Dalilan da suka sa INEC ta tsawaita yin rijistar zabe

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar zaben Najeriya wato INEC, ta kara wa'adin dakatar da yin rajistar zabe a duk fadin kasar da makwanni biyu.

INEC, ta ce hakan zai bayar da karin dama ga wadanda ba su samu yin rajistar ba, da kuma wadanda suka cika shekara goma sha takwas, su samu su yin rajistar.

Mai magana da yawun hukumar, Zainab Aminu Abubakar, ta shaida wa BBC cewa, idan ba a manta ba tun a watan Augustan shekarar 2025, INEC, ta fara yin rijistar zabe inda aka yi zango-zango.

Ta ce,"Bisa ka'ida ya kamata ace na dakatar da yin rijistar a ranar 10 ga watan Yulin, 2026, to amma sakamakon bukata daga 'yan siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu dama wasu al'umma na kasar da suka bukaci a dan tsawaita lokacin yin rijistar, shi y asa mu dauki wannan mataki."

"Yanzu za a dakatar da yin rijistar zaben a ranar 26 ga watan Yulin 2026, kuma muna fatan wannan lokaci da aka kara zai ba wa wadanda ba su samu damar yin rijistar ba damar yinta." In ji ta.Hukumar zaben Najeriya wato INEC, ta kara wa'adin dakatar da yin rajistar zabe a duk fadin kasar da makwanni biyu.

INEC, ta ce hakan zai bayar da karin dama ga wadanda ba su samu yin rajistar ba, da kuma wadanda suka cika shekara goma sha takwas, su samu su yin rajistar.

Mai magana da yawun hukumar, Zainab Aminu Abubakar, ta shaida wa BBC cewa, idan ba a manta ba tun a watan Augustan shekarar 2025, INEC, ta fara yin rijistar zabe inda aka yi zango-zango.

Ta ce,"Bisa ka'ida ya kamata ace na dakatar da yin rijistar a ranar 10 ga watan Yulin, 2026, to amma sakamakon bukata daga 'yan siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu dama wasu al'umma na kasar da suka bukaci a dan tsawaita lokacin yin rijistar, shi y asa mu dauki wannan mataki."

"Yanzu za a dakatar da yin rijistar zaben a ranar 26 ga watan Yulin 2026, kuma muna fatan wannan lokaci da aka kara zai ba wa wadanda ba su samu damar yin rijistar ba damar yinta." In ji ta.

Mai magana da yawun hukumar ta INEC,ta ce," Idan mutum ya bari wannan wa'adi ya cika bai yi rijista ba, to dama ta wuce shi, sai ya jira bayan zaben 2027 kuma."

Ta ce,"Yanzu hukumar INEC ta inganta yadda ta ke yin aikin rijista, misali a baya sai mutum ya je ofishin hukumar kafin ayi masa rijista, to daga baya kuma sai aka saukaka mutum zai iya fara cike bayanansa a wayarsa ta salula ko komputa, sannan sai ka ziyarci ofishin INEC domin a dauki hoton fuska da dan yatsa, to amma yanzu zaka iya amfani da wayarka ko komputarka ka cike bayananka sannnanka dauki hoton fuskarka ba sai kaje ofishin INEC ba."

INEC kan bai wa ƴan Najeriya damar yin rajistar zaɓe a duk lokacin da aka tunkari kakar babban zaɓe a ƙasar.

Dama ce da hukumar ke bai wa ƴan Najeriya da suka cika shekara 18, ko waɗanda wasu dalilai suka hana yin rajistar a shekarun baya ko kuma wani tsautsayi ya sa rijistar tasu ta ɓata.

Katin zaɓe wani ginshikin makami ne a tsarin mulkin dimokraɗiyya da Najeriya ke bi, domin kuwa da shi ake amfani domin samun damar zaɓen shugabanni da wakilai a lokacin zaɓukan ƙasar.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ƴan ƙasar damar kaɗa ƙuri'unsu a lokacin zaɓukan ƙasar, don haka wannan dama ce a gare su na yin amfani a damar da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su.

Haka kuma mallakar katin zaɓen, hanya ce da mutane za su bi domin zaɓar shugabannin da suke so ko sauya waɗanda ba sa so.

Baya ga zaɓe kuma katin zaɓe kan taimaka wajen tantance bayanan mutum da suka ƙunshi suna ko shekaru musamman a bankunan ƙasar.