Abu 3 da suka sa Spain ta jima tana mamaye ƙwallon duniya

Spain midfielder Lamine Yamal with the World Cup trophy
Bayanan hoto, Lamine Yamal na cikin matasan ƴan ƙwallon Spain da ke jan zare
    • Marubuci, Dane Massey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Zakarar gasar duniya, da ta Turai da ma gasar Olympic, sannan ƙasar da ba a doke ba a kusan shekara biyu da rabi. Yanzu lallai za a cewa Spain ta zama jigo a ƙwallon ƙafa a duniya.

A cikin gasa guda goma da aka buga a baya, Spain ce ta lashe guda biyar.

A yanzu da za ta fafata wasa da Ingila a gasar Nations League a ranar Asabar a filin Wembly da ke Birtaniya, ƙasar ta buga wasa 38 ba tare da rashin nasara ba. Rabon da a doke Spain a wasa, tun wasan sada zumunta da Colombia ta doke da ci ɗaya mai ban haushi a shekarar 2024.

Haka kuma ba wai babbar tawagar ƙasar ba ce kawai take samun nasara, a cikin ƴan tsakankanin nan, Spain ta lashe:

  • Gasar turai ta ƴan ƙasa da shekara 19 sau shida
  • Gasar turai ta ƴan ƙasa da shekara 21 sau uku
  • Gasar cin kofin duniya ta mata ta 2023

A matakin ƙungiya kuwa, ƙungiyoyin Spain ne suka lashe kusan rabin gasar zakarun turai da gasar europa da aka buga tun daga shekarar 2009.

Masani kuma mai sharhi kan harkokin wasannin Spain, Guillem Balague ya bayyana wa BBC Radio 5 cewa akwai "abubuwa guda uku da suka ginshiƙai" da suka Spain ta zarce sa'anni.

"Na farko shi ne kasancewar akwai jami'a, musamman wata da ake kira National Institute of Physical Education," in ji shi.

"Jami'o'i sun shiga harkokin wasanni a Spain da daɗewa, tun a kusan tsakankanin 1990s, kuma hakan ya sa aka samu masu horarwa da dama da suka san harkar sosai, musamman a ɓangaren atisaye da horo.

"Wasu daga cikin irin waɗannan masu horarwar na karatu sun samu nasara sosai, kamar Rafa Benitez da Marcelino Garcia Toral.

"Abu na biyu shi ne al'adar Basque. Al'adar Basque wata daɗaɗɗiyar al'ada ce a harkar ƙwallon Spain da ke da alaƙa da jajircewa.

"Na uku shi ne abin da kowa ya sani: rawar da Barcelona ta taka, da rawar Johan Cruyf wajen sauya salon harkar, da kuma ƙoƙarin da ya biyo ba."

Bayanan bidiyo, Lokacin da Spain ta lashe gasar kofin duniya

Rawar da Barcelona ta taka

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin ƴan wasan tawagar Spain da ta lashe gasar kofin duniya ta 2010, akwai ƴan wasan ƙungiyar Barcelona guda takwas, sannan a cikin ƴan wasan tawagar da ta lashe gasar ta ƙarshe da aka buga a ƙarƙashin koci Luis de la Fuente ma akwai ƴan Barselona guda takwas.

Barcelona ta lashe kofin turai na farko wato Europa a lokacin a shekarar 1992 a ƙarƙashin koci Cruyff.

A lokacin Gurdiola ne kuma Barcelona ta ƙara kwaikwayon tsarin ƙwallon, inda a tsakankanin zamanin ta lashe La liga uku, sannan Spain ta lashe gasar turai sau biyu a jere a 2008 da 2012, sannan ta lashe gasar kofin duniya a 2010.

Xavi da Iniesta da Bosquet duk sun taso ne a ƙarƙashin irin tsarin, inda suke koyon riƙe a yi ta rarrabawa a tsakiyar.

Jordi Gratacos, daraktan kwalejin horar da ƴanwasan ƙungiyar a tsakaninn 2009 zuwa 2011, da kuma zagaye na biyu a 2016 zuwa 2020 ya shaida wa BBC cewa, "burinmu shi ne samar da ƙwararrun ƴanƙwallo da suka fahimci tamaula sosai.

A kaka biyu na farko da ya jagoranci Barcelona, Hansi Flick ya fara yunƙurin maimaita abin da Guardiola ya yi.

Yanzu haka waɗanda suke jagorantar ƙungiyar da tawagar a yanzu su ne Lamine Yamal da Dani Olmo da Pau Cubarsi.

Kalli abubuwan da ke faruwa
Bayanan bidiyo, Matasan da suka lashe gasar

Tsarin Basque

Idan Barcelona da Catalonia suna nuna ƙwarewa a taka leda, tsarin Basque ne ka bayyana yanayin al'adar ƙwallon ƙasar.

Ƴanwasan biyar a cikin waɗanda suka lashe kofin duniya ta 2026 ƴan yankin ne.

Haka kuma akwai Mikel Merino, wanda ya zura ƙwallo a wasan kwata-fainal da Spain ta doke Jamus gasar turai ta 2024, sannan ya ci ƙwallo shida a wasa shida na wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya.

Haka kuma kimanin kilomita biyar daga Pamplona ne garin Zizur, inda aka haifa tsohon ɗan wasan Spain da Chelsea Cesar Azpilicueta.

Da aka tambaye shi a game da al'adar Basque, Azpilicueta ya bayyana wa BBC : "tsari ne na jajircewa da aiki tare da sadaukarwa."

Cruyff ya taɓa bayyana cewa, "abu na farko da nake yi a lokacin da nake koci shi ne in tabbatar da ina da ƴanwasan aƙalla huɗu da suka san tsari da al'adar Basque. Ba su da tsaro a filin ƙwallo."

A tawagar ta yanzu, a shekarar 2026, Unai Simon ya kasance mai tsaron raga, sannan akwai tsohon ɗanwasan Man City, Aymeric Laporte da Nico Williams da Ferran Torres da Martin Zubimendi.

Ilimi da ƙwarewar masu horarwa

Abu na ƙarshe shi ne ilimin masu horarwa.

Tsohon kocin Liverpool, Rafa Benitez ya ce, "mun kasance muna ƙoƙarin samar da zaratan ƴanwasa da suke da ƙwarewa da jajircewa a tawagar Spain."

"Na je jami'ar Liverpool John Moores domin ganin yadda ake nazarin kimiyyar wasanni, sai na ga ba su kai mu fahimtar harkar ba.

"Suna da ƙwarewa da fahimta a ɓangaren atisaye, amma a ɓangaren taka leda, ba su da ƙwarewa sosai. Don haka a Ingila babu ƙwararrun masana harkar ƙwallo kamar yadda muke nazari a jami'o'inmu."