Yadda jima'i ke ƙara fita daga ran matasa - Bincike

    • Marubuci, Michelle Roberts
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan lafiya na dijital
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wani bincike ya nuna cewa al'ummar Birtaniya, musamman matasa, na yin jima'i a ƙasa da yadda al'ummomin da suka gabace su ke yi, ko kuma ba sa yin sa kwata-kwata, duk da cewa da yawa daga cikinsu na kallon fina-finan batsa da kuma aika wa juna saƙonni ko hotunan batsa ta intanet.

Wannan ne karon farko da binciken da aka fi sani da Natsal, wanda ke nazarin rayuwar jima'i ta al'ummar Birtaniya, ya haɗa tambayoyi kan yadda mutane ke amfani da intanet wajen mu'amalarsu ta jima'i.

Binciken ya nuna cewa rabin mutanen da shekarunsu ke tsakanin 16 zuwa 24 sun aika ko kuma sun karɓi hotunan batsa ta wayoyinsu a cikin shekarar da ta gabata.

Haka kuma, daya daga cikin mata biyu, da kuma kusan tara cikin goma na maza a wannan rukunin shekaru, sun ce sun taɓa kallon fina-finan batsa.

Sai dai binciken ya gano cewa kashi ɗaya bisa uku na matasan ba su taɓa yin jima'i ba, adadin da ya karu daga kashi ɗaya bisa biyar a binciken da aka gudanar shekaru 12 da suka gabata.

Binciken ya kuma nuna cewa mutanen da shekarunsu ba su kai 45 ba na yin jima'i a ƙasa da yadda suke yi a baya.

A matsakaita, yanzu suna yin jima'i sau biyu a wata, sabanin sau ɗaya a mako a shekarar 1990.

Manya 'yan ƙasa da shekara 45 suma ba sa yin jima'i sau biyu a wata, a matsakaici, ƙasa da sau ɗaya a mako a shekarar 1990.

Rashin jima'i, ƙarin batsa?

Fiye da kashi ɗaya bisa uku (37%) na mata sun ce sun kalli fina-finan batsa a cikin shekarar da ta gabata.

A bangaren maza kuwa, adadin ya kai kusan kashi huɗu cikin biyar (81%).

Daga cikin matasan da shekarunsu ke tsakanin 16 zuwa 24, rabin mata da kuma mafi yawan samari, wato kashi 86%, sun ce suna kallon fina-finan batsa.

Binciken ya kuma nuna cewa kallon fina-finan batsa da kuma yin wasa da al'aura ba su da yawa a tsakanin mutanen da ba su taɓa yin jima'i ba.

Masu gudanar da binciken sun ce hakan na nuna cewa ayyukan da mutum ke yi shi kaɗai ko kuma ta intanet ba lallai ne su maye gurbin jima'i tsakanin mutane ba, duk da cewa ba su da cikakken tabbacin hakan.

Masu binciken sun ce ba su yi tambayoyi kan amfani da fasahar (AI) ko kuma kulla alaƙar soyayya da manhajojin kwamfuta da ke kwaikwayon hirar masoya ba.

Sai dai sun ce akwai yiwuwar su haɗa irin waɗannan tambayoyi a bincike na gaba.

Jinkirta fara yin jima'i

Binciken Natsal na huɗu ya bayyana sauye-sauyen da ake samu, amma bai iya yin cikakken bayanin dalilan da ke haddasa su ba.

Binciken da ya gabata, wanda aka gudanar a shekarar 2010, ya nuna cewa babban abin da matasa ke nadamar yi shi ne fara yin jima'i da wuri, a lokacin da suke rasa budurcinsu.

Sai dai yanzu, alamu na nuna cewa mutane da yawa na ƙara jinkirta fara yin jima'i.

Kusan mata biyu cikin biyar (38%) da kuma fiye da ɗaya bisa huɗu na samari (28%) sun ce ba su taɓa yin jima'i ba. Wannan ya karu daga kusan mutum ɗaya cikin biyar a binciken da aka gudanar a shekarun 1990, 2000 da 2010.

Haka kuma, mafi yawan manya da ke yin jima'i yanzu suna yin sa ne a ƙasa da yadda suke yi a baya. A da, matsakaicin yawan yin jima'i sau ɗaya ne a mako, amma yanzu ya koma sau ɗaya a kowane mako biyu.

Sabbin sakamakon binciken, wanda aka wallafa a mujallar *The Lancet*, ya dogara ne kan tambayoyin da aka yi wa mutane 6,700 masu shekaru 16 zuwa 59, waɗanda aka zaɓa ba tare da nuna bambanci ba a faɗin Birtaniya.

Binciken ya gano cewa:

- Kashi uku cikin huɗu na manya sun yi jima'i a cikin shekarar da ta gabata.

- Matsakaicin yawan abokan jima'i da mutum ya taɓa samu a rayuwarsa shi ne biyar.

- Mata na yin jima'i sau ɗaya a wata, yayin da maza ke yin sa sau biyu a wata, a matsakaita.

- Yawan mutanen da suka ce sun taɓa yin jima'i da wanda ke jinsi ɗaya da su ya karu, a tsakanin maza da mata, amma ba a iya tantance ainihin yawan karuwar ba.

Yin jima'i ba tare da kariya ba

Alkaluman binciken sun nuna cewa da yawa daga cikin al'ummar Birtaniya, musamman matasa, na yin jima'i ba tare da amfani da hanyoyin kariya ba, lamarin da ka iya haifar da ɗaukar ciki da kuma kamuwa da cututtukan da ake yaɗawa ta hanyar jima'i (STIs).

Haka kuma, amfani da magungunan hana ɗaukar ciki na mata ya ragu a tsakanin matasa mata.

Sai dai yawan matan da ba su taɓa haihuwa ba, amma suka ce ba sa son haihuwa, ya ƙaru sosai.

Adadin ya ninka cikin shekaru 10 da suka gabata, inda ya tashi daga kashi 8% zuwa 17% a tsakanin matan da shekarunsu ke tsakanin 16 zuwa 44.

Wata mai binciken, Dakta Laura Oakley daga Makarantar Kiwon Lafiyar Jama'a da Magungunan Zafi ta Landan (LSHTM), ta ce:

"Ya kamata a mayar da hankali kan fahimtar abubuwan da ke haddasa wannan sauyi, ko matsin tattalin arziki ne, fargabar illolin sauyin yanayi ko kuma sauyin abubuwan da mutane ke bai wa muhimmanci a rayuwarsu.

"Wannan na da muhimmanci ga bincike da manufofin da za a tsara a nan gaba, saboda yana da tasiri kan shirye-shiryen samar da ayyukan kiwon lafiya, kulawa da kuma hidimomin da suka shafi iyali."