Yadda Najeriya da Afirka ta Kudu za su fafata wasan neman gurbin zuwa gasar kofin duniya

Super Faalcons

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Super Falcons ta Najeriya za ta kara da Afirka ta Kudu a wasan neman gurbin shiga matakin gasar cin kofin duniya a birnin Casablanca na ƙasar Morocco.

Za a buga wasan ne da misalin ƙarfe 9 na dare agogon Najeriya, a filin wasa na Stade Moulay Rachid.

Najeriya ta rasa damar samun tikitin shiga gasar kai-tsaye bayan rashin nasara a wasan kwata-fainal, inda Kamaru ta doke ta ci 1 mai ban haushi.

A ɗaya ɓangaren kuma, Afirka ta Kudu kuma mai masaukin baƙi Morocco ce ta doke ta da ci 2-1.

A ƙa'idar gasar ta cin kofin Afirka ta mata, ƙasashe biyu da suka samu nasarar zuwa zagaye wasannin kusa da ƙarshe, su ne suka samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya na mata.

Sai kuma akwai wasannin cike gurbi, wanda ƙasashe da suka buga kwata-fainal za su buga, sai waɗanda suka yi nasara a Afirka su ƙara fafatawa da wasu ƙasashen wasu nahiyoyin kafin samun gurbi a babbar gasar ta duniya.

Najeriya da Afirka ta Kudu

Najeriya za ta shiga wannan wasan ne bayan rashin nasara a hannun Kamaru a kwata-fainal.

Super Falcons ce ta fi taka leda da kai hare-hare a wasan, amma mai tsaron ragar Kamaru ta hana ƙwallo shiga raga.

Najeriya ta kammala wasan da kai hari 19, ciki har da guda 9 da suka nufi raga, amma duk da haka ba ta samu nasarar zura ƙwallo ba.

Tawagar, wadda koci Justine Madugu ke horaswa ta shiga matakin zagaye na biyu ne da ƙarin gwiwa bayan da warware daga rashin nasarar 3-2 da Malawi a wasan farko, amma daga baya ta doke Zambia da Egypt.

Nasarar da ta samu wajen lallasa Masar da ci 6-2 ta j hankali, inda aka yi tunanin ƙasar wadda ta daɗe tana mamaye harkar ƙwallon ƙafar mata ta koma ganiya, amma sai Kamaru ta yi waje da ita.

Ita kuwa tawagar Banyana Banyana za ta shiga wasan ne da raɗaɗin dokewar da Morocco ta yi mata da ci 2-1.

Afirka ta Kudu ta matsa wa Morocco lamba sosai a kwata-fainal, amma Sakina Ouzraoui Diki da Hanane Ait El Haj suka zura ƙwallo a raga domin ba Morocco nasara a wasan.

Fitattun ƴanwasan da za su iya ba da mamaki

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rasheedat Ajibade za ta kasance mai muhimmanci musamman a tsakiyar fili da ƙirƙirar damar kai hari. Chiamaka Nnadozie za ta taka rawa wajen tsare ragar Najeriya, sannan ana tunanin Asisat Oshoala za ta taka rawar gani a gaba.

Akwai matasan ƴanwasa Najeriya irin su Deborah Abiodun da Jennifer Echegini da Rinsola Babajide da ake sa ran za su iya nuna bajinta a wasan.

Sai dai akwai aiki ja a wajen kocin tawagar, Justine Madugu, musamman wajen fitar da ƴanwasa 11 na farko da za su fara take wasa.

A wasan tawagar na kwata-fainal da Kamaru, an soki ƴar wasa Esther Okoronkwo da ɓarar da babbar damar da Najeriya ta samu, sannan an soki mai tsaron ragar tawagar, Chiamaka.

Sai dai waɗannan ƴanwasa ne da ake gani suna da muhimmanci, inda Chiamaka take riƙe da gwarzuwar mai tsaron raga a Afirka na CAF, sannan ake kallon Esther a matsayin wadda za ta iya lashe kambun gwarzuwar ƴaƙwallon Afirka a nan gaba duk da cewa a gasar bana ba ta nuna bajinta ba sosai.

Sauran waɗanda ake tunani a tawagar Najeriya sun haɗa da Demehin da Ohale a baya da Ucheibe da Payne Kanu a tsakiya da gaba.

Wannan ya sa kocin zai iya shiga tsaka mai wuya wajen fitar da ƴanwasan da za su fara masa wasa, da kuma uwa-uba wajen canjin ƴan wasa bayan wasa ya yi wasa komai ya yi zafi.

Ita kuma Afirka ta Kudu, zaratan ƴanwasanta da ake ganin za su taka rawa sosai sun haɗa da Thembi Kgatlana, wadda ake ganin za ta kasance babbar barazana saboda yana da gudu kuma ta iya jefa ƙwallo a raga.

Akwai kuma Refiloe Jane, wadda ta ƙwara wajen taka leda da juyawa a tsakiyar fili tare da taimakawa wajen tura ƙwallo gaba.

Sauran ƴanwasan Afirka ta Kudu da ake ganin suna da muhimmanci su ne: Motau da Jane da Motlhalo da Cesane da Kgatlana.