Yadda sabon bincike ke kawo fatan daƙile alamomin zuwan jijjiga

    • Marubuci, Kate Bowie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Lokacin da Maria Patzwald mai shekara 38 ta samu juna biyun ɗanta na biyu, da farko ba ta samu wata damuwa ba. "Komai na tafiya daidai - har sai da ta fara ganin baƙon abu," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Ta ce tana tunanin da za ta haifi jaririn kafin lokacin da ta haife shi kuma da ya fsukanci ƙalubale da ba ta samu kulawa ba.

Lokacin da cikinta ya kai mako 32, an gano Maria tana fama da alamomin zuwan jijjiga wato pre-eclampsia a Turancin Ingilishi - wata babbar matsala da ke kisa da ke faruwa sakamakon hawan jini - kuma an shaida mata cewa tana buƙatar ta zauna a asibiti har sai ta haihu.

Yayin da ta zaƙu ta haihu, an sanya ta cikin mata 16 da za a yi gwajin wani tsari da masana kimiyya ke fatan zai iya warkar da matsalar tun daga tushe a karon farko.

Matsalar na janyo mace-macen mata sama da 70,000 da jarirai 500,000 a faɗin duniya duk shekara tare da wasu matsalolin da ke da nasaba da hawan jini.

Duk da yaɗuwar matsalar, tsawon shekaru babu maganinta inda likitoci suka gaza dakatar da matsalar da zarar ta fara. Magani ɗaya tilo har yanzu shi ne haihuwa.

A farko-farkon gwajin tsarin, masana kimiyya a Amurka suna nazari kan sinadarin protein da suke gain wataƙila yana kawo alamomin zuwan jijjiga, don su ga ko tsame shi daga jinin uwa zai iya inganta lafiyarta ya kuma kare haihuwa kafin lokaci.

Masanan sun gano mata 16 da suka haifi bakwaini da suka yi fama da alamomin zuwan jijjiga sun samu ƙarin kwana 10 kafin su haihu kuma ba su fuskanci wata matsala da ta shafi jariransu ba, inda suka wallafa sakamakon nazarin a mujallar Nature Medicine.

Ga Maria, hakan na nufin ta haifi ɗanta Bennet yana mako 34, wani gagarumin ci gaba a batun juna biyu da ke bai wa bakwaini damar rayuwa.

Dabarar tace jini

Yayin da masana kimiyya ba su da tabbaci, bincike ya nuna cewa alamomin zuwan jijjiga na faruwa ne a lokacin da mahaifa ta samu matsala, lamarin da zai sauya yadda jini ke gudana a cikin jiki inda kuma yake shafar hawa da saukar jini na uwa.

Hawan jinin da yake janyowa na iya haifar da bugun jini da taɓuwar wata gaɓa.

An fi yawan samun matsalar daga mako na 20 da mace take da juna biyu ko kuma da zarar an haifi jariri, ana iya gano shi ne a lokacin da uwa take zuwa awo da gwajin fitsari.

Sauran alamomin sun haɗa da matsanancin ciwon kai da magani ba ya warkar da shi, matsalar gani da jin zafi a ƙasan haƙarƙari da kumburin fuska, hannu ko ƙafafu.

Gwajin, wanda wata tawaga daga cibiyar likitoci ta Cedars-Sinai a Amurka ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ravi Thadhani da Farfesa Ananth Karumachim, ya ƙunshi ɗaukan jinin mata, tace sinadarin protein da ake kira sFlt-1 da suka tunanin yake rura matsalar tare da maido da shi jikin matan a wani tsari irin na wankin ƙoda.

Yayin da matan da aka gano da matsalar ake iya ba su magunguna domin kare jijjiga tare da kula da jininsu, ana iya waraka ne kaɗai da zarar mace ta haihu - sai dai haihuwar bakwaini na janyo hatsari ga jaririn.

Wasu daga cikin matan irin su Maria daga Jamus, sun yi gwaje-gwaje da dama a binciken. Kulawar da aka bai wa jaririnta ta ƙara ba shi damar ƙara mako biyu a cikin mahaifiyarsa.

"Idan aka haifi jariri a mako na 34 ko fiye, yiwuwar a ce ba su da wata matsala ta lafiya suna da yawa," in ji shi.

Jagororin binciken na ganin cewa bayar da kulawa zai iya taimakawa mata su kaucewa haihuwar bakwaini.

"Burin shi ne a soma da wuri a kuma riƙa bayar da kulawa a kai a kai...idan muka soma da wuri, wataƙila mu iya hana haihuwar bakwaini," in ji Thadhani.

Rashin tabbas

Farfesa Asma Khalil da ke asibitin St George a London ta ce matan da ke nuna alamun zuwan jijjiga, har ma su samu ƙarin kwanaki na iya zama muhimmin abu ga jaririn.

Yayin da take ganin tsarin dabara ce mai kyau, batun ko tace jini ba shi da wata matsala ga uwa da jaririnta wani abu ne da har yanzu ba a tabbatar ba, in ji Andrew Shennen, shugaban ƙungiyar Charity Action kan alamomin zuwan jijjiga kuma farfesa kan lafiyar uwa da ɗan tayi a Kwalejin lafiya ta King's College da ke London.

Akasarin mata da suka mutu sanadin alamomin zuwan jijjiga na zaune ne a ƙasashe marasa ƙarfin tattalin arziki da ke fama da rashin wuraren kula da lafiya, in ji shi. Wataƙila waɗannan matan ba lalle ba ne su ci gajiyar tsarin tace jini, in ji shi.

"Muna da fasahar da za ta kawo sauyi a gobe idan muka inganta wasu abubuwan," kamar yadda ya jaddada.

Sai dai Thadhani ya ce injin da ake buƙata na tace jinin iri ɗaya ne da na wankin ƙoda.

Abin alfahari ne gare ni

Thadhani ya ce a shekara mai zuwa za a soma gagarumin nazari kan magani kuma yana fatan cewa za a samu maganin a asibitoci cikin shekara uku zuwa biyar.

"Ba za mu kasance a nan ba idan babu jarumai mata da suka amince su ba mu haɗin kai... [su ne] jaraumai, in ji shi.

Maria ta ce abin burgewa ne a yi tunanin cewa binciken da aka yi a kan ta na iya taimakawa mata da jarirai, inda kuma ta bayyana godiyarta ga damar da ta samu.

"Kwanaki da suka gabata, na yi magana da wasu mata a kan lamarin inda suka nuna godiyarsu gare ni saboda yadda na samu ƙwarin gwiwar bayar da gudunmawa da kuma taimakawa wajen inganta rayuwar jarirai da mata," in ji ta.

"Sai kuma na gane cewa abu ne da zan iya alfahari da shi."