Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 21/10/2026

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 21/10/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Rabi'atu Kabir Runka

  1. Rasha ta saki wani Baʼamurke bayan ziyarar wakilin Amurka

    Rasha ta saki wani ɗan ƙasar Amurka mai shekaru 74, Stephen Hubbard, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai bisa zargin yaƙi a gefen Ukraine.

    Sakin nasa ya zo ne a daidai lokacin da wakili na musamman na Amurka, Steve Witkoff, ya kai ziyara birnin St. Petersburg domin ganawa da Shugaba Vladimir Putin.

    Rahotanni sun ce an kai Hubbard filin jirgin saman Pulkovo da sanyin safiyar Laraba. Hubbard dai ya shiga hannun dakarun Rasha a birnin Izyum na Ukraine bayan mamayar da Moscow ta fara a shekarar 2022, kuma an yanke masa hukuncin a shekarar 2024.

    Daga baya, Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da sakin Hubbard, yana mai cewa yana kan hanyarsa ta komawa ƙasarsa.

    Trump ya kuma ce ba a yi musayar fursunoni ba domin a samu sakin nasa.

    Trump ya ce sakin Hubbard ya biyo bayan wata buƙata da ya miƙa kai tsaye ga Putin a makon da ya gabata. A baya ma wasu ƴan ƙasar Amurka sun samu ƴanci daga hannun Rasha ne ta hanyar yarjejeniyoyin musayar fursunoni tsakanin ƙasashen biyu.

  2. Dars Hausa: BBC za ta ƙaddamar da shirin ilmantar da yaran da ba sa zuwa makaranta

    BBC World Service ta faɗaɗa shirin ilmantarwa na "Dars" da ya samu lambar yabo zuwa harshen Hausa domin yara a Yammacin Afrika.

    Za a gabatar da darussa ga yara a talabijin da rediyo da kuma kafofin sada zumunta na intanet da suka hada da Youtube da Facebook da X da Instagram da kuma Tiktok.

    Dars Hausa, wanda sashen Hausa na BBC zai ƙaddamar, shiri ne da zai yi ƙoƙarin bayar da gudunmawa wajen magance ƙalubalen bukatar gaggawa ta ilimi a yankin, ta hanyar isar da darussa ga yara 'yan shekara 11 zuwa 16 daga cikin ingantattun kayan koyarwa na BBC.

    Najeriya na cikin ƙasashen duniya da ke da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa kusan yara miliyan 19 ne ba sa samun ilimi.

  3. Hare-hare ta sama sun kashe gomman yara a Sudan

    Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta ce aƙalla yara 18 na daga cikin ɗaruruwan mutanen da aka bada rahoton mutuwarsu sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙa da na sama da suka auku a sassa daban-daban na Sudan cikin makon da ya gabata.

    A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, akalla yara 10 sun mutu a hare-haren jirage marasa matuƙa da aka kai a ƙarshen mako, yayin da wasu yara uku suka mutu a ranar Litinin a birnin Khartoum.

    Haka kuma, a ranar Alhamis, wasu yara biyar daga iyali ɗaya sun mutu a wani hari ta sama a jihar North Kordofan, yayin da mahaifiyarsu ta tsira da raunuka.

    Daraktar ƙungiyar ta Save the Children a Sudan, Claire Henery, ta ce sabbin hare-haren na ƙara jefa yara da iyalai cikin haɗari a lokacin da ƙasar ke fama da ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin jin ƙai a duniya.

    Ta ce baya ga asarar rayuka, hare-haren na iya ƙara jefa asibitoci, makarantu da sauran muhimman ayyuka cikin matsala, lamarin da zai ƙara tsananta wahalhalun da iyalai ke ciki.

    Ƙungiyar ta yi kira ga ɓangarorin da ke rikici da su kare fararen hula tare da mutunta dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa.

    Ta ce yara bai kamata su rayu cikin fargabar hare-hare ba, ko a gida, ko a makaranta, ko lokacin neman kulawar lafiya.

    Rikicin Sudan ya riga ya tilasta wa kusan mutum miliyan 11 barin gidajensu, yayin da masana ke gargaɗin ƙara haɗarin yunwa a wasu sassan Darfur da Kordofan.

  4. Houthi ta musanta kai hari Madina

    Mai magana da yawun rundunar sojin Houthi a Yemen, Yahya Saree, ya ce ƙungiyar ba ta harba wani jirgi mara matuƙi zuwa yankin Madina na Saudiyya a ranar Laraba, kuma ba ta kai wani hari kan ƙasar ba.

    Kalaman nasa na zuwa ne bayan da ƙawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta ya sanar da cewa ya tarwatsa jirage marasa matuƙa guda biyar da suka nufi ƙasar.

    Ƙawancen ya ce ɗaya daga cikin wuraren da aka nufa da hare-haren shi ne yankin Madina. Mai magana da yawun ƙawancen, Turki al-Maliki, ya ce an cafke tare da lalata jirage marasa matuƙa huɗu da aka harba zuwa Saudiyya.

    A cikin wani saƙo na daban, Al-Maliki ya ce an tarwatsa jiragen ne a yankin gabashin Saudiyya da kuma yankin Madina.

    Daga baya kuma ya sanar da cewa an sake tarwatsa wani jirgi mara matuƙi a gabashin ƙasar, ba tare da ya bayyana wanda ya kai harin ba.

  5. Ethiopia ta samar da wuraren gina tashar makamashin Nukiliya

    Habasha Ta Zaɓi Wurare Uku Domin Gina Tashar Makamashin Nukiliya

    Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya ce ƙasar ta tantance sama da wurare 30 da aka tsara domin gina tashar samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya, amma daga ƙarshe an rage su zuwa wurare uku.

    Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai hedkwatar Hukumar Makamashin Nukiliya ta ƙasar.

    Abiy ya ce Habasha ta samu ci gaba wajen kafa cibiyoyi da tsare-tsaren da ake buƙata domin bunƙasa fasahar nukiliya.

    A cewarsa, an kafa ƙungiyar bincike da wani kamfani a hukumance, sannan an naɗa ma'aikata da shugabanni tare da kammala tsarin gudanarwa.

    Ya ce wuraren da aka ware tun farko sun ragu daga sama da 30 zuwa 13, daga nan zuwa biyar, kafin daga ƙarshe a zaɓi wurare uku.

    Sai dai ya jaddada cewa Habasha ba za ta iya tabbatar da dacewar wuraren da kanta ba, yana mai cewa kamfanonin ƙasashen waje ne za su gudanar da tantancewar ƙarshe.

    Firaministan ya ƙara da cewa idan an tabbatar da dacewar wuraren, za a fara shirye-shiryen aiwatar da aikin tare da rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanonin da ke samar da fasahar nukiliya.

    Ya ce irin waɗannan manyan ayyuka ba sa kammala cikin ɗan lokaci, kuma suna buƙatar haɗin gwiwar ƙwararru da cibiyoyi da dama. Ya kuma jaddada cewa Habasha za ta yi amfani da makamashin nukiliya ne kawai domin ayyukan zaman lafiya.

  6. Shin PSG ce ƙungiyar da ta fi kowa a duniyar ƙwallon ƙafa?

    Ana ci gaba da muhawara game da ƙarfin ƙungiyar PSG idan aka haɗa ta da sauran ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa.

    Ko PSG ta fi ƙarfin kowa a yanzu?

  7. Rasha ta ce za ta aikawa Amurka man Diesel

    Mataimakin Firaministan Rasha, Alexander Novak, ya ce Rasha za ta aika jirginta na farko ɗauke da man diesel zuwa Amurka a ranar Alhamis.

    Hakan na zuwa ne bayan rahotannin da ke cewa an cimma wata yarjejeniya tsakanin shugaban Amurka, Donald Trump, da Rasha kan samar da man fetur.

    Rasha ta ɗage haramcin fitar da man diesel a ranar 9 ga Oktoba. Tun farko an sanya haramcin ne domin tinkarar ƙarancin man fetur bayan hare-haren jiragen sama marasa matuƙa na Ukraine da suka shafi masana'antun tace mai na ƙasar.

    Novak ya ce jirgin farko zai ɗauki tan 40,000 na man diesel, inda ya ce da takardun da suka shafi yarjejeniyar samar da man na gab da kammaluwa.

    Sai dai bai bayyana tashar jirgin ruwan da za a loda man ba.

    Ya kuma ce ana sa ran ƙarin jigilar man fetur zuwa Amurka a nan gaba. A cewarsa, Rasha na da ƙarfin biyan buƙatun Amurka.

    Rahotanni sun ce Trump ya bayyana cewa Amurka za ta karɓi tan 300,000 na man diesel da farko, sannan a watan Nuwamba za a ƙara tan 500,000, kafin a sake fitar da ƙarin tan miliyan ɗaya daga baya.

  8. Jihohin da Tinubu ka iya fuskantar ƙalubale a zaɓen 2027

    Yayin da zaɓen shugaban Najeriya na shekarar 2027 ke ƙara matsowa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fuskantar ƙalubalen siyasa a wasu jihohi da ka iya zama masa tarnaƙi, yayin da yake neman samun nasara domin yin wa'adi na biyu a zaɓen mai zuwa.

  9. Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa da Houthi ta harba Madina

    Ƙawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta a yaƙin da yake yi da mayaƙan Houthi na Yemen ya ce ya tarwatsa jirage marasa matuƙa guda biyar da suka nufi ƙasar Saudiyya.

    Ƙawancen ya ce ɗaya daga cikin wuraren da aka nufa da waɗannan hare-hare shi ne yankin Madina.

    Madina na ɗaya daga cikin biranen Musulunci mafi tsarki, inda Annabi Muhammad (SAW) yake kwance, kuma akwai Masallacin Annabi.

    A baya mayaƙan Houthi sun ce ba za su kai hari kan biranen Makka da Madina ba.

    Mai magana da yawun ƙawancen, Turki al-Maliki, ya ce an cafke tare da lalata jirage marasa matuƙa huɗu da aka harba zuwa Saudiyya.

    Ya ce an tarwatsa jiragen ne a yankin gabashin Saudiyya da kuma yankin Madina.

    Daga baya Al-Maliki ya sanar da cewa an sake tarwatsa wani jirgi mara matuƙi a gabashin Saudiyya, ba tare da ya bayyana wanda ya kai harin ba.

    A cikin makonnin baya-bayan nan, Saudiyya ta sha fuskantar hare-hare daga mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran, ciki har da harin da aka kai filin jirgin saman Riyadh wanda ake ganin na daga cikin mafi muni da ƙasar ta fuskanta a ƴan shekarun nan.

  10. Me cutar Ebola ke yi wa jikin wanda ta kama?

    Cutar Ebola ta sake tayar da hankalin jama'a a Najeriya bayan da gwamnatin ƙasar ta tabbatar da ɓullar cutar a Abuja, babban birnin ƙasar.

    Ministan lafiyar kasar, Farfesa Ali Pate, ya ce wata mata ce ta kawo cutar bayan komawarta ƙasar daga Uganda a jirgin sama, kuma an killace ta tare da fara bibiyar mutanen da suka yi mu'amala da ita domin daƙile yiwuwar yaɗuwar cutar.

    Wannan sanarwa ta zo ne shekaru 12 bayan Najeriya ta yi nasarar shawo kan ɓarkewar Ebola da ta afku a shekarar 2014, wadda ta jawo ɗimbin damuwa a cikin ƙasa da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.

    A yanzu hukumomi na cewa sun gano mutum 44 da suka yi mu'amala da matar, yayin da aka sanya cibiyoyin lafiya cikin shirin ko-ta-kwana.

    Ebola na daga cikin cututtuka masu haɗari da ke haddasa zazzaɓi mai tsanani kuma tana iya kai wa ga lalacewar wasu muhimman gaɓoɓin jiki.

    Dr Nasir Sani Gwarzo, ƙwararren likita kan cuta masu yaɗuwa a Najeriya, ya ce cutar Ebola kan kwashe fiye da mako guda a jikin wanda ya kamu da ita kafin ta fara nuna alamomi.

    ''Saboda da haka duk wanda ya yi mu'amala da mai ɗauke da cutar a lokacin da yake kan ganiyar cutar to zai iya kamuwa da ita'', in ji shi.

    Don haka ne ya bayar da shawarar cewa a duk lokacin da aka samu labarin cewa wani ya yi mu'alama da mai cutar ko ya ce ƙasar da ake yin cutar to abin da ya kamata shi a a killace shi.

  11. Tsarin raba bayanai tsakaninmu da Amurka ya dawo aiki - Zelensky

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce raba bayanan sirri tsakanin ƙasarsa da Amurka "na aiki yanzu", bayan wata ganawa da ya yi da wakilin na musamman na Amurka, Steve Witkoff, a birnin Oslo na ƙasar Norway.

    Bayan kammala tattaunawar, Witkoff ya isa Rasha domin ganawa da Shugaba Vladimir Putin kan yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin.

    Kafin wannan ci gaba, Ukraine ta zargi Amurka da dakatar da ba ta wasu muhimman bayanan sirri da suka shafi hare-haren Rasha, wanda ta ce ya janyo asarar rayuka.

    Sai dai Amurka ta ƙaryata zargin. Bayan tattaunawar Oslo, Zelensky da ƙawayensa na Turai sun ce yanzu ya rage ga Rasha ta mayar da martani kan shawarwarin da aka amince da su.

    Har yanzu Shugaba Putin bai yi wata magana a bainar jama'a kan tattaunawar ba. Amma Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce Kremlin za ta saurari abin da wakilin Amurka zai gabatar, duk da cewa Rasha ba za ta amince da wani "rangwamen siyasa" ba.

    A nasa ɓangaren, shugaban Finland, Alexander Stubb, ya ce an samu ci gaba a ƙoƙarin samar da zaman lafiya, sai dai ya ce hakan ka iya ɗaukar lokaci.

  12. Iraqi ta rufe kan iyakarta da Iran

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato majiyoyin da ke aiki a kan iyaka na cewa Iraq ta rufe mashigin Chazaba da ke kan iyakarta da Iran har sai wani lokaci da ba a bayyana ba.

    Rahoton ya ce an dakatar da zirga-zirgar fasinjoji da motoci da kuma manyan motocin dakon kaya ta wannan mashigi na wucin gadi.

    Mashigin Chazaba na daga cikin manyan hanyoyin da ake amfani da su wajen zirga-zirgar mutane da kayayyaki tsakanin Iran da Iraq.

    Majiyoyin sun shaida wa Reuters cewa an dauki wannan matakin ne domin sake duba tsare-tsaren tsaro da ake da su a mashigin.

    Tun da farko, wani jami'in gwamnatin Iraq ya shaida wa Al Jazeera cewa Firaministan kasar ya ba da umarnin rufe mashigin Shalamcheh da ke kan iyakar Iran har sai wani lokaci da ba a bayyana ba.

    Jami'in ya kara da cewa ana sa ran a hankali za a rufe wasu mashigai da ke tsakanin Iraq da Iran a cikin kwanaki masu zuwa.

    Sai dai har yanzu gwamnatin Iraq ba ta bayyana dalilin daukar wannan mataki ba.

  13. Kwankwaso ya ba da gudunmawa wajen bunƙasa Najeriya - Abba Kabir Yusuf

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, murnar cika shekara 70 da haihuwa.

    A wata sanarwa, Gwamna Yusuf ya bayyana wannan rana a matsayin wata muhimmiyar dama ta tunawa da rayuwar Kwankwaso, da jagorancinsa, da kuma gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

    Gwamnan ya yaba da rawar da Kwankwaso ya taka a ci gaban siyasar jihar Kano, yana mai cewa bikin cika shekarun na ba da damar waiwayen ayyukan hidimar jama'a da ya yi tsawon shekaru.

    Ya ce Kwankwaso ya bayar da gudunmawa a fannoni daban-daban da suka haɗa da mulki, gina ababen more rayuwa da kuma ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a jihar Kano.

    A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2026, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikinta.

    Lamarin da ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin makusantan biyu.

    A wajen bikin komawarsa APC, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya ɗauki matakin sauya sheƙar ne bisa la'akari da inda aka dosa a siyasar Najeriya da kuma buƙatar bin hanyar da za ta kawo ci gaba ga jama'ar Kano baki ɗaya.

    Sai dai a wata hira da BBC,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da yaƙinin cewa sai gwamnan Kano Abba Kabir da muƙarrabansa sun yi da-na-sanin raba gari da tsarinsu.

  14. Ba za mu tattauna da Amurka ba har sai ta amince da sharuɗɗanmu - Iran

    Iran ta shaida wa babban kwamandan rundunar sojin Pakistan cewa ba za ta shiga tattaunawa da Amurka ba har sai an cika sharuɗɗan da ta gindaya.

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa shugaban ƙasar, Massoud Pezeshkian, ya gana da babban kwamandan sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, a Tehran, inda suka tattauna kan ƙoƙarin sasanta rikice-rikice da kuma halin da yankin ke ciki.

    Pakistan na taka muhimmiyar rawa a ƙoƙarin shiga tsakanin Amurka da Iran.

    Munir ya kuma gana da kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf. A wata sanarwa da Iran ta fitar bayan ganawar, ta ce Tehran ba za ta sake amincewa da Washington ba har sai Amurka ta cika sharuɗɗa bakwai da Iran ta gabatar a watan da ya gabata dangane da sake buɗe mashigin ruwa na Hormuz.

    Iran ta ce daga cikin sharuɗɗan akwai ɗage takunkuman da aka ƙaƙaba wa tashoshin jiragen ruwanta, kawo ƙarshen takunkumi kan fitar da man fetur ɗinta, da kuma dakatar da rikice-rikice a sassa daban-daban na yankin.

    Shugaban hukumar leƙen asirin Iran, Mohsen Rezaei, shi ma ya isar da irin wannan saƙo ga Munir, yana mai jaddada cewa Tehran ba za ta shiga tattaunawa da Washington ba har sai an biya mata waɗannan buƙatu.

    Ya kuma ce dukkan sinadarin uranium da Iran ta tace zai ci gaba da zama a cikin ƙasar, ra'ayin da ya ce ya yi daidai da matsayin jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei.

  15. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba, ta bawa ranar samu, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Rabi'atu Kabir Runka ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku biyu mu a shafunkanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.