Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ma'aikatun Najeriya 5 da suka fi yawan ma'aikatan bogi - ICPC
Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana mamakin yadda binciken ICPC ya gano ma'aikatan bogi 908 a wasu ma'aikatun ƙasar.
Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ce ta bankaɗo badakalar ta shafi ma'aikatu da hukumomi daban daban.
ICPC ta ce ta ƙwace kusan naira miliyan 942 da ake zargi suna da alaƙa da badaƙalar biyan albashin ma'aikatan bogin.
Shugaban hukumar Barsita Musa Aliyu SAN, ya tabbatar wa BBC an gano ma'aikatan bogin ne bayan wani bincike da hukumarsa ta ƙaddamar a 2024.
Ya ce sun ƙaddamar da binciken ne bayan gano biyan kuɗin fansho na bogi a 2024.
Su wane ne ma'aikatan bogi?
Ma'aikatan bogi su ne mutanen da ake cusa sunayensu a matsayin ma'aikata, amma babu su a zahiri.
Akan riƙa biyan mutanen albashi da sunan aiki, saboda an riga an shigar da sunayensu a cikin rajistar biyan ma'aikata albashi, da Zarar lokacin biya ya yi kudin za su shiga asusunsu, amma kuma ba sa aiki.
A wasu lokutan wasu manyan jami'ai ne ke sanya sunayen mutanen, inda suke karkatar da albashin ma'aikatan zuwa aljihunsu.
Barista Musa Adamu ya ce daga cikin binciken nasu sun gano wani mutum da ya saka sunan matarsa da ɗansa da surukarsa, sannan shi kuma yana karɓar albahsin ma'aikata 12.
Waɗanne hukumomi ne kan gaba?
Shugaban hukumar ta ICPC ya ce daga binciken da suka yi sun gano ma'aikatu da hukumomin gwamnati aƙalla 50 da suka samu da wannan badaƙala, sai dai ya lissafo wasu biyar da ya ce matsalar ta fi ƙamari a cikinsu.
Ma'aikatar tsaron Najeriya ce ta biyar cikin jerin ma'aikatun da aka gano ma'aikatan bogi masu yawa a cikinta.
''A ma'aikatar tsaro mun gano mutum 19 da ke zama a matsayin ma'aikatan bogi'', in ji shi.
Ma'aikatar ce ke da alhakin kula da rundunonin sojin ƙasar.
Sauran ma'aikatun sun haɗa da:
- Lantarki mutum 17
- Cikini da zuba jari mutum 17
- Lafiya mutum 15
- Ofishin shugaban ɗaukar ma'aikata mutum 12
- Ofishin babban akanta na ƙasa
- Ma'aikatar cikin gida
Shugaban hukumar ta ICPC ya ce rundunar ƴansandan ƙasar ce kan kana a jerin inda ICPC ta gano ma'aikatan bogi da yawa.
''A cikin wannan rundunar mun gano mutum 570 da muke zargin c ewa mutanen ne nab ogo da aka saka suna karɓar albashi alhalin bas a aiki'', in ji shi.
Hukumar ƴansandan na daga cikin ma'aikatun ƙasar da ake yawan ɗaukar ma'aikata.
Hukuma ta gaba da binciken ICPC ya gano ma'aikatan bogi da yawa it ace hukumar samar da albarkatun ruwa ta ƙasar.
''A wannan hukuma mun gano sunayen mutum 80 da ke karɓar albashi, alhali sub a ma'aikatan hukumar ba ne'', in ji Barista Adamu.
Hukumar albartakun ruwa ta ƙasa ce ke da alhakin samar da ruwan sha a ƙasar.
Ma'aikatar ayyuka ta ƙasa na daga cikin hukumomin gwamnatin da binciken ICPC ya gano ma'aikatan bogi.
"Mun gano sunayen ma'aikatan bogi su 56'', in shi Barista Musa Adamu.
Ma'aikatar c eke jagorantar shiryawa da gina da kuma kula da manyan tituna a faɗin ƙasar ƙasar da gina.
Ma'aikatar da ta zo a matsayi na huɗu da aka fi samun ma'aikatan bogi it ace ma'iakatar harkokin ƙasashen waje.
''A wannan ma'aikata mun gano 24 da ke zama a matsayin ma'aikatan bogi'', in ji shugaban na ICPC.
Ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen ce ke lura da alaƙa tsakanin Najeriya da ƙasashen waje.