Wane tarihi Pep Guardiola ya kafa a ƙungiyar Manchester City?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Tun farko alamomi sun nuna yiwuwar Pep Guardiola zai bar Manchester City a cikin makon da ya gabata.

A ranar Juma'ar da ta wuce, an tambayi Guardiola ko ziyarar da zai kai filin wasa na Wembley washegari za ta kasance ta ƙarshe a gare shi. Guardiola ya amsa da cewa "ba haka ba ne" saboda har yanzu yana da sauran "shekara ɗaya a kwantaraginsa".

Sai dai yadda ya faɗi maganar cikin wasa da kuma yadda ya fice daga ɗakin manema labarai cikin sauri ya sa mutane da dama suka ƙara zargin cewa zai iya barin aiki da zarar aka kammala kakar bana.

Manchester City ta lashe kofin FA na Ingila karo na uku ƙarƙashin Guardiola, bayan doke Chelsea a ranar Asabar. Wataƙila abin da ya ja hankali shi ne yadda ya ɗauki hoto da kofin tare da kowane ma'aikaci, ɗaya bayan ɗaya.

Kyamarar talabijin ta kuma nuna shi daga nesa ya yi zugum cikin tunani, yayin bikin murnar ɗaukar kofin a filin wasan, kamar yana tananin lokutansa na ƙarshe a katafaren babban filin wasa na Ingila.

Bayan kunnen doki da Bournemouth a ranar Talata a gasar Premier League, an sake tambayar Guardiola ko har yanzu zai kasance koci City zuwa ranar Lahadi. Sai ya amsa da cewa dole ne zai tattauna da shugaban ƙungiyarsa cikin kwanaki masu zuwa.

Shin wane kofi ne ya fi shan wahalar ɗauka?

Bayan kusan wasa 600 da ya jagoranci Manchester City, yana da wuya a ware lokaci ɗaya a matsayin mafi girma a zamanin Pep Guardiola a ƙungiyar.

Daga lashe Premier League da haɗa maki 100 a kakar tamaula, zuwa ɗaga kofin UEFA Champions League, har zuwa zama ƙungiya ta farko a tarihi da ta lashe kofin Premier League sau huɗu a jere, Guardiola ya samu manyan nasarori masu yawa sosai.

Amma ana ƙyautata zaton cewa zai nuna nasarar da ƙungiyar ta samu a gasar Champions League ta 2023 a matsayin abin da ya fi alfahari da shi a lokacin da yake horar da City.

Ba wai kawai nasarar da suka samu da ci 1-0 a kan Inter Milan da ta kai ya lashe kofi uku rigis ba (treble) , har ila yau ya haɗa da cika burin City na lashe manyan kofuna da ya yi a lokacin da ya ja ragamar ƙungiyar ta Manchester City.

Tarihin yadda Guardiola ya fara a Man City

Pep Guardiola ya sanya hannu kan kwantiragin kaka uku a farko da Manchester City ta ɗauke shi a watan Fabrairun 2016, domin maye gurbin Manuel Pellegrini kafin fara kakar wasa ta 2016-17.

Ko da yake ya fara da kammala wannan kakar ba tare da lashe kofi ba karo na farko a tarihin aikinsa na koci — sannan kuma bai ɗauki kofi ko da ɗaya ba a kakar wasan bara — amma ƙungiyar City ta mamaye ƙwallon ƙafar Ingila a mafi yawan lokacin jagorancinsa.

City ce kaɗai ƙungiyar da ta taɓa kaiwa ta haɗamaki 100 a kakar Premier League, tarihin da ta yi a kakar 2017-18. A wannan shekarar kuma ta kafa tarihin mafi yawan ƙwallayen da aka ci a kakar wasa guda, inda ta zura ƙwallaye 106 a raga.

A kakar 2022-23, City ta zama ƙungiya ta biyu a tarihin Ingila — bayan Manchester United a 1998-99 — da ta lashe kofuna uku (Treble) a kaka ɗaya: wato Premier League da FA Cup da kuma UEFA Champions League.

Daga baya ƙungiyar Guardiola ta zama ta farko da ta ɗauki gasar Premier League ta Ingila sau huɗu a jere, bayan nasarar da ta samu a kakar 2023-24.

Tsohon ɗan wasan ƙasar Spain ɗin ya sake sanya hannu kan sabon kwantiragin ƙarin shekaru biyu a watan Nuwamban 2024, wanda zai kai shi har zuwa ƙarshen kakar 2026-27.

Yadda Guardiola ya shimfiɗa tarihin lashe kofuna Manchester City

Manchester City ta samu nasarori da yawa a ƙarƙashin Pep Guardiola.

Jimilla, Guardiola ya ja ragamar lashe kofi 20 har da na Premier League shida da Champions League a karon farko a tarihin ƙungiyar.

Ga jerin kofunan da Guardiola ya ɗauka a City:

  • Premier Leagues - 6
  • League Cup - 5
  • Kofin ƙalubale (FA Cup) - 3
  • Community Shields - 3
  • Zakarun Turai (Champions League) - 1
  • Uefa Super Cup - 1
  • Fifa Club World Cup - 1

Ƴan kwallo 11 da Guardiola ya bunƙasa wasanninsu

Yayin da tarihin ƙwallon ƙafa ya ci gaba da sauyawa, sakamakon salon wasan Pep Guardiola mai tsauri da dogaro da mallakar ƙwallo da kai hare-hare, babban tarihin da zai bari shi ne yadda ya gina wasu daga cikin fitattun ƴan wasan duniya.

Daga sake fasalin matsayi da tsarin wasa, yana da baiwa ta gano matasa daga makarantar horaswa, har zuwa haɓaka ɗan wasan da ya lashe kyautar Ballon d'Or, Guardiola ya taimaka wajen bunƙasa da daburan ƴan ƙwallon da yake horarwa.

Yawancin ƴan ƙwallon da suka yi fice a zamaninsa sun bar ƙungiyar ba kawai a matsayin gwarazan Manchester City ba, har ma a matsayin taurarin duniya baki ɗaya.

Jerin ƴan wasan da BBC ta zaƙulo waɗanda Guardiola ya bunƙasa wasanninsu:

  • Raheem Sterling
  • Ilkay Gundogan
  • Kyle Walker
  • David Silva
  • Ederson
  • Kevin de Bruyne
  • Bernardo Silva
  • Rodri
  • Erling Haaland
  • Phil Foden
  • John Stones

Ga yadda aka fassara ƙwazon da wasu ƴan wasa suka yi ƙarƙashin Guardiola:

Kevin De Bruyne — jagoran kirkirar damarmaki kuma zuciyar wasan tsakiyar City.

Erling Haaland — mashahurin mai cin ƙwallaye wanda ya kafa tarihi a gasarPremier League.

Rodri — ginshiƙin wasan tsakiya, kuma gwarzon karawar ƙarshe a gasar Champions League ta 2023.

David Silva — ɗaya daga cikin mafi fasaha da natsuwa a tarihin ƙungiyar.

Sergio Agüero — gwarzo mai cin ƙwallaye wanda ya ci gaba da haskakawa a farkon zamanin Guardiola.

Vincent Kompany — jagoran tsaron baya, kuma kyaftin mai aiki tuƙuru.

Bernardo Silva — ɗan wasa mai iya taka rawar gani a wurare daban-daban.

Phil Foden — ɗan makarantar renon ƴan wasan Manchester City da Guardiola ya gina ya mayar da shi tauraro.

Rúben Dias — wanda ya kawo kwarin gwiwa, kuma katanga a tsaron bayan City.

İlkay Gündoğan — kyaftin ɗin da ya jagoranci City zuwa lashe kofi uku rigis wato Treble a 2023.

Za a saka sunan Guardiola a wajen zaman ƴan kallo a filin wasa na Etihad

Pep Guardiola zai samu wani ɓangare na filin wasan Etihad da za a sanya wa sunansa bayan da ya sanar da cewar zai bar Manchester City, bayan shekaru 10 yana jagorantar ƙungiyar.

Ƙungiyar ta tabbatar da cewa za a sauya sunan ɓangaren ƴan kallo na arewa da ke cikin filin Etihad, wato 'North Stand' zuwa "The Pep Guardiola Stand" domin karrama kocin ɗan kasar Spain, wanda ya jagoranci City zuwa lashe kofin zakarun turai na UEFA Champions League na farko a tarihinta.

Sabon ɓangaren da aka faɗaɗa a Etihad za a buɗe shi a karon farko a ranar Lahadi, lokacin da City za ta karɓi baƙuncin Aston Villa a wasan ƙarshe a kakar Premier League.

Maresca na daf da maye gurbin Guardiola a Man City

Tsohon kocin Chelsea, Enzo Maresca, shi ne ke kan gaba a jerin mutanen da ake sa ran za su maye gurbin Pep Guardiola a Manchester City, domin fara jan ragamar kakar wasa ta 2026-27.

City ta shafe sama da wata shida tana shirye-shiryen yiwuwar rabuwa da Guardiola, kuma tattaunawa da Maresca ta kai mataki na ana daf da kammala komai.

Kocin ɗan Italiya, mai shekara 46, wanda ya kai Leicester City gasar Premier League daga Championship, yana son aikin, kuma ana sa ran za a tabbatar da shi a matsayin magajin Guardiola nan gaba kaɗan.

Maresca ya lashe FIFA Club World Cup da kuma UEFA Europa Conference League tare da samun gurbin buga UEFA Champions League a kakar wasa guda a Stamford Bridge.

Tun kafin hakan, ya yi aiki a Manchester City inda ya kasance mataimaki ga Guardiola a kakar da ƙungiyar ta lashe kofuna uku (Treble) ta 2022-23. Haka kuma ya taka muhimmiyar rawa a makarantar horar da matasa ta ƙungiyar kafin shiga babbar ƙungiyar City.

Tsohon ɗan wasan tsakiya na West Bromwich Albion da Juventus ya bar City a 2023 domin horas da Leicester City.