Wane tasiri rundunar tsaron gandun daji za ta yi ga matsalar tsaro a Najeriya?

A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta bayar da umurnin ɗaukar jami'an tsaron gandun daji 1,000 domin taimakawa wajen kuɓuto da malamai da ɗaliban da aka sace a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jihohi da dama musamman a Arewacin Najeriya sun riga sun fara aiwatar da irin wannan tsari
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta bayar da umurnin ɗaukar jami'an tsaron gandun daji 1,000 domin taimakawa wajen kuɓuto da malamai da ɗaliban da aka sace a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Ko da yake ta bayyana cewa ba saboda abin da ya faru a jihar Oyo kaɗai ba ne, ta ce jihohi da dama musamman a Arewacin Najeriya sun riga sun fara aiwatar da irin wannan tsari.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban Bola Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a halin yanzu aƙalla jihohi 10 sun riga sun kafa rundunar tsaron gandun daji, inda kowace jiha ta ɗauki kusan jami'ai 1,000.

Gwamnatin jihar Kaduna ta shaida wa BBC cewa ta fara horas da dakarun tsaron gandun daji 1,000 domin taimakawa wajen kare dazuka da kuma fatattakar masu aikata laifi da ke fakewa a cikin su domin yaƙi da rashin tsaro a jihar.

Tuni wasu suka fara nuna damuwa kan samar da waɗannan dakarun, da tunanin ko kwalliya za ta biya kuɗin sabulu?

Yadda rundunar ta samo asali

A ranar 15 ga watan Mayu, 2025 shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin samar da dakarun gandun daji wato Presidential Forest Guards Initiative domin daƙile matsalar tsaro a dazukan Najeriya.

An fara shirin ne a watan Fabrerun 2024, bayan wata ganawa tsakanin shugaban ƙasar da gwamnonin jihohi, inda ya ba su umurnin ɗaukar dakaru 2,000 zuwa 5,000.

Dakarun za su riƙa lura da motsin da ake yi a dazuka, tare da tattara bayanan sirri da taimakawa jami'an tsaro wajen dakile hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro da wuraren da ba za a iya zuwa ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Maganar ta sake ɗaukar hankali ne bayan sace ƴan makaranta da malamansu sama da 80 a jihohi Borno da Oyo da kuma wasu shida a Zamfara, inda shugaba Tinubu ya ba da sabon umurnin.

Dama dai tuni wasu jihohin ƙasar suka fara aiwatar da tsarin yayin da wasu jihohin ke ci gaba da shirye-shiryen kafa irin wannan runduna.

Daga cikin jihohin da ya ce tuni suka fara aiwatar da tsarin akwai Borno, Yobe, Adamawa, Kwara, Sokoto, Kebbi, Neja, Filato da Benue.

A ɓagaren majalisar dokokin ƙasar ma ta gabatar da ƙudurin dokar da ta amince da ita mai lamba SB477 da kuma HB90 na wani tsari da ake cewa Nigeria Forest Security Establishment Bill, "amma kuma har yau shugaban ƙasa bai sa hannu a kai ba," in ji Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazari kan tsaro a nahiyar Afrika.

Masanin ya ce Tinubu ya yi amfani da ƙarfin ikonsa na shugaban ƙasa ne wajen aiwatar da tsarin na baya-bayan nan da kuma majalisar tattalin arziki.

Ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da ma'aikatar muhalli ta Najeriya ne za su kula da shirin, amma jihohi ne za su ɗauki dakarun.

Wane tasiri rundunar za ta yi?

Kusan jihohi tara da suka rungumi wannan tsari sun ɗauki jami'ai aƙalla 7,000 wanda jami'an tsaron farin kaya na DSS suka ba su horo, kuma har an tura su jihohin da ke fama da matsalar tsaro.

Dr Kabiru Adamu, ya yi wuri a iya gano tasirinsu saboda irin makaman da aka ba waɗannan dakaru bai kai na masu kai hare-hare ba.

"Makamai ne ƙanana waɗanda ba su iya saffara kansu... iyakarsu harsasai biyu," in ji shi.

Ya ce duk gudummuwaar da za su bayar, za su yi ne tare da sauran jami'an tsaro kuma akwai giɓi a dazuka, inda masanin yake ganin abu na farko shi ne dakarun su mamaye dazukan kafin fara wannan aikin.

"Su hana ɓata gari da sauran ƴan bindiga mallakar waɗannan dazuka..., amma kafin haka ya kamata manyan jami'ai da ke da makamai irin sojoji su shige dazuzzukan su tabbatar sun amshe iko da su, in ba haka ba babu abin da zai faru."

Masanin ya ce ƙirƙirar wannan runduna shi ne mataki na farko waje ƙirƙirar ƴansandan jihohi da ake shirin yi, kamar yadda aka tattauna batun a majalisar tattalin arziki wanda mataimakin shugaban ƙasar ke jagoranta da gwamnonin jihohi.

'Kar a saka siyasa a lamarin'

Dr Kabiru ya ce duk da yake an ɗauki matakai wajen ɗaukar dakarun, akwai buƙatar bin tsari mai kyau da cire siyasa a lamarin idan har ana so ya yi tasiri.

Masanin ya bayar da wasu shawarwari ga hukumomin da abin ya shafa, inda yake ganin dakarun za su taimaka sosai wjaen tsare waɗannan dazuka idan ba a kauce daga manufar samar da su ba.

Ya ce akwai buƙatar tabbatar da duk wanda za a ɗauka ya shiga ne domin ya yi aiki da manufa mai kyau, kuma ƴan siyasa su kai zuciya nesa wajen sanya son rai da siyasa a lamarin.

Sannan kuma ya ce ya kamata a tabbatar an saka su cikin tsarin dokokin tsaro na ƙasa, "ba wai wani ɓangare da za su yi zaman kansu ba", saboda waɗanda za su yaƙa suna da makamai waɗanda suka fi nasu.

Ya kuma buƙaci al'umma su ba da goyon baya wajen cin nasarar tsarin.

"Muna da buƙatar wannan tsarin, kuma mu yi haƙuri da kura-kuran da za a yi na farko, idan aka yi kura-kuran aka gyara, za mu ga abin da muke so daga baya".