jami'an tsaro sun sha ƙaddamar da hare-hare kan maboyar 'yan bindigar tare da tura ƙarin jami'ai zuwa yankunan da abin ya fi kamari, hare-haren na ci gaba da faruwa a wasu wurare.

Yan fashin daji

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Yan fashin daji

A jihar Zamfara musamman, hare-haren 'yan bindigar sun daɗe suna haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, inda al'ummomi da dama suka rasa 'yan uwansu, yayin da wasu suka tilasta barin muhallansu saboda rashin tsaro. Haka kuma a jihohin Sakkwato da Katsina, an sha samun rahotannin hare-hare a ƙauyuka da yankunan da ke kusa da dazukan da maharan ke amfani da su a matsayin mafaka.

Masana harkokin tsaro na ganin cewa warware matsalar na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, jami'an tsaro da kuma al'ummomin yankunan da abin ya shafa. Suna kuma jaddada muhimmancin magance matsalolin da ke bai wa masu aikata irin waɗannan laifuka damar samun mafaka da kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da wani shamaki ba.

Harin da ya afku a Goro-Nqmaye na zuwa ne a daidai lokacin da manoma ke ci gaba da shirye-shiryen noma da kuma aikin gona a daminar bana, lamarin da ya sake tayar da hankulan mazauna yankin game da tsaron rayukansu yayin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.