Kotu ta tabbatar wa Senegal lashe kofin AFCON
An tabbatar da Senegal a matsayin wadda ta lashe gasar Kofin Nahiyar Afirka ta 2025 (Afcon) bayan wani hukunci da Kotun Sulhunta Rikice-rikicen Wasanni (Cas) ta yanke.
Hukuncin kotun ya soke wani mataki da aka ɗauka a baya wanda ya ƙwace wa ƙasar ta yammacin Afirka kambun da ta lashe a filin wasa, bayan wasan ƙarshe mai cike da ce-ce-ku-ce da ta buga da mai masaukin baƙi, Moroko, a watan Janairu.
Sakamakon wasan da aka buga a birnin Rabat,inda Senegal suka yi nasara da ci 1-0 bayan an ƙara lokaci, ya sauya kusan watanni biyu bayan gasar, lokacin da kwamitin daukaka ƙara na Caf ya yanke cewa Senegal ta karya dokokin gasar.
Kwamitin ya ce 'yan wasan Senegal sun bar filin wasa a lokacin da aka shiga ƙarin lokaci domin nuna rashin amincewarsu da fenaritin da aka bai wa Moroko.
Daga nan ne Hukumar Kwallon Kafar Senegal (FSF) ta ɗaukaka ƙara zuwa Cas, wadda ita ce babbar kotun wasanni ta duniya. Wani kwamitin alkalai uku ne ya saurari ƙarar a wani zama na sirri a birnin Lausanne na ƙasar Switzerland a ranar 8 ga Oktoba.