Me ya haifar da rikicin shugabancin majalisar dattawa mai zuwa tun yanzu?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Tun kafin a gudanar da zaɓen 2027, wata taƙaddama ta ɓarke a Majalisar Dattawan Najeriya bayan amincewa da wani ƙudiri da ke neman shugabannin majalisar na yanzu su ci gaba da jagoranci a majalisa ta gaba da za a zaɓa a watan Janairu.

Matakin ya haifar da muhawara mai zafi tsakanin sanatoci, inda wasu ke kallonsa a matsayin yunƙurin tabbatar da ci gaba da kwanciyar hankali, yayin da wasu kuma ke ganin kamar an fara raba mukamai tun kafin zaɓe.

Rikicin ya ƙara ƙamari ne bayan wasu sanatoci sun yi Allah-wadai da kudirin, suna masu cewa ba aikin majalisar da ke kan mulki ba ne ta yanke hukuncin wanda zai jagoranci majalisar da za a kafa bayan sabon zaɓe.

A cewarsu, irin wannan mataki na iya tauye 'yancin sabbin mambobin da za su shiga majalisar bayan zaɓen.

Me ƙudirin ya ƙunsa?

Ƙudirin wanda aka gabatar a ranar 15 ga watan Oktoba a gaban zauren majalisar. kuma aka amince da shi a fatar baki, yatanadi cewa duka shugabannin majalisar zarce a kan mukamansu a majalisar a majalisa ta 11.

Shugabannin majalisar da ƙudirin ya ƙunsa sun haɗa da shugaban Majalisar, sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa Sanata Barau Jibril da shugaban masu rinjaye na Majalisa, Sanata Bamidele da mataimakinsa da mai tsawatarwa da mataimakinsa da shugaban marasa rinaye da sauran shugabannnin majalisar.

A watannin baya ma majalisar ta yi wani ƙudiri da ya yi tanadin cewa ƴanmajalisar da suka yi wa'adi biyu a jere ne kawai za su iya zama shugabannin majalisar dattawa.

Wani abu da wasu ke ganin hanya ce ta hana wasu ƴanmajalisa zama shugaban majalisar.

Kodayake daga baya an soke ƙudirin bayan sanya bakin Shugaba Bola Tinubu.

Me masu adawa da ƙudirin ke cewa?

Masu adawa da ƙudirin sun bayyana matakin da cewa "riga malam masallaci", suna masu jaddada cewa shugabancin majalisa ya kamata ya kasance sakamakon tattaunawa da zaɓin da 'yan majalisar za su yi bayan an kammala zaɓe, ba kafin lokaci ba.

Sun yi gargaɗin cewa hakan na iya janyo rabuwar kai da rashin jituwar siyasa a cikin majalisar.

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno na daga cikin masu hammaya da ƙudirin ya kuma kuma shaida wa kafar yaɗa labarai ta Arise cewa duk da bai halarci zaman da aka gabatar da ƙudirin ba, ba zai amince da shi ba.

''Ni bana goyon bayan wannan ƙudiri, bana cikinsa ba na ma cikinsa, babu abin da hakan zai sauya, saboda ya saɓa doka'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa duka ƴanmajalisar APC da suka samu tikitin sake tsayawa takara ba su 50, don haka wannan ba abu ne da za a amince da shi ba.

A ɗaya ɓangaren kuma, masu goyon bayan ƙudirin na cewa ci gaba da shugabancin da ake da shi zai taimaka wajen tabbatar da daidaito da kuma ci gaban ayyukan majalisar, musamman a lokacin da ake fuskantar muhimman batutuwan ƙasa.

Suna ganin gogewar shugabannin na yanzu za ta iya zama ginshiƙi wajen tafiyar da harkokin majalisar cikin sauƙi.

Yayin da muhawarar ke ci gaba da ɗaukar hankali, tambayar da ke gaban masu sa ido ita ce me ya janyo rikicin, kuma wannan rikici zai tsaya ne a kan batun tsarin mulki da dokokin majalisa, ko kuwa yana nuna fara gwagwarmayar neman iko da tasiri a majalisa tun kafin 'yan Najeriya su kai ga babban zaɓen da ke tafe.

Me ya janyo ƙudirin?

Masana harkokin siyasa sun ce tsantsar son kai ne ya sa ƴanmajalisar ke wannan kokawa tun yanzu.

Farfesa Abubakar Umar Kari, Mai sharhi ne kan al'amuran siyasar kasar ya kuma shaida wa BBC cewa zalama da haɗama ce ta sa ƴanmajalisar suka fara wannan yunƙuri tun yanzu.

''Wannan na kara fito da zamalar shugaban majalisar na yanzu a fili'', in ji shi.

Farfesa Kari ya zargi shugaban majalisar da yin irin wannan yunƙuri a lokuta da dama a baya domin daƙushe yunƙurin zama shugaban majalisar na gaba.

''A baya ya yi rigima da tsohon gwamnan jihar Edo, kuma tsohon shugaban APC mai mulki, wanda shi ma ake ganin zai iya neman kujerar a majalisar ta 11'', in ji Farfesa Kari.

''Haka ma mun ga irin takun-saƙar da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, wanda shi me ake ganin yana hararar kujerar shugaban majalisar'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

'Ya saɓa wa dimokraɗiyya'

Farfesa Kari ya ce wannan ya saɓa wa tsarin dimokraɗiyya.

''Ni dai tun da nake ban taɓa ganin irin wannan ba a tsarin dimokraɗiyya, a kowace kasa kuwa''.

Ya ce majalisar dattawan Najeriya na 10 ta rasa abubuwa na ƴancin kanta.

''Wannan majalisa ce kawai ta Tinubu da Akpabio'', kamar yadda ya bayyana.