Everton na son Delap, ƙila Salah ya tafi Turkiyya maimakon Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images
Dan gaban Liverpool Mohamed Salah, mai shekara 33, zai iya watsi da bukatar tafiya gasar Saudiyya a bazaran nan a maimakon haka dan Masar din kila ya tafi kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya. (A Spor)
Manchester United na son El Hadji Malick Diouf, na West Ham, inda matashin dan wasan na tawagar Senegal mai shekara 21, zai samar da gasa ga Luke Shaw, na Ingila mai shekara 30, a bangaren hagu na baya. (Guardian)
Everton na shirin sabunta bukatarta ta zawarcin dan gaban Chelsea Liam Delap, mai shekara 23, yayin da suke kuma neman wasu 'yan baya John Stones, mai shekara 31, wanda zai bar Manchester City a karshen kaka, da kuma Ben White, na Arsenal mai shekara 28.
Haka kuma suna son tsawaita aron dan wasan gaba na Ingila, Jack Grealish mai shekara 30 daga Manchester City. (i paper)
Chelsea ta yi amanna za ta iya samun har fam miliyan 60 a kan dan wasan gaba na Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, wanda ya yi tsawon kakar nan a matsayin aro a Bayern Munich. (Athletic)
Tottenham za ta sayar da mi tsaron ragarta Guglielmo Vicario, dan Italiya mai shekara 29, ga Inter Milan a bazaran nan, inda za ta iya maye gurbinsa da mai tsaron ragar Manchester City James Trafford, mai shekara 23, ko kuma golan Brighton da Netherlands Bart Verbruggen, mai shekara 23. (Teamtalk)
Juventus na son golan Liverpool da Brazil Alisson Becker, mai shekara 33 wanda shekara daya ta rage a kwantiraginsa a Anfield. (Mail)
Aston Villa na duba yuwuwar neman dan wasan tsakiya na Morocco da Girona Azzedine Ounahi, mai shekara 26. (Sportsboom)
Wata kungiyar Italiya wadda ba a bayyana sunanta ba ta gabatar da binciken farko a kan dan wasan gaba na gefe na Manchester United mai shekara 26, dan Ingila Jadon Sancho, wanda zai kasance ba wani kwantirgi a kansa a bazaran nan.
Nottingham Forest ta kusa cimma kudin da Fenerbahce ta sanya a kan dan wasanta na baya bangaren hagu, Archie Brown. (A Spor )













