Yadda na ji bayan Gawuna ya koma wajen Kwankwaso - Ganduje
Yadda na ji bayan Gawuna ya koma wajen Kwankwaso - Ganduje
Lokacin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Ganduje ba ya da ikon ba shi umarni, mutane da dama sun yi mamaki.
A hirarsa da BBC, Abdullahi Ganduje ya ce kalaman na Abba Kabir ba su saɓa wa ɗa'ar jam'iyyar APC ba, sannan ya yi bayanin yadda ya ji bayan Nasiru Gawuna ya koma wajen Kwankwaso.
Ganduje ya yi mataimakin gwamnan Kano sau biyu, ya yi gwamnan jihar wa'adi biyu a jere sannan ya yi shugaban jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.



