Me ya shiga tsakanin Sanata Hanga da Kwankwanso?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wata sabuwar dambarwar siyasa ta kunno kai a jihar Kano tsakanin Sanata Rufa'i Sani Hanga da Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sanata na daga cikin 'yan majalisar dokokin Najeriya daga jigar Kano da suka ci gaba da kasancewa tare da Kwankwaso tun bayan ficewar Gwamna Abba Kabir daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.

A farkon shekarar nan ne Kwankwaso da mutanensa ciki har da Sanata Hanga suka fice daga NNPP zuwa ADC, daga baya kuma suka koma NDC.

A baya-bayan nan an ga Sanata Hanga na ganawa da wasu jiga-jigan APC, ciki har da shugabanta na kasa da Gwamna Abba, a wani mataki da masu sharhin siyasa ke ganin kamar zai bar tafiyar Kwankwasiyya.

A shekarar 2023 ne aka zabi Sanata Rufai Sani Hanga a matsayin ɗanmajalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kano ta Tsakiya a jam'iyyar NNPP kwankwasiyya.

Sai dai da alama dangantaka ta fara tsami tsakanin Sanata Hanga da jagoran Kwankwasiyya tun bayan fitar da ƴantakarar jam'iyyar NDC.

Me ya janyo tsamin dangantakar?

Dr Kabiru Sa'id Sufi Malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai shairhi kan al'amuran siyasar Najeriya ya ce batun takara ne ya shiga tsakanin ƴansiyasar biyu.

''Rashin ba shi wata dama ta takara ko bai wa yaransa na siyasa a zaɓen 2027 da ke tafe ne ya assasa rikicin nasu'', in ji shi.

Dr Nasiru Yusuf Gawuna ne dai aka bai wa takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam'iyyar NDC, yayin da aka bai wa Comr. Aminu Abdussalam a matsayin ɗantakarar gwamna, Mustapha Kwankwaso a matsayin ɗantakarar mataimaki.

Dr Sufi ya ce matakin bai yi wa Sanata Hanga daɗi ba, kasancewar shi ne mutum mai riƙe da babban muƙami a tafiyar NDC a jihar Kano.

Masanin siyasar ya ce wannan al'amari ya ɓata wa Sanata Hanga da magoya bayansa.

Me Sanata Hanga ya ce?

Cikin wata hira da tashar Youtube ta Dau'uwa Rano TV, Sanata Hanga ya zargi Kwankwaso da hana shi takara a sabuwar jam'iyyar NDC, da gangan domin a binne shi a siyasance.

Ya kuma zargi jagoran kwankwasiyyar da kitsa tsayar da ɗansa takarar mataimakin gwamnan jihar Kano.

''Da fari an ce za a bani takarar mataimakin gwamnan, amma daga baya sai abubuwa suka sauya'', in ji shi.

''Ina gida aka turo min wasu wakilai cewa an yanke shawarar bai wa Mustapha takarar mataimakin gwamnan Kano'', in ji shi

Ya kuma yi iƙirarin cewa duk da cewa ya ci zaɓe a tafiyar Kwankwasiyya, amma ba kwankwasiyyar ce ta sa ya ci zaɓe ba.

''Ai ba wannan ne karon farko da na taɓa cin zaɓe ba, a baya na yi ɗanmajalisar tarayyya da sanata kuma babu ma Kwakwasiyyar'', in ji shi.

Mene ne martanin Kwankwaso?

Jagoran Kwankwasiyyar ya ce ba shi da matsala da Sanata Hanga.

Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta DITV Kaduna, Sanata Kwankwaso ya ce tsayar da ƴantakarar ba abu ne mai sauƙi ba a siyasance saboda lissafin da ake yi a ciki.

Ya ci gaba da cewa babban abin da ya dama masa lissafi shi ne komawar Dr Nasiru Yusuf Gawuna jam'iyyarsa.

''Tun bayan dawowar Gawuna nake ta lissafi kan yadda za mu yi, amma da fari abin da na bari a zuciyata shi ne za mu haɗa Gawuna da Comrade Aminu Abdussalam''.

Sai dai ya ce bayan nazari ya gano cewa Gawuna ya yi mataimakin gwamna kusan sau biyu.

''Don haka ne muka yi tunanin ba shi kujerar Sanata, domin kada a yi masa dariyar cewa ya dawo tafiyarmu ba mu ba shi komai ba'', in ji shi.

Kwankwaso ya ce abin da ya so tun farko shi ne Sanata Hanga ya yi mataimakin gwamna.

Amma daga baya sai wasu suka ba shi shawarar kada a yi wa Sanata Hanga mataimakin gwaman saboda shekarunsa.

''Mun yi nazarin yawan shekarun Aminu Abdussalam da Sanata Hanga game da haa su takarar tare'', in ji shi.

Ya ce daga baya sun yanke shawarar cewa idan Sanata Hanga ya dawo daga neman lafiya za su zauna a duba abin da ya kamata a yi masa.

''Amma da ya dawo maimakon ya zo mu zauna sai ya riƙa maganganu, har maganganu suka yi yawa'', in ji shi.

Kwankwaso ya kuma musanta hannu a bai wa ɗansa Mustapha Kwankwaso takarar mataimakin gwamnan Kano.

''Shugabannin jam'iyya ne na ƙasa da sauran jagororin tafiyarmu suka bai wa Mustapha takarar amma ba ni ba'', in ji shi.

Ya ce da farko ma jagororin jam'iyyar sun so a bai wa Mustapha takarar gwamna, ''amma na hana su, daga baya suka sake dawowa kan batun mataimakin gwamna'', in ji shi.

Ko rashin takarar Hanga illa ce ga Kwankwasiyya?

Dr Sufi ya ce ko shakka rashin Hanga ga tafiyar Kwankwasiyya ba ƙaramar illar zai yi wa tafiyar ba.

''Idan ka duba a yanzu yadda ake shi ne mutum mafi girman muƙami a tafiyar Kwankwasiyya, kuma yana da ɗimbin magoya baya don haka rashinsa a tafiyar zai iya shafar tafiyar'', in ji shi.

Masanin siyasar ya ce daga kalaman ake ake ji daga bakunan magoya bayansa a baya-bayan nan za a iya fahimtar irin tasirinsa a siyasance.

''A duk lokacin da aka tunkari kakar zaɓe akwai wasu rukunin mutane da bai kamata a rabu da su saboda tasirinsu wajen magoya baya da masu kaɗa ƙuri'a, kuma dai yadda ake yanzu a NDC a Kano ba za ka cire Hanga ba'', in ji shi.

Me ya kamata Kwankwaso ya yi?

Dr Sufi ya ce abin da ya kamata Engr. Dr Rabi'u Kwankwaso ya yi shi ne ya haƙurƙurtar da Sanata Hanga.

''Duk da cewa wasu jiga-jigan Kwankwasiyyar sun je sun same shi har gida sun zauna da shi, hakan bai wadatar ba, ya kamata shi ma da kansa Kwankwaso ya zauna da Hanga ya kuma rarrashe shi'', in ji shi.

Masanin siyasar ya kuma ce ya kamata Kwankwaso ya yi hakan tun kafin wasu jam'iyyun su ɗauke Sanata Hanga.

''Idan har shugaban APC na ƙasa zai je wajensa su gana, sannan gwamnan Kano ya gana da shi, to lallai ya kamata Kwankwaso ya zauna da shi domin haƙurƙurtar da shi'', in ji shi.