Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Cardinal Onaiyekan, kuma me ya haɗa shi da fadar shugaban ƙasa?
Kusan mako guda ke nan ana ta musayar yawu tsakanin fadar gwamnatin Najeriya da wasu ƴan siyasa musamman na ɓangaren hamayya, tun bayan da babban malamin addinin Kirista na Najeriya, Cardinal Onaiyekan ya fito ya nuna irin halin da ƴan Najeriya ke ciki.
Onaiyekan dai ya bayyana damuwarsa kan tsadar rayuwa da wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta, a yayin hira da yan jarida jim kaɗan bayan wata ganawar sirri da malaman addinin Kirista suka yi da shugaba Tinubu a fadar gwamnati.
Hakan ne ya sa fadar gwamnatin ta Najeriya ta ce malamin na addinin Kirista bai kyauta ba saboda yadda ya bayyana abin da aka tattauna a sirri da shugaban ƙasa sannan kuma aka zarge shi da yi wa abokan hamayya aiki.
Sai dai kuma tuni ƴan hamayyar a Najeriya suka fara mayar da martani tare da gasgata abin da Oneiyekan ya faɗi da kuma ba shi kariya.
Abin da Onaiyekan ya faɗi
Da yake magana bayan taron manyan malaman addinin Kirista a fadar shugaban ƙasa, Cardinal Onaiyekan ya ce malaman sun shaida wa Shugaba Tinubu cewa Najeriya na "zubar da jini", wato ƙasar na fuskantar mawuyacin hali, kuma jama'a da dama na fama da tsananin matsin tattalin arziki.
Ya kuma yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu bai amince da bahasin da suka ba shi kan yanayin da ƙasar ke ciki, inda shugaban ya dage cewa tattalin arzikin ƙasar na tafiya yadda ya kamata.
"Mun faɗa masa cewa tattalin arzikin ƙasar ba ya taimaka wa talakawan Najeriya, amma shi ya dage cewa tattalin arzikin na tafiya daidai kuma yana cikin yanayi mai kyau," in ji Onaiyekan
Har ila yau, Cardinal ɗin ya bayyana cewa manyan malaman sun kuma tattauna batun babban zaɓen 2027 tare da jaddada muhimmancin kare sahihanci da amincin tsarin zaɓe domin tabbatar da zaɓe na gaskiya da adalci.
Martanin fadar shugaban kasa
Fadar shugaban ƙasa a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban, Temotope Ajayi ya fitar ta soki Cardinal Onaiyekan da cin amanar abin da aka tattauna a sirri.
"A ganina, akwai abin da bai dace ba a yadda Cardinal John Onaiyekan ya yi hira da tashar talabijin inda ya ba da nasa labari da fassarar abin da ya faru a ganawar sirri tsakanin ƙungiyar Bishof-bishof na Katolika ta Najeriya da Shugaba Bola Tinubu. A fahimtata, wannan cin amanar wata dama ce ta musamman da matsayinsa na malamin addini ya ba shi," in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa tsarin mulki ya bambanta da yadda malaman ke gudanar da tsarin coci-cocinsu.
"Abin da malaman addinin ke yawan mantawa a irin waɗannan tsoma-bakin shi ne, tafiyar da ƙasa ya sha bamban da jagorantar coci. A tsarin dimokuraɗiyya, kowace ƙungiya mai ruwa da tsaki, ciki har da Cocin Katolika, na da cikakken 'yancin neman gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen gudanar da ayyukanta. Wannan wani ɓangare ne na shiga cikin harkokin dimokuraɗiyya."
Onaiyekan na yi wa ƴan hamayya aiki - Wike
Shi kuma ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyeson Wike ya bayyana kalaman na Cardinal Onaiyekan da na tallafa wa abokan hamayya.
Wike ya yi waɗannan kalamai ne yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Talata, inda yake mayar da martani kan bayanan da Cardinal Onaiyekan ya yi.
"Idan aka ga ko aka fahimci cewa wani shugaban addini yana goyon bayan wani ɓangare, kuma hakan a fili yake, to zai yi wa mutane wuya su ɗauki irin waɗannan kalamai a matsayin waɗanda za su amfani al'umma ko su taimaka wajen magance matsaloli," in ji Wike.
Amaechi ya kare Onaiyekan
Tsohon Ministan Sufuri kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, Rotimi Amaechi, ya kare Cardinal John Onaiyekan daga zarge-zargen cewa sukar da ya yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana da alaƙa da siyasa.
Amaechi ya ce Onaiyekan ba ya goyon bayan wata jam'iyyar siyasa ko wani ɗan takara, sai dai yana magana ne kan wahalhalu, talauci da cin hanci da rashawar da ke addabar 'yan Najeriya.
Tsohon Ministan Sufuri ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Talata yayin da ya bayyana a shirin Politics Today na tashar talabijin ta Channels Television.
"Ba ya goyon bayan kowa. Ina yawan haɗuwa da Cardinal Onaiyekan; har ma ina ibada a ɗakin ibadarsa na kashin kai. Cardinal Onaiyekan da kansa ba ya goyon bayan kowa. Mun yi tattaunawa da shi sau da yawa. Abin da kawai ke damun sa shi ne irin yadda ake tafiyar da al'amura ba tare da taka-tsantsan ba, da kuma yawan talauci da cin hanci da rashawa da ke addabar ƙasar. Waɗannan su ne abubuwan da ke damun sa," in ji Amaechi.
Wane ne John Cardinal Onaiyekan?
John Cardinal Onaiyekan fitaccen malamin addinin Kirista ne a Najeriya kuma ɗaya daga cikin manyan jagororin Cocin Katolika da suka yi fice a Afirka.
An haife shi a ranar 29 ga Janairun 1944 a jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
John Onaiyekan ya taɓa zama Archbishop na Abuja wato babban limamin Katolika na yankin Abuja.
A shekarar 2012, Faparoma Benedict XVI ya naɗa shi Cardinal, wanda ya sanya shi cikin manyan jagororin Cocin Katolika a duniya.
Ya yi fice wajen kira ga zaman lafiya, haɗin kan addinai, da kuma magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki.
Sau da dama yana bayyana ra'ayinsa kan harkokin ƙasa, musamman batutuwan talauci, cin hanci da rashawa, zaɓe, da shugabanci.