Yadda aka yi wa jariri tiyata tun yana cikin mahaifiyarsa

    • Marubuci, Camilla Horrox
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan lafiya
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Likitoci sun yi amfani da wata sabuwar dabara ta musamman wajen yi wa wani jariri tiyata tun yana cikin mahaifiyarsa.

An yi wa mahaifiyarsa, Maisie Savage daga Landan, tiyata a Amurka lokacin da cikinta yake mako 26.

Jaririn nata mai suna Theo, wanda a yanzu yake da watanni biyar da haihuwa, na cikin koshin lafiya.

Tun da farko likitoci sun gano jaririn na auke da wata cuta da ake kira gastroschisis, wadda ke faruwa idan cibiya ba ta girma yadda ya kamata ba, lamarin da ke sa hanji ya fito ya girma a wajen ciki.

Likitocin sun ɗan buɗe mahaifar, sannan suka yi msa tiyata tare da mayar da hanjin cikin sauki.

Theo shi ne jariri na uku a duniya da aka yi wa irin wannan aiki, amma irin nasa ne na farko a duniya.

Girman matsalar lalurar a duniya

Maisie mai shekara 29 da mijinta Josh French, mai shekara 36, dukkansu malaman makaranta ne, sun ce sun ji matuƙar daɗin nasarar wannan sabuwar tiyata ta musamman.

"Wannan abin al'ajabi ne da ba mu taa tsammani ba?" kamar yadda Maisie ta shaida wa BBC.

Irin wannan lalura na shafar jariri ɗaya cikin kowane jarirai 3,000 da ake haifa a Birtaniya a kowace shekara.

A faɗin duniya kuwa, yawan masu fama da cutar gastroschisis ya bambanta sosai daga yanki zuwa yanki.

Nahiyar Kudancin Amurka ce ke da mafi yawan masu fama da wannan matsalar, a cewar wani nazari na duniya da aka gudanar a shekarar 2025 kan bincike daga ƙasashe masu matsakaicin da kuma manyan kuɗaɗen shiga.

Bayanai daga ƙasashe masu ƙarancin kuɗaɗen shiga kuwa ba su da yawa.

A yanayin da abubuwa suka fi sauƙi, jariran da aka haifa da wannan matsala kan buƙaci shafe makonni a sashen kula na musamman, tare da samun abinci ta bututu ko kuma ta hanyar allurar jini (IV), baya ga tiyatar gyara matsalar.

Amma a lokuta masu matuƙar rikitarwa kamar na Theo, sakamakon kan fi tsanani, inda jariri kan iya shafe har watanni shida a sashen kula na musamman na jarirai, a yi masa tiyata sau da dama, sannan a ci gaba da ba shi abinci ta hanyar allurar jini har na tsawon shekara biyu, tare da yiwuwar buƙatar dashen hanji.

Ko da an samu kulawar likitanci mafi inganci, jariri ɗaya cikin goma da ke fama da wannan matsala kan rasa ransa.

Yadda aka gano cutar

Da farko, iyayen Theo ba su da masaniyar cewa akwai wata matsala da jaririnsu da ke cikin ciki yake fama da ita.

"Yayin da muke dab da zuwa yin gwajin hoton ciki na makonni 20, abin da ke zuciyarmu kawai shi ne farin cikin ganin hoton jaririnmu," in ji Josh. "A lokacin ma ba mu san cewa namiji ne ba."

Josh ya ce gano cewa jaririn nasu na fama da gastroschisis ya girgiza su sosai kuma ya tayar musu da hankali tare da jefa su cikin fargaba.

Lokacin da cikin ya kai makonni 24, ƙwararrun likitoci a Asibitin Great Ormond Street (GOSH) da ke Landan sun fara faɗa wa Maisie da Josh, yadda watanni shida na farkon rayuwar Theo za su kasance.

Sai dai bayan da aka gano cewa Theo yana da wata nau'in cutar da ta fi tsanani, sai likitocin suka tura shi zuwa Asibitin Yara na Texas da ke birnin Houston.

A can ne wata tawagar likitocin tiyata masu kula da jarirai tun suna cikin mahaifa da kuma na yara, ƙarƙashin jagorancin Dakta Michael Belfort, suka jagoranc aikin tiyatar mayar da Thoe hanjinsa.

Dakta Belfort, wanda ya jagoranci aikin, ya taɓa jagorantar irin wannan tiyata ta laka da ake kira ''spina bifida''.

Yadda aka gudanar da aikin

An shaida wa Maisie cewa dole ne ta je Texas a Amurka, ta kuma zauna a can har zuwa lokacin haihuwarta.

"Gagarumin mataki da dole ne mu ɗauka, domin ceto rayuwar jaririnmu,'' in ji ta.

A matsayin wani ɓangare na aikin, da farko ta je Asibitin Leuven da ke Belgium, inda ƙwararrun likitoci suka yi mata allurar Botox ta cikin mahaifa zuwa fatar cikin jaririn nata, wanda z ata taimaka wajen sassauta tsokar cikin ta yadda aikin zai zo da sauƙi.

Daga nan ne iyalan suka tashi zuwa Texas, inda aka yi tiyatar a watan Nuwamban bara, lokacin da cikin ya kai makonni 26.

Josh ya ce lokacin da likitoci ke yi wa Maisie tiyatar ya shiga tsananin damuwa da fargabar yadda aikin zai kasance.

"Tsawon wuni ya kasance tamkar mako guda a gareni,'' in ji shi.

"Kana jira ba tare da sanin ainihin halin da ake ciki ba."

An ɗan fito da mahaifar Maisie waje domin auna mahaifar da kuma jaririn yadda ya dace.

Daga nan aka fitar da ruwan (amniotic fluid) da ke kewaye da jaririn, aka maye gurbinsa da iskar carbon dioxide (CO₂) domin faɗaɗa wurin da za a gudanar da aikin tiyatar.

Ta hanyar tiyatar, likitocin suka samu nasarar mayar da hanjin Theo zuwa cikinsa, sannan suka ɗinke wajen domin rufe shi.

'Na sha wahala kafin na warke'

An yi nasarar tiyatar gaba ɗaya, kuma Theo ya ci gaba da zama a cikin mahaifa har zuwa cikar lokacinsa, inda ta haife shi da kanta a watan Fabrairu.

Amma ba kamar sauran mata da ke murmurewa daga irin wannan tiyata ba, ta ci gaba da jinyar raunin tare da jariri a cikinta na tsawon makonni kafin ta haife shi.

Ta ce takan ji motsin Theo da shure-shurensa a cikinsa har zuwa kusa da tabon tiyatar, wanda hakan ke yi mata zafi.

"Na sha wahala soai kafin na warke," in ji Maisie.

Dakta Belfort, shugaban sashen kula da mata masu juna biyu da cututtukan mata a Asibitin Yara na Texas, ya ce shi da tawagarsa sun yi matuƙar farin cikin nasarar tiyatar.

"Komai ya tafi yadda ake fata, daga mahaifiyar, zuwa jaririn, zuwa aikin tiyatar da lokacin da aka yi ta. Haka kuma ba mu samu wata matsala ba a lokacin tiyatar da aka yi wa jaririn tun yana cikin mahaifa ko bayan an kammala ta.

Bayan komawarta gida Landan, Maisie ta ce jaririnta na cikin ƙoshin lafiya kuma yana ci gaba da girma.

"Abin da likitocin suka yi ya sauya gaba ɗaya abin da zai iya zama farkon rayuwa mai matuƙar wahala a gare shi, kuma yanzu shi ne mafi alherin abin da muka samu. A taƙaice dai, jariri ne kamar kowane jariri."

Josh ya ce: "Muna jin mun yi babbar sa'a ƙwarai, muna jinjina ga taimakon da suka bai wa iyalinmu, tun daga tawagar likitocin Asibitin Great Ormond Street har zuwa Dakta Belfort da tawagarsa, duk sun yi mana taimakon da ba za mu manta ba''.

Ya ƙara da cewa: "Sun taimaka wajen sauƙaƙa mana wani lokaci mai cike da firgici da damuwa a rayuwarmu, yanzu muna cikin fari ciki tare da ryuwa da jaririnmu cikin nishaɗi'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.