Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane tasiri takarar Makinde za ta yi ga Tinubu a kudu maso yamma?
Sukar da gwamnan jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APM, Seyi Makinde ke yi wa gwamnatin shugaba Tinubu dangane da zargin riƙe kuɗaden jihohi da ƙananan hukumomi na ribar iskar gas da gwamnatin tarayya ta yi, ya ƙara fito da irin caccakar da ɗan takarar na APM ke yi wa APC.
A baya-bayan nan, babban abin da Seyi Makinde ya fi sukar gwamnatin Bola Tinubu a kai shi ne halin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa, yana zargin gwamnatin da kasa sauƙaƙa wa 'yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta.
Makinde, ta bakin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Dr Sulaimon Olanrewaju, ya ce fadar shugaban ƙasa ta ƙasa mayar da hankali kan ainihin batun da ya tayar a martanin da ta mayar kan zarge-zargensa.
Gwamna Seyi Makinde shi ne gwamna mai tilo a Najeriya da ke takarar shugaban ƙasa.
'Ɓata ruwa ba don a sha ba a jihar Oyo'
Dakta Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta CAS da ke Kano kuma masanin kimiyyar siyasa, ya ce babu shakka takarar Gwamnan jihar Oyo za ta iya zama ƙalubale ga jam'iyya mai mulki musamman a yankin kudu maso yamma.
" Saboda haka takarar ta shi Seyi Makinde a jam'iyyar APM za ta iya zama abin da ake kira da 'mai ɓata ruwa ba don ta sha ba' ta hanyar rage ƙuri'un yankin musamman jihar Oyo," in ji Dakta Sufi.
Dangane da zaɓen 2027, jihar Oyo na daga cikin manyan jihohin Kudu maso Yamma masu yawan masu kaɗa ƙuri'a, kuma kasancewar Makinde gwamna mai ci, duk wani tasiri da yake da shi a Oyo na iya taka muhimmiyar rawa ga sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a yankin.
Sai dai kuma Dakta Kabiru Sufi ya ce ba lallai takarar ta Makinde ta zama barazana ga takarar Shugaba Tinubu ba kasancewar hakan ka iya zama alkairi ga APC ta hanyar rarraba ƙuri'a.
Idan Makinde, Peter Obi da Atiku da sauran ƴan hamayya ba su dunƙule ba, hakan na iya rarraba ƙuri'un adawa, lamarin da zai amfani jam'iyyar APC ta Tinubu.
Tasirin Makinde a jihohin kudu maso yamma
Babu ƙaƙƙarfar hujja da ke nuna cewa gwamna Makinde zai iya yin tasiri irin na Oyo a sauran jihohin Kudu maso Yamma guda biyar, amma akwai wasu dalilan siyasa da ke sa masu sharhi ke ganin zai iya zama barazana ga Tinubu.
Sai dai masana sun bayar da wasu dalilai guda uku da bai kamata a yi wa takarar ta Seyi riƙon sakwa-sakwa ba.
- Seyi Makinde shi ne gwamna mai ci a Jihar Oyo kuma ya yi suna a yankin Kudu maso Yamma saboda yadda ya lashe zaɓen gwamna sau biyu. Wannan na iya ba shi damar jawo hankalin wasu masu zaɓe a wasu jihohin yankin.
- Ya fito ne daga yankin da ake kallon a matsayin sansanin siyasar Bola Tinubu, don haka kasancewarsa ɗan takara daga yankin na iya rage wa Tinubu cikakken rinjaye a wasu wurare.
- Yana fafutukar neman ƙuri'u a Lagos da sauran jihohin Kudu maso Yamma, kuma ya gina kamfen ɗinsa ne kan suka ga gwamnatin Tinubu musamman kan tattalin arziƙi da tsadar rayuwa wanda ke damun al'umma.
Wane Makinde?
Seyi Makinde ɗan kasuwa ne kuma injiniya kafin ya shiga siyasa. Ya fara neman muƙamin zaɓe ne a shekarar 2007 lokacin da ya tsaya takarar Sanatan Oyo ta kudu, amma bai yi nasara ba.
Daga baya ya sake neman tikitin jam'iyyar PDP a 2011 a wannan kujera, amma bai samu tikitin ba.
A 2014 ya nemi tikitin gwamnan jihar Oyo a jam'iyyar PDP amma bai samu ba.Daga nan ya koma jam'iyyar SDP inda ya tsaya takarar gwamna a 2015, amma ya zo na uku.
A 2017 ya sake komawa PDP, inda ya samu tikitin gwamna, sannan ya lashe zaɓen gwamnan Oyo a 2019.
Ya kuma sake lashe zaɓe a 2023, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin gwamnoni masu tasiri a yankin Kudu maso Yamma