Juventus da Atletico na hamayya kan Madueke, ƙungiyoyin Premier na rububin Kounde

Asalin hoton, Getty Images
Atletico Madrid da Juventus na zawarcin ɗan wasan gaba na Arsenal da Ingila, Noni Madueke, mai shekara 24. (Telegraph)
Chelsea da Arsenal da Liverpool da Manchester United da Manchester City duk suna bibiyar ɗan wasan baya na Barcelona da Faransa, Jules Kounde, mai shekara 27, inda ƙungiyar ta Spain ke shirin sauraron tayi mai tsoka kan ɗan wasan. (Sport)
Ɗan wasan gaba na Ingila, Harry Kane, mai shekara 33, na gab da kammala yarjejeniyar sabuwar kwantiragin shekara uku da Bayern Munich. (Talksport)
AC Milan na iya sake gwada ɗaukar ɗan wasan gaba na Manchester United ɗan ƙasar Netherlands, Joshua Zirkzee, mai shekara 25, a watan Janairu, mai yiwuwa ta hanyar neman aro tare da zaɓin sayensa daga baya. (Calciomercato)
Arsenal da Liverpool, da Borussia Dortmund na zawarcin ɗan wasan gaba na Fulham ɗan ƙasar Ingila mai shekara 19, Josh King, wanda darajarsa ta kai fam miliyan 51. (4-4-2.ch)
Real Madrid ta ƙuduri aniyar ƙin sayar da ɗan wasan gaba na Brazil Endrick mai shekara 20, duk da sha'awar da Arsenal da Tottenham ke nunawa a kansa. (Teamtalk)
Yiwuwar Tottenham ta samu ɗan wasan gaba na Atletico Madrid, Julian Alvarez, na da ƙarancin gaske, kasancewar ɗan wasan na Argentina mai shekara 26 ya fi son komawa ƙungiyar Barcelona. (Football Insider)
Wakilan ƙungiyoyi daga gasar Premier League da Major League Soccer na sa ido kan ɗan wasan tawagar Colombia ƴan ƙasa da shekaru 20, Edmilson Herazo, mai shekara 18, wanda ke buga wa Barranquilla wasa. (Dan jaridar Colombia, Pipe Sierra)
Liverpool da Manchester United na zawarcin ɗan wasan baya na hagu na Barcelona da Spain, Alejandro Balde, mai shekara 22, wanda kuma Juventus ke son ɗauka. (Calciomercato)
Paris St-Germain ta sake nuna sha'awar ɗaukar Leny Yoro, ɗan wasan baya mai shekara 20 daga Manchester United. (KickFootball)
Ƙungiyoyin Inter Milan da Juventus duk suna zawarcin Giovanni Leoni, ɗan wasan baya ɗan ƙasar Italiya mai shekara 19 da ke buga wa Liverpool wasa. (Tuttosport)































