KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 13/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 13/08/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Mayaƙan Houthi da na al-Shabab na yunƙurin ƙwace Mashigar Bab al-Mandab'

    Mayaƙan Houthi

    Asalin hoton, Mohammed Hamoud/Getty Images

    Jaridar The Telegraph ta Birtaniya ta wallafa wani rahoto mai taken: "Mayaƙan Houthi na shirin buɗe sabon babi a yaƙin Iran, bayan yunƙurin rufe wata muhimmiyar mashigar ruwa ta biyu."

    Jaridar ta ce mayaƙan Houthi, waɗanda a yanzu ake kallonsu a matsayin mafiya ƙarfi cikin ƙungiyoyi masu alaƙa da Iran a yankin, suna shirye-shiryen rufe mashigar Bab al-Mandab domin amfanin Iran, da nufin ƙara matsin lamba kan shugaban Amurka Donald Trump, lamarin da zai iya ƙara jefa tattalin arzikin duniya cikin matsala.

    Rahoton ya ce akwai haɗin gwiwa tsakanin mayaƙan na Houthi da ƙungiyar al-Shabaab da ke Somalia, wanda manufarsu ita ce mallake ɓangarori biyu na mashigar Bab al-Mandab tare da rufe ta idan Iran ta yanke shawarar yin hakan.

    Rahoton ya ambato wata majiya da ta ce mayaƙan Houthi na miƙa fasahar ƙera da amfani da jiragen sama marasa matuƙa (drones) na Iran ga ƙungiyar al-Shabaab bisa umarnin Tehran.

    Manufar hakan, in ji rahoton, ita ce haifar da yanayi a Bab al-Mandab mai kama da wanda ake gani a mashigar Hormuz.

    Jaridar ta ce kimanin kashi 10 zuwa 12 cikin 100 na cinikayyar duniya na bi ta mashigar Bab al-Mandab, wadda ke haɗuwa da Mashigar Suez.

    Telegraph ta yi gargaɗin cewa idan aka rufe mashigar, jiragen ruwa za su tilasta bin wata hanya ta daban wadda za ta ƙara musu makonni suna zagayawa ta kudancin Afirka, lamarin da zai ƙara kuɗaɗen sufuri.

  2. Al'ummar Zambiya na zaɓen sabon shugaban ƙasa

    Wata mata na kaɗa ƙuri'a

    Asalin hoton, Getty Images

    Al'ummar Zambiya na gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin ƙasar.

    Ana kallon zaɓen a matsayin ma'aunin gwajin ingancin dimokuraɗiyya a ƙasar mai tarihin 'ɗorewar tsarin dimokuraɗiyya a Afrika.

    Shugaban ƙasar Hakainde Hichilemana wanda ke neman wa'adi na biyu na da farin jini sakamakon rawar da ya taka lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki.

    Akwai damuwa game da ƙaruwar rashin aikin yi.

    Ana ganin za a fafata ne tsakanin shugaban ƙasar da jagoran adawa Brian Mundibile wanda magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu ke mara wa baya.

    Ɗan takarar shugaban ƙasa dai na buƙatar sama da kashi 50 na ƙuri'u kafin ya yi nasara.

  3. Amurka ta soki Isra'ila kan ci gaba da zaman sojojinta a Lebanon

    Donald Trump

    Asalin hoton, EPA

    Amurka ta yi Allah wadai da ƙawarta Isra'ila, a wani yanayi da ba kasafai ake ganin irinsa ba, bayan ministan tsaron Isra'ila ya dage sojojinsa za su ci gaba da zama a kudancin Lebanon.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana sa rai Isra'ila za ta yi amfani da tsarin yarjejeniyar janye sojoji.

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ne ya yi waɗannan kalamai yayin da ya ziyarci kudancin Lebanon, inda ya tabbatar da yadda sojojinsa ke rusa dukkan gidajen yankin.

    Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya ce ɓarnar da Isra'ila ke yi ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

    Yarjejeniyar ta ƙunshi janye dakarun Isra'ila daga yankunan yayin da sojin Lebanon za su ƙwace makaman ƴan Hezbollah.

    Ministocin Isra'ila na ƙara zafafan kalaman ne a lokacin da zaɓe ke ƙaratowa.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Ahamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.