Kasashe 5 da za su fuskanci yunwa nan da wata 6 - Rahoto

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) da Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP) sun yi gargaɗin cewa yunwa za ta ƙara tsananta a wurare 16 da suke fama da matsalar ƙarancin abinci a duniya cikin watanni shida masu zuwa.

A cikin sabon rahoton haɗin gwiwa da suka fitar, wanda ya shafi watan Disambar 2026 zuwa Mayun 2027, FAO da WFP sun ce Arewacin Najeriya da Sudan da Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Yemen ne ke fuskantar mafi girman barazanar yunwa.

Rahoton ya ce rikice-rikice da tashe-tashen hankula da kauracewa matsugunai da matsin tattalin arziki da kuma matsanancin sauyin yanayi ne ke haddasa wannan barazana.

Hukumomin sun kuma yi gargadin cewa raguwar tallafin jin ƙai daga ƙasashen duniya na ƙara raunana ƙoƙarin daƙile ɓarkewar matsalar yunwa.

Ga yadda rahoton FAO da WFP ya bayyana halin da kasashen biyar za su iya shiga cikin watanni shida masu zuwa:

Arewacin Najeriya

Rahoton FAO da WFP ya sanya arewacin Najeriya cikin kasashen da ke fuskantar mafi girman barazanar yunwa a duniya cikin watanni shida masu zuwa.

Ya ce rikice-rikice da tashe-tashen hankula da ƙauracewa matsugunai da matsin tattalin arziki suna daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da matsalar rashin abinci a yankin.

Sudan

A Sudan rahoton FAO da WFP ya ce akwai barazanar ɓarkewar yunwa a yankuna 13 na Arewacin Darfur da South Kordofan har zuwa watan Janairun 2027.

A cewar rahoton, yaƙin da ake yi a ƙasar yana kawo cikas ga noma da samar da abinci da harkokin kasuwanni da kuma isar da kayan agaji ga mabukata.

Sudan ta Kudu

FAO da WFP sun kuma ce akwai haɗarin yunwa a wasu sassan Sudan ta Kudu, inda ƙaruwar tashe-tashen hankula ke ƙara dagula matsalar jin ƙai da tuni ta yi muni a ƙasar.

Rahoton ya ce tashin hankalin na ci gaba da lalata hanyoyin samun abinci da kuma rayuwar al'umma.

Somaliya

A Somaliya, rahoton FAO da WFP ya bayyana cewa akwai barazanar yunwa musamman tsakanin mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Baidoa.

Hukumomin sun ce yawan mutanen da rikice-rikice da matsaloli suka raba da gidajensu ya kara jefa dubban mutane cikin mawuyacin hali na rashin wadataccen abinci.

Yemen

A Yemen rahoton FAO da WFP ya ce rikice-rikice da tilastawa mutane yin ƙaura daga matsugunai da matsalolin tattalin arziki na ci gaba da barazana ga rayuwar miliyoyin mutane.

Hukumomin sun bayyana Yemen a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fuskantar mafi tsananin hadarin yunwa a duniya.

Tasirin El Niño da rage tallafin agaji

Rahoton FAO da WFP ya ce rikice-rikice da tashe-tashen hankula ne manyan abubuwan da ke haddasa yunwa a wurare 12 cikin 16 da aka sanya cikin jerin wuraren da ke cikin haɗarin yunwa.

Har ila yau, tsadar abinci da makamashi da sufuri na ƙara raunana ƙarfin mutane wajen samar wa kansu abinci.

Hukumomin sun kuma yi gargadin cewa sauyin yanayin El Niño da ke tasowa na iya ƙara tsananta matsalar, inda zai iya haddasa fari da tsananin zafi a kudancin Afirka da wasu sassan Amurka ta Tsakiya, tare da yiwuwar ambaliyar ruwa mai tsanani a wasu yankunan gabashin Afirka.

Rahoton ya kuma ce tallafin jin kai ga ƙasashen biyar da ke fuskantar mafi girman barazanar yunwa ya ragu da kashi biyu bisa uku tsakanin 2022 da 2025, lamarin da ka iya ƙara janyo matsala a ƙoƙarin kauce wa bala'in yunwa.