Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Rasha na son ganin an kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya?
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban Rasha Vladimir Putin ranar Litinin a wayta ziyarar bazata.
Araqchi ya je St Petersburg ne daga Islamabad, wajen da ake tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, duk da cewa wakilan Amurka ba su je Pakistan ba a wannan karo.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yanke shawarar kin tura waɗanda za a tattauna da su zuwa Islamabad.
A cewar rahotannin kafafen yaɗa labarai, Tehran ta faɗa wa Amurka cewa a buɗe mashigar Hormuz, sannan a kawo karshen yaƙi, sai kuma a ɗage batun tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran zuwa wani lokaci.
Sai dai, Amurka na kallon nukiliyar Iran a matsayin abin da ya fi muhimmanci a tattauna a kai.
Me ya sa ministan harkokin wajen Iran ya kai ziyara Rasha? Shin yaƙin ya kusa zuwa karshe? Wa ke jagorantar Iran yanzu?
Waɗannan na daga cikin tambayoyin da sashen Rasha na BBC ya tattauna da wani kwararre kan Iran mai suna Nikita Smagin.
BBC: Mu tattauna kan ziyarar Araqchi zuwa Rasha. Mun gan shi a Islamabad, amma tawagar Amurka ba ta je Pakistan ba. Ya kuma je St. Petersburg inda ya haɗu da Putin. Me suka tattauna a kai kuma me suka cimma?
Nikita Smagin: Idan muka duba bayanan da suka fito lokacin tattaunawa da kuma bayan haka, za mu sun fayyace komai kai-tsaye;
Rasha na goyon bayan Iran, Rasha za ta yi komai don samar da zaman lafiya, Putin ya samu sako daga jagoran addinin ƙasar. Haka batun yake a ɓangaren Iran ma.
A taƙaice babu wani sabon bayani. Idan muka yi magana kan yanayin tattaunawar, za mu iya cewa ministan wajen Iran ɗin bai gana da takwaransa kaɗai ba, amma har da Putin.
A ɗaya gefen, mun san ba komai da aka tattauna a kai za a bayyana ba. Amma jigon tattaunawar ba zai wuce ta taimakon soji ba.
BBC: Putin ya ce Rasha na son ganin an samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, sai dai ana ganin kamar yanayin da ake ciki yana da alfanu ga Rasha, saboda an cire tankar man ta daga cikin takunkumin Amurka na wucin gadi. Kuma kamar tana cin gajiyar abin da ke faruwa a mashigar Hormuz.
Nikita Smagin: Gaskiyar ita ce, ybazuwar rikici a yankin Gulf na da alfanu ta wani bangare ga Rasha, idan aka duba abubuwan da ke wakana yanzu.
Yanayin da ake ciki na sanya matsin lamba sosai kan farashin mai kuma ana buƙatar man Rasha. Har ƙasashen da suka daina sayan mai daga Rasha na ɗan wani lokaci, kamar Indiya, suna komawazuwa ga ƙasar yanzu.
Yanzu Rasha na son bai wa Iran taimakon soji. Abu mafi muhimmanci shi ne Rasha na bai wa Iran bayanan sirri kan yaƙin da ake yi.
Akwai kuma hujjar cewa Rasha ta tura ko tana shirin aika jiragenta marasa matuki na Shahed.
Kuma a tsawon shekaru biyu da suka wuce Rasha na bai wa Iran makamai da za ta yi amfani da su kan Amurka ko Isra'ila ko kuma ƙasashen Gulf, kamar jirage masu saukar ungulu, makamai da kuma motoci masu sulke.
Amma an fi amfani da da irin waɗannan kayaki wajen ayyuka a cikin Iran ɗin kamar murksuhe masu zanga-zanga ko kuma daƙile duk wata barazana ta bore, maimakon fito na fito da Amurka da Isra'ila.
Shiga fagen daga
BBC: Wani lamari da ke faruwa shi ne, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya fi kasancewa sosai a Gabas ta Tsakiya a yanzu fiye da Turai, inda yake taimakon ƙasashen Gulf wajen samun tsarin tsaro na sama da kuma amfani da ƙwarewar Ukraine a wannan fanni, musamman wajen magance jiragen leƙen asiri na Iran, waɗanda suka kasance na Rasha Gran-2s.
Duk da cewa ba a tabbatar da wannan bayani ba, amma idan ya tabbata hakan na nufin cewa Rasha da Ukraine sun sauya aƙala zuwa Gabas ta Tsakiya, kuma sun kara aikin da suke yi. Me kake tunani kan haka?
Nikita Smagin: A ɗaya gefen, mun ga Rasha da Ukraine sun shiga Gabas ta Tsakiya kuma suna ƙokarin taka rawa a can; kowa yana wani ɓangare a daban, kuma shakku kan haka.
Sai dai a ɗaya gefe, ba su shiga cikin rikicin da ake yi dumu-dumu ba, illa masu taimako a gefe. Kuma ana ganin suna yin haka ne saboda kulla alaka da za ta yi amfani nan gaba.
Ba wani abu bane idan aka yi tunanin cewa Rasha za ta goyi bayan Iran - alal misali, taimakonta wajen bai wa Iran bayanan sirri - don daƙile bayann sirrin da Amurka za ta bai wa Ukraine. Duk da cewa babu hakan a yanzu, amma za a iya samu.
Duk da cewa ba lallai ne goyon bayan Ukraine ya yi tasiri a yankin ba, amma zai kawo bambanci a wasu ɓangarori.
Me ya faru da tattaunawa da ake yi?
BBC: Mu duba batun tattaunawar Amurka da Iran. Me ya aka kasa ci gaba da ita? Araqchi ya je Islamabad, sai dai Trump ya yanke shawarar kin tura wakilansa, Steve Whittaker da Jared Kushner, waɗanda aka sa ran za su yi balaguro zuwa Pakistan. Mece ce matsalar?
Nikita Smagin: Wannan zai iya zama wani tunani na Trump. A baya, Iran ce ta ki hakartar tattaunawar, kuma lamarin ya zama wani iri. Kuma babu wani ɓangare da yake son ya je ya yi ta jira.
Sai dai a yanzu za a iya cewa an kasa cimma matsaya kan tattaunawa. Amma akwai alamun cewa Amurka ta dan sassauta. Babu wasu ƙarin sharuɗa masu aywa, sai dai mayar da hankali kan shirin nukiliya.
Alamu sun nuna cewa abin da Amurka ke so kawai shi ne Iran ta daina samar da uranium kuma ta amince ta sauya wuraren uranium, yayin da aka jingine wasu batutuwa - aƙalla a yanzu.
Ƙari kuma shi ne akwai batun sake buɗe mashigar Hormuz. Sai dai, Iran ba ta jayayya kan haka kuma tana son buɗe mashigar amma bisa wasu sharuɗa.
Maganar gaskiya inda matsalar take shi ne batun nukiliyar Iran, inda Iran ta nace cewa a bar batun zuwa tattaunawa ta gaba, bayan cimma matsaya kan sauran batutuwa. Wannan na nuna cewa Iran ba ta son ganin kanta a matsayin wadda ta yi rashin nasara a tattaunawar.
Abubuwa da ke ƙara faruwa na nuna cewa duniya na kallon Amurka a matsayin wadda ta sha kaye (ko wadda ba ta yi nasara ba). Ba mu san burin da ƙasar ta shimfiɗa wa kanta ba, kuma ba mu san abin da Trump ke son cimma wa ba.
Wa ke jagorantar Iran?
BBC: Ina so in yi tambayar cewa wai wanene ke jagorantar Iran a halin yanzu. Abbas Araqchi ya kai ziyara Rasha kuma yana jagorantar tattaunawa da Amurka, amma waye ainihi yake da iko na mulki a Iran? Mojtaba Khamenei bai bayyana a bainar jama'a ba kuma a cewar wasu bayanan sirri an jikkata shi.
Nikita Smagin: Bayan kashe muhimman jagorori masu yanke hukunci, tsarin iko na ƙasar ya shiga wani yanayi.
A ɗaya gefe, abun da ya fito ƙarara shi ne waɗanda suka fi tasiri a yanzu su ne dakarun juyin juya-hali. Sai dai ita rundunar kanta ba a haɗe yake ba kuma akwai ɓangarori da dama da kuma gaba.
A wani ɓangare alamu sun nuna kakakin majalisar Iran Mohammad Baqer Ghalibaf wanda shi ma ya fito daga rundunar ta IRGC, yana son cimma matsaya da Amurka ko kuma aƙalla a ci gaba da yin tattaunawa, sai dai hakan ya citura.
Wannan ya nuna cewa lamarin yana da tsarkakiya. Wasu manyan jagorori ciki har da kwamandan IRGC, Ahmad Vahidi, yana da majalisar mambobi huɗu da ke yi masa aiki, duk da cewa ba a tabbatar da bayanan ba.
Har ila yau, Mohammad Baqer Zolghadr, shugaban kwamitin majalisar tsaron ƙasar, wanda ya maye gurbin Ali Larijani, wani soja ne da ke tsattsauran ra'ayi. Ga alama masu tsattsauran ra'ayi ne ke da rinjaye.
A yanzu, duk abin da Iran ke yi sai an ji shawarar manyan jagorori da dama kafin yanke hukunci ko ɗaukar mataki, saboda kowa yana da muhimmanci.