Ƙasa ɗaya a duniya da ba ta shiga harkokin kwallon ƙafa

Asalin hoton, Paul Watson
Yayin da ƙwallon ƙafa ya kasance ɗaya daga cikin wasannin mafiya shahara a duniya, har yanzu akwai wata ƙasa da ba a damu da wasan ba.
A ƙasar Nauru, wadda wani tsibiri ne da ke tekun Fasikik, wasan kwallon ƙafa bai samu karɓuwa ba.
Amma lamarin ya fara sauyawa bayan da Sifaniya, mai maƙwabtaka da tsibirin ta lashe Gasar Kofin Duniya na 2026.
Nauru ba ta taɓa buga wani wasa na hukumar ƙasa da ƙasa da wata ƙasa ba, sannan ƙasar na da filin wasa guda ɗaya kacal, wanda filayensa ya kasance mai taurin yumɓu maimakon ciyawa.
Duk da cewa mutanen ƙasar na matuƙar sha'awar kallon manyan wasannin gasar Firimiya ta Ingila, kuma yara kan sanya rigunan taurarin ƙwallon ƙafa irin su Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, duk wani yunƙuri na taka ƙwallon ƙafa da muhimmanci a Nauru sau da yawa kan fuskanci zolaya da izgili.

Asalin hoton, Nauru Football Federation
Nauru ta yi ta yunƙurin samar da tawagar kwallon ƙafa a baya, har yanzu wasan bai samu karɓuwa a ba a ƙasar.
Wani yunƙuri na kusa da suka yi na kusa shi ne wasan da aka yi da Nauru da tsuburin Solomon da 'yan ƙasar waje ne ke zaune a wajen a 1994 da kuma tawagar 'yan gudun hijira 2014.
Mummunan tarihin Nauru na baya ya yi bayanin halin da ya sa ƙasar ta kasa samun hanyar fara wasan da ya fi kowanne ɗaukaka a duniya, ta gaza samun 'yan wasa da kuma magoya baya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Nauru na kusa da tekun Pacific, kimanin kilomita 2,500 daga arewa maso gabashin Australia. Tarihin tarin duniyar da yankin ke da shi ya samo asali ne saboda tarin sinadarin samar da takin zamani, wanda ya taru saboda yawan kashin da tsuntsaye suke yi a yankin.
Yankin Nauru wanda a baya yake mallakin Australia kafin samun samun 'yancin kai a 1968, yana cike da sinadarin Phosphate da ake takin zamani da shi a ƙarshen shekarun ƙarni na 20. Lokacin da sinadarin ya ƙare, sai yankin ya zama tamkar kufai da yake narkar da abubuwa. A baya an san ƙasar da kirarin "Tsuburin farin ciki" amma a yau wani ɓangare mai yawa a tsakiyar ƙasar ba zai zaunu ba a wurin mutane kuma ba za a iya noma a wurin ba.
Dalilin haka ya sa mafi yawan al'ummar ƙasar da ba su fi 12,000 suka mayar da hankali wajen zama a bakin teku. Inda za a iya mora a ƙasar ba shi da yawa, saboda wurin ba zai fi girman murabba'i 21 ba, kuma ƙasar kullum raguwa take, saboda matsala sauyin yanayi da yadda gaɓar ruwa ke ƙara faɗaɗa tana cinye ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Lalacewar asar noman Nauru ya tilasta mata shigo da kusan kashi 90 na abincin da ake ci, kuma mafi yawan abincin da ake shiga da shi abincin gwangwani ne da kawai sai dai a ci. Wannan ya sa kashi 69 na mutanen ƙasar suke da ƙiba, yayin da kashi 40 cikin 100 ke da ciwon siga mataki na biyu.
Daya daga cikin hanyoyin da Nauru ke samun kuɗin shiga a yau shi ne wata cibiya da Australia ke amfani da ita wajen tsare 'yan cirani, wadda ƙasar ke kula da iya na tsawon shekaru.
Rayuwar yau da gobe a yankin tana da wuya, yayin da shib kuma wasanni na hutu ne da nishadi da motsa jiki. Babban wasan da ya fi zama ruwan dare a Australia shi ne Rules Football, wanda kusan kashi 30 na mutanen ƙasar ke yi. Wasannin tsalle-tsalle da na ɗaga ƙarfe da gina jiki na daga cikin abubuwan da suka shahara a wajen motsa jiki.
A 2028 Nauru na son ƙarɓar wasannin Micronesia, wani tarin wasanni da ya haɗa da na kwallon ƙafa. Wannan wata alama ce da ke nuna Nauru na son tsoma kanta cikin harkokin wasanni a duniya.

Asalin hoton, PAUL WATSON
Yunƙurin da aka yi a baya na kawo kwallon ƙafa Nauru ya samu koma baya ne dalilin wasa ɗaya tal da aka ba da. An sake wani irinsa shekara biyu baya, lokacin da wani tsohon dan wasan Premier Dave Kitson ya jagoranci tawagar Nauru mai mutane 18 suka yi atisaye na makonni biyu.
An tsara wasa ne da za su yi na sada zumunta da XLFC, domin bunƙasa rayuwar mazauna yankin da kuma tabbatar da lafiyarsu, sai dai wasan bai yiwu ba saboda dalilin kudi, dan haka wasan da aka so a yi na farko da Nauru haka aka ɗaga shi.
Amma yanzu yadda ake so a dauki kwallo a yankin ya sauya, hukumar kwallon ƙafa ta yankin ta ce za ta ɗauki shirin ya zama na dogon lokaci maimakon yin shi cikin gaggawa.












