Ko me ya sa rikicin cikin gida na jam'iyyar ADC ke ci gaba da ƙamari?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ga dukkan alamu rikicin cikin gida da ke addabar jam'iyyar ADC na ci gaba da ƙamari bayan da shugabannin jam'iyyar na jihohi dake takun saƙa da shugabancin Sanata David Mark, sun zarge shi da ƙokarin tilasta mu su sauka ba tare da ƙarewar wa'adin su ba.

Sai dai ɓangaren shugaban jam'iyyar ya ce ihu suke bayan hari, domin ba su fahimci yadda doka da kuma kundin tsarin mulkin jam'iyyar ke aiki ba.

Shugabannin jam'iyyar na jihohi, sun yi zargin cewa shugabancin Sanata David Mark yayi gaban kansa wajen karya doka musamman yadda ya fara sayar da fom ɗin tsayawa takara ba tare da sa hannunsu ko amincewarsu ba.

Muhammad Raji Sulaiman, wanda shine shugaban jam'iyyar ADC reshen jihar Adamawa, ya shaidawa BBC cewa matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam'iyyar da kuma umarnin kotu.

''Ba'a yin abu ba tare da doka ba, doka ta ce kar ayi, su na yi, shi ne mu kam kukanmu','

''Kuma mu na tsoron kan abinda zai je ya jawo muna gaba ɗaya a rusa a rasa.Duk abinda aka gina shi ba a kan ƙa'ida ba, toh abin nan ba zai ɗore ba'', in ji shi

Sulaiman ya ce sun nemi shugabancin su dakatar da tsarin saboda sun shigar da ƙara a gaban kotu kuma tsarinsu ba zai yi tasiri ba.

Ya kuma musanta zargin da ake yi a kan cewa an ɗauki nauyinsu ne shi yasa su ke tayar da zaune tsaye a cikin jam'iyyar:

''Wa zai ɗauki nauyinmu, gaskiya fa ɗaya ce, mu na son mu yi abu ne da zai ɗore, idan muka bari aka tafi a haka, gobe aka je kotu aka je aka rusa, wa ya rasa?''

A ɗayan ɓangaren kuma Faisal Kabir, ɗaya ne daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ADC ya musanta zargin.

''Mu a ranar da mu ka gudanar da babban taro, mun ce mun gudanar da shi amma ba za mu rantsar da shugabannin mu ba sai ranar 19 ga watan Mayu kuma wa'adinsu ya zo ƙarshe''

''Jam'iyya ta na da dama ko da bayan shekara biyu ya rage wa'adin mutum ya zo ƙarshe ta gudanar da zaɓe amma kuma ba za ta ranstar da abun ba, sai lokacin da wa'adin ya ƙare kuma za mu rantsar da sabbin shugabanninmu nan ba da jimawa ba'' in ji shi.

Rikicin cikin gida a jam'iyyar dai na ci gaba da ƙara tsami tsakanin ɓangarorin biyu, inda suke ci gaba da zargin juna da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa, a daidai lokacin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen 2027.