Yadda Gwamna Abba ke ƙoƙarin amfani da EFCC don tozarta ni da iyalina - Kwankwaso

    • Marubuci, Aminu Kutama
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin ɓata masa suna da kuma raunana damar jam'iyyarsa ta NDC a zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Jumaʼa, Sanata Kwankwaso ya ce yana zargin gwamnan da ƙoƙarin shigar da shi da iyalansa cikin ce-ce-ku-ce ta hanyar amfani da Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa, EFCC.

Tsohon ministan ya kuma ce Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya taɓa aiki a ƙarƙashinsa a matsayin mataimaki na musamman, babban sakataren sirri da kwamishina, ya yi amfani da amincewar da ya samu a tsakaninsu wajen samun bayanan da yake zargin ana amfani da su wajen ɓata masa suna.

Zargin amfani da ƙungiyoyi don tursasa EFCC

Duk da dai ba a fito da wata shaida ta fili ba, Sanata Kwankwaso ya kuma yi zargin cewa gwamnan ya gabatar da wata buƙata ga EFCC watanni da suka gabata domin hukumar ta bincike shi, amma bayan abin da ya bayyana a matsayin rashin nasarar wannan yunƙuri, sai aka yi amfani da wata ƙungiya mai suna Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative, wato SACGGI, wajen matsa wa hukumar lamba.

"Muna ganin cewa bayan ya kasa tilasta wa hukumar ta bi wannan hanya, saboda mutuncin hukumar da ƙa'idojin aikinta, sai ya koma amfani da wata ƙungiya da ba a san ta sosai ba."

A ranar 24 ga watan Nuwamba ne ƙungiyar ta Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative ta miƙa ƙorafi ga hukumar ta EFCC domin neman ta binciki Jagoran na Kwankwasiyya.

Masu zanga-zangar, ƙarƙashin jagorancin mai magana da yawun ƙungiyar, Muhammad Abdullahi, sun kuma yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan kadarorin da ake zargin Kwankwaso ya mallaka, da suka haɗa da gidaje da filaye, asusun banki, bayanan biyan haraji, da kuma bayanan bayyana kadarori

Zargin amfani da kafafen yaɗa labarai don ɓata suna

Sanata Rabiu Kwankwaso ya kuma yi zargin cewa gwamnan da wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwarsa na amfani da kafafen yaɗa labarai wajen yaɗa bayanai da nufin ɓata masa suna.

"Muna ganin ana fitar da bayanai ne bisa zaɓi, sannan a yaɗa su ta kafafen yaɗa labarai da sauran hanyoyin sadarwa domin nuna lamarin a mafi munin yanayi."

Sanata Kwankwaso ya ce wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓen 2027, kuma yana ganin ana ƙoƙarin karkatar da hankalin jama'a daga muhimman batutuwan da suka shafi ƙasar. Ya kuma yi gargaɗin waɗannan matakai na iya ƙara tsananta siyasa da kuma raunana zaman lafiya a Kano.

Kwankwaso ya yaba wa EFCC

Duk da zarge-zargen da ya yi, Sanata Kwankwaso ya kuma yaba wa EFCC kan yadda ta gudanar da gayyatar da ta taɓa yi masa a baya.

"Ina godiya ga EFCC bisa ƙwarewar da ta nuna wajen gudanar da gayyatar da ta taɓa yi mini sau biyu a shekarun da na yi a aikin gwamnati, da kuma hankali da taka-tsantsan da ta nuna a duk tsawon wannan lokaci.

"Na kuma yi godiya ga Allah cewa sama da shekaru 11 bayan na bar gwamnatin Kano, bayan na yi cikakkun wa'adi biyu a matsayin gwamna, ban da shekaru 17 da na yi a aikin gwamnati, na ci gaba da kasancewa da tsabtataccen tarihi."

A ƙarshe Sanata Kwankwaso ya yi kira ga matasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati da su yi taka-tsantsan wajen amfani da iko da damar da suke da ita don tozarta wasu.

"Bai kamata wannan maganar ta fito daga bakin Kwankwaso ba" - Gwwamna Abba

A tattaunawarsa da BBC, Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kano kuma mai magana yawun Gwamna Abba, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce gwamnatin ba ta da hannu a batun kai Sanata Kwankwaso ƙara EFCC.

"Ba ma Sanata Kwankwaso ba duk wanda irin wannan lamari ya shafa, gwamnatin Kano na da tata hukumar mai yaƙar cin hanci da karɓar ƙorafe-ƙorafe, saboda haka babu wani takamaimai da ya shafi rashawa tsakaninsa da gwamnatin Kano."

Sanusi Bature ya ce sun san cewa Sanata Kwankwaso yana da ƙorafe–korafe da dama tsawon sama da shekaru 11 a gaba EFCC kuma har yanzu yana fama da su.

"Bayan mun ƙaryata hannu a wannan lamari ne kuma ya fito da wannan maganar, duk wanda yake Najeriya ya san Kwankwaso na da matsala a EFCC tsawon shekaru."

Gwamnatin ta kuma musanta amfani da wata ƙungiya don cusguna wa tsohon gwamnan, kasancewar rabuwar siyasa kawai aka samu tsakaninsa da Gwamna Abba.