Fafaroma Leo ya nemi kaɗa ƙuri'a a zaɓen rabin wa'adi na Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Wani ofishin zaɓe a Amurka ya tabbatar da cewa Fafaroma Leo ya nemi a aiko masa da takardar kaɗa ƙuri’a ta gidan waya domin zaɓen rabin wa’adi da za a gudanar mako mai zuwa.
Fafaroman, wanda aka haifa a birnin Chicago, har yanzu yana da rajistar zaɓe a gundumar Will da ke jihar Illinois, inda masu zaɓe za su zaɓi sabon sanata, da wakilan majalisa, da kuma gwamna.
Idan ya cike ya kuma mayar da takardar kaɗa ƙuri’arsa, zai zama Paparoma mai ci na farko da ya taɓa kaɗa ƙuri’a a wani zaɓen siyasa na farar hula.


















