Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sauye-sauye 6 da aka samu tun bayan zaɓen Tinubu a 2023
- Marubuci, Uche Akolisa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 10
Ƴan Najeriya na shirin sake komawa rumfunan zaɓe a watan Janairun 2027, inda miliyoyin masu kaɗa ƙuri'a za su zaɓi shugaban ƙasa, gwamnoni, da kuma ƴan majalisun tarayya da na jihohi.
A zaɓen 2023, mutane da dama sun sa ran cewa amfani da sabbin fasahohi a zaɓe, yawan fitowar matasa kaɗa ƙuri'a da kuma zazzafar takara tsakanin manyan ƴan takara uku za su ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya.
Sai dai matsalolin da aka samu daga hukumar zaɓe ta INEC na rashin nuna sakamakon zaɓe ta intanet (IReV) sun haifar da shakku kan sahihancin zaɓen a idanun mutane da dama.
An ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar. Sai dai manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, sun ƙalubalanci sakamakon a kotu, amma Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Tinubu.
Bayan shafe shekaru uku, an ga sauye-sauye dama a fagen siyasa da tattalin arziki Najeriyar. An samu sauye-sauyen dokokin zaɓe, jam'iyyar APC ta ƙara faɗaɗa tasirinta a siyasance, yayin da ƴan ƙasar ke ci gaba da ƙorafi kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da matsalar wutar lantarki.
Ga wasu manyan sauye-sauye guda shida da suka faru tun bayan zaɓen shugaban ƙasar na 2023.
Sauya dokokin zaɓe
Zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya sha suka daga sassa daban-daban na ƙasar bayan da Hukumar Zaɓe Ƙasar ta INEC ta kasa ɗora sakamakon rumfunan zaɓe kai tsaye a shafinta na IReV (IReV) kamar yadda aka yi tsammanin shafin zai inganta gaskiya da adalci.
Kafin wannan zaɓen dai an yi amfani da tsarin yadda ya kamata a wasu zaɓukan gwamnoni da na cike gurbi da aka gudanar a shekarar 2022. Sai dai a zaɓen shugaban ƙasa, matsalolin da INEC ta danganta da tangarɗar na'ura sun sa mutane da dama suka fara nuna shakku kan sahihancin zaɓen.
A ƙoƙarin magance irin wannan matsala, sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanadi cewa dole ne duk jami'in da ke jagorantar zaɓe a kowace rumfar zaɓe ya ɗora sakamakon rumfar zuwa IReV bayan ya cike takardar sakamakon EC8A, kamar yadda sashe na 60(3) na dokar ya tanada.
Sai dai dokar ta kuma ba da damar ci gaba da amfani da tsarin tattara sakamako yadda aka saba ba tare da na'ura ba idan aka samu matsalar sadarwa ko tangarɗar na'ura. Har yanzu wannan sashe na ci gaba da jawo muhawara gabanin zaɓen 2027.
Darakta a cibiyar nazarin siyasa da zamantakewa ta Abuja School of Social and Political Thought, Sam Amadi, ya ce wannan sashen na iya rage yardar da jama'a k da ita kan gyaran da aka yi.
"Damar da aka bayar ta amfani da tsarin tura sakamako ba tare da na'ura ba idan akwai matsalar sadarwa na iya haifar da ruɗani, domin wasu jami'an INEC na iya amfani da hakan a matsayin hujjar ƙin ɗora sakamakon rumfunan zaɓen," in ji shi.
Sai dai INEC ta ce ɗora sakamako ta hanyar na'ura ba ya maye gurbin tsarin tattara sakamako da aka saba ba ne, illa dai yana ƙara masa sahihancin zaɓen ne.
Kwamishinan zaɓe na jihar Edo, Obo Effanga, ya ce "har yanzu ana ƙirga ƙuri'u da hannu, ana rubuta sakamakon a takardar sakamako, muna amfani da na'urar BVAS wajen hoton takardar domin a ɗora shi a IReV."
Ya ƙara da cewa ko da babu sadarwa, jami'an zaɓe za su yi ƙoƙarin ɗora sakamakon, amma hakan ba zai hana a ci gaba da tattara sakamakon ta hanyar da aka saba ba. "Ko da babu sadarwa, za a yi ƙoƙarin ɗora sakamakon a shafin, amma za a ci gaba da tattara sakamakon kamar yadda aka saba," in ji shi.
Masu goyon bayan dokar na ganin za ta ƙara inganta gaskiya da bayyana sakamakon zaɓe sahihi, yayin da masu suka ke cewa damar da aka bayar na amfani da tsohon tsarin na iya ci gaba da haifar da rashin tabbas.
Dokar ta kuma tanadi wasu sauye-sauye, ciki har da tsarin ƙato bayan ƙato wajen zaɓen fidda gwani a jam'iyyu, miƙa rajistar mambobi ta intanet, damar sauke katin zaɓe ta yanar gizo, da kuma amincewa da sabbin jam'iyyun siyasa biyu, ciki har da NDC da Peter Obi ke takara a cikint, lamarin da ya sa yawan jam'iyyun siyasar Najeriya suka zama 20.
Za a ga tasirin waɗannan sauye-sauyen ne a lokacin da ƴan Najeriya za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen 2027.
Jam'iyya mai mulki ta ƙara faɗaɗa tasirinta
An samu gagarumin sauyi a taswirar siyasar Najeriya tun bayan zaɓen 2023.
Zaɓen shugaban ƙasar ya kasance ɗaya daga cikin zaɓukan da suka fi ɗaukar hankali tun bayan komawa mulkin dimokuraɗiyya a 1999. Jam'iyyar APC mai mulki ta fuskanci ƙalubale mai zafi daga PDP da kuma LP, inda ɗan takarar LP, Peter Obi, ya samu gagarumar goyon baya musamman daga matasa da waɗanda suka kaɗa ƙuri'a a karo na farko.
Sai dai gabanin zaɓen 2027, lamuran siyasa da dama sun sauya. Bayan sauya sheƙar gwamnoni da dama zuwa APC, jam'iyyar yanzu tana da goyon bayan gwamnoni 30 daga cikin jihohi 36 na Najeriya. Wannan ya sa ana ta muhawara kan ko Najeriya na shirin komawa tsarin jam'iyya ɗaya.
Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da irin haka ke faruwa ba. A shekarar 2007, jam'iyyar PDP da ke mulki a lokacin tana riƙe da iko a jihohi 28 cikin 36 na ƙasar.
Masu sharhi na ganin cewa tattare ikon siyasa a jam'iyya ɗaya na iya raunana tsarin dimokuraɗiyya.
Amma masu goyon bayan hakan suna cewa sau da yawa gwamnoni kan koma jam'iyyar da ke mulki a matakin tarayya ne domin samun kyakkyawar alaƙa da gwamnatin tarayya da kuma sauƙaƙa samun ayyuka da tallafin gwamnatin tarayya ga jihohinsu.
Rashin tsaro na ci gaba da zama babban ƙalubale
Rashin tsaro na daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023, kuma har yanzu yana ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da za su yi tasiri a zaɓen 2027.
A lokacin rantsar da Shugaba Bola Tinubu a ranar 29 ga Mayun 2023, ya yi alƙawarin bai wa fannin tsaro fifiko, inda ya ce "ba za a iya samun ci gaba ko adalci ba a cikin yanayin rashin tsaro da tashe-tashen hankula." Ya kuma yi alƙawarin "sake fasalin tsaron" Najeriya.
Tun daga lokacin, gwamnatin ta ce ta ɗauki ƙarin jami'an ƴansanda 20,000 aiki, ta ƙara kuɗaɗen da ake ware wa tsaro tare da sauya shugabannin hukumomin tsaro.
Sai dai duk da waɗannan matakai, ana ci gaba da satar mutane domin neman kuɗin fansa, ƴan bindiga da sauran laifuka. Haka kuma, hare-haren sun fara yaɗuwa zuwa wasu yankunan da a baya ba su cika fuskantar irin waɗannan matsaloli ba, musamman wasu sassan Kudu maso Yamma.
Misali, a jihar Oyo, jami'an tsaro sun ceto mutum 45, ciki har da ɗalibai da malamansu, bayan sun shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane.
Daya daga cikin manyan hare-haren da suka fi ɗaukar hankali a lokacin mulkin Tinubu shi ne sace fiye da yara 300 daga makarantar St Mary's Private Catholic School da ke jihar Neja.
Ƙungiyar ACLED ta ce, tsakanin shekarar 2015 da 2023 an samu hare-hare 10 kan makarantu a Najeriya, inda aka yi garkuwa da kimanin ɗalibai da malamai 1,127.
A cikin shekaru ukun farko na gwamnatin Tinubu, an samu manyan hare-haren garkuwa da mutane guda tara da suka shafi fiye da mutum 500. Masana na cewa abin damuwa shi ne yadda hare-haren suka fara yaɗuwa zuwa yankunan da a baya ake ɗauka suna da ɗan kwanciyar hankali.
Hare-haren da ake kai wa kan manoma sun rage yawan noman da ake yi tare da ƙara matsalar ƙarancin abinci. Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ta yi hasashen cewa mutum miliyan 35 a Najeriya na iya fuskantar matsalar ƙarancin abinci a shekarar 2026, idan aka kwatanta da miliyan 24.8 a shekarar 2023.
Yayin da 'yan Najeriya ke shirin sake kaɗa ƙuri'a a 2027, ana sa ran batun tsaro zai kasance ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da masu zaɓe za su yi amfani da su wajen auna nasarorin gwamnati mai ci da kuma alƙawuran masu neman maye gurbinta.
Tsadar rayuwa ta ƙaru a Najeriya
Babban daraktan ƙungiyar Yiaga Africa, Samson Itodo, ya ce "duk ɗan Najeriyar da ya damu da ingancin rayuwarsa... ya kamata ya damu da wanda zai lashe zaɓen 2027 domin shugabannin da za su zo ne za su yanke shawarar tattalin arzikin da za su shafi makomar ƴan ƙasa."
A lokacin rantsar da shi a 2023, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, inda ya ce kasafin kuɗin da ya gada bai tanadi kuɗin ci gaba da biyan tallafin ba.
Tun daga lokacin, janye tallafin fetur da kuma wasu tsare-tsaren tattalin arziki da sakin farashin naira da dala sun sauya yanayin tattalin arzikin ƙasar, inda farashin sufuri, kayan abinci da sauran buƙatun yau da kullum suka yi tashin gwauron zabo.
Bayanan Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa hauhawar farashi ta kai kashi 24.7 a 2023, kuma ta kai kashi 37.57 a watan Agustan 2024. Daga baya ta sauko zuwa kashi 17.18 a watan Janairun 2026, sai dai har yanzu ƴan Najeriya da dama na ci gaba da fama da tsadar rayuwa.
Masanin tattalin arziki, Boniface Chizea, ya ce ƙalubalen tattalin arzikin Najeriya ya ƙara tsananta tun bayan zaɓen da ya gabata.
"Najeriya na da duk abin da take buƙata domin ci gaba, amma cin hanci da rashawa, ƙarin talauci da matsalolin tsaro suna hana ta cimma hakan. Duk da raguwar hauhawar farashi, abubuwa ba su kai haka muni ba a 2023 kamar yadda suke yanzu."
Ga ƴan Najeriya da dama, babban abin da za su yi la'akari da shi a zaɓen 2027 ba wai kawai manufofin siyasa ba ne, illa ganin ko rayuwa ta fi sauƙi da araha fiye da yadda take shekaru huɗu da suka gabata.
Rashin wutar lantarki na ci gaba da addabar an Najeriya
Samar da isasshiyar wutar lantarki na daga cikin manyan alƙawuran da ƴan Najeriya za su auna wannan gwamnati, kuma har yanzu yana cikin manyan batutuwan da za su yi tasiri a zaɓen 2027.
A lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, Bola Tinubu ya yi alƙawarin cewa: "Idan ban samar muku da ingantacciyar wutar lantarki ba, sannan na dawo neman wa'adi na biyu, kada ku zaɓe ni, sai dai idan na ba ku gamsassun dalilan da suka hana ni cika alƙawarin."
Tun bayan hawan Tinubu mulki, gwamnatinsa ta aiwatar da wasu daga cikin manyan sauye-sauye a fannin wutar lantarki.
Sabuwar Dokar Wutar Lantarki da kuma gyaran kundin tsarin mulki sun bai wa jihohi damar kafa tashoshin samar da wutar lantarki na kansu, ba tare da dogaro da babban layin wutar lantarki na ƙasa ba.
Gwamnatin ta kuma amince da shirin kashe dala biliyan 2.4 domin magance basussukan da suka daɗe suna addabar ɓangaren wutar lantarki, da nufin inganta harkokin kamfanonin lantarki da ƙara ingancin samar da wuta.
Sai dai duk da waɗannan sauye-sauye, ƴan Najeriya da dama na ci gaba da kokawa kan rashin wutar lantarki, yayin da kuma farashin lantarkin ya ƙaru.
Bayanan Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) sun nuna cewa ƙasar ta samar da fiye da megawatt 4,922 na wuta a shekarar 2023. Zuwa watan Janairun 2026 kuwa, matsakaicin wutar da ake iya aikawa bai wuce megawatt 4,901, duk da cewa ƙarfin da aka girka ya kai megawatt 13,625.
Gidaje da kasuwanci da dama na ci gaba da dogaro da janareto da sauran hanyoyin samar da wuta, batun lantarki na ci gaba da zama ɗaya daga cikin muhimman ma'aunin da masu zaɓe za su yi amfani da su wajen tantance ayyukan gwamnati a zaɓen 2027.
Yawan matasa masu kaɗa ƙuri'a
Matasa sun taka muhimmiyar rawa a siyasa da zaɓen 2023, kuma ana sa ran za su sake yin muhimmin tasiri a zaɓen 2027.
INEC) ta ce mutane masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 su ke da kashi 76 na sabbin masu rajistar zaɓe a 2023. Sai dai duk da haka, kashi 30.56 ne kawai daga cikinsu suka fito suka kaɗa ƙuri'a.
Tun daga wancan lokaci, ana ci gaba da samun ƙarin matasa masu rajistar zaɓe. A yayin ci gaba da rajistar masu zaɓe ta 2026, INEC ta ƙara samun sabbin masu rajista miliyan 2.78, wanda ya ƙara yawan masu rajista daga miliyan 93.47 a zaɓen 2023 zuwa miliyan 96.25 a watan Janairun 2026.
Daga cikin waɗannan sabbin masu rajistar, kusan kashi 69 cikin 100 matasa ne.
Sai dai masana na cewa yawan rajistar masu zaɓe ba shi ke nufin yawan fitowar masu zaɓe ba.
Saboda haka, ana sa ran yadda matasa suka fito zaɓe a 2027 na iya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su iya yin tasiri kan sakamakon zaɓen.
Tasirin zaɓen Najeriya na 2027
Zaɓen Najeriya na 2027 ba iya asar kawai yake aukar hankali ba. A matsayinta na ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka kuma ɗaya daga cikin manyan masu tattalin arziƙi a nahiyar, duk wani rikici ko rashin kwanciyar hankali a Najeriya na iya yin tasiri ga kasuwanci, ci-rani, tsaron yankin da kuma zuba jari a faɗin Yammacin Afirka da ma duniya baki ɗaya.
Masanin tattalin arziƙi, Boniface Chizea, ya ce girman Najeriya da matsayinta a nahiyar na nufin cewa duk wata matsala ta siyasa ko tattalin arziƙi ba za ta tsaya a cikin ƙasar kaɗai ba.
"Najeriya ƙasa ce mai matuƙar muhimmanci. Muna da al'umma sama da miliyan 200, kuma ba kowace kasashe ba ce a duniya da ke da irin wannan yawan jama'a ko faɗin ƙasa. Idan aka samu rikicin siyasa, hauhawar farashi ko kuma mutane suka fara tserewa daga Najeriya a matsayin ƴan gudun hijira, hakan zai girgiza yankin Yammacin Afirka, har ma ya yi tasiri a sauran sassan duniya, kamar yadda ake gani a rikicin Iran," in ji shi.
Sai dai ga ƴan Najeriya da dama, abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda rayuwarsu ta sauya cikin shekaru huɗu da suka gabata. Bayan sauye-sauyen da aka samu na siyasa da tattalin arziƙ tun bayan zaɓen 2023, al'umma za su sake yin zaɓe a 2027 tare da tambaya guda:
Shin rayuwarsu ta fi inganta a yanzu fiye da lokacin da suka kaɗa ƙuri'a a 2023?