Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Flick ne zai jagoranci wasan Barca da Real duk da mutuwar mahaifinsa
Kocin Barcelona Hansi Flick ne zai jagoranci ƙungiyar a wasan El Clasico da za su fafata da Real Madrid duk da rashin mahaifinsa da yayi.
Za a nuna alhinin rashin mahaifin nasa a Nou Camp, inda za a yi shiru na minti ɗaya gabanin sa wasa, kuma 'yan wasan za su ɗaura baƙin kyalle yayin fafatawar.
Yayin da ta sanar da mutuwar a yammacin Lahadi, Barcelona ta ce: "Barcelona da sauran iyalanta na aika saƙon ta'aziyyarta ga Hansi Flick na mutuwar mahaifinsa.
"Muna jajantawa tare da lahinin rashin mahaifinka tare da miƙa gaisuwarmu ga duka iyalan gidanka a wannan lokaci na alhini."
Flick mai shekara 61, zai iya ciwa Barcelona gasar sau biyu a jere idan ya yi nasara ko ya yi canjaras da Real.
Tsohon kocin Bayern Munich ɗin da Jamus ya lashe kofuna hudu da da Barcelona tun lokacin da ya maye gurbin Xavi a watan Mayun 2024.
Abokan hamayyarsu Madrid suma sun wallafa cewa, "Real Madrid da Shugabanta da sauran ma'aikatanta na miƙa jajensu da ta'aziyyarsu ga Hensi Flick na rashin mahaifinsa."