Ƴanwasan Premier League da ba su yi ƙoƙari ba a 2025/26

Asalin hoton, Getty Images
A kakar Premier League ta 2025/26, an shaida labarai masu jan hankali da dama. Wasu ƙungiyoyi da ƴan wasa suna taka rawar gani da take burge magoya baya, wasu kuwa suna jin dadi da rawar da suke takawa. Amma akwai wasu da suka kasa taka rawar gani ko komawa kan ganiya a kakar nan.
Sabbin ƴan wasa da aka saya su ne suka fi fuskantar matsin lamba. Yawancinsu sun je sabbin ƙungiyoyinsu cikin farin jini da fatan za su daga darajar ƙungiyoyinsu. Sai dai bayan watanni ana buga gasar bana, wasu daga cikin waɗannan fata da aka yi ya koma takaici da tambayar ko da gaske an bukaci sayensu, ko ya dace da aka sayo su.
A lokacin kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo kan fara kakar nan, an kulla cinikin sayen manyan ƴan wasa har guda 155 a gasar Premier League, sannan aka kara wasu sababbin ƴan ƙwallon a watan Janairu. Yanzu mafi yawan ƴan wasan sun yi watanni suna taka leda, ana iya tantance waɗanda suka yi tasiri da kuma wadanda suka gaza.
Ga jerin wasu ƴan wasa da ake ganin ba su taka rawar gani ba a Premier League a bana, bayan da aka sa babban burin za su yi bajinta tun farko.
Alexander Isak

Asalin hoton, Getty Images
Kowa ya yi tsammanin Alexander Isak zai bajinta sosai bayan rawar da ya taka a Newcastle United, wadda ta buɗe hanyar komawarsa Liverpool kan kuɗi mafi tsada a tarihin Birtaniya a fannin taka leda a ranar ƙarshe ta rufe kasuwar saye da sayar da ƴan wasa. Duk da cewa ya zura ƙwallaye uku cikin wasa 20 a ƙungiyar Anfield a bana, ya sha fama da jinya da kuma kasa yin tasiri a wasanni da yawa.
Ɗan wasan tawagar Sweden ya sake fuskantar babban cikas bayan da ya samu rauni a idon sawu da kuma karaya, bayan ya ci Tottenham ƙwallo a watan Disambar 2025.
Wannan ya zo ne masa a matakin mafi muni, domin ƙwallon da ya zura a raga a lokacin ta zama ta farko da ya ci a Anfield. Sai dai magoya bayan Liverpool ba su kara ganin ɗan wasan ba har sai cikin watan Afirilu a karawa da Fulham, bayan da bai yi karawa 14 ba a Premier League.
Yoane Wissa Newcastle United
Yoane Wissa ya zama ɗaya daga cikin ƴan wasan da aka yi zawarci sosai tun kan fara kakar bana, saboda ƙwallo 19 da ya zura a raga cikin wasa 25 da ya buga wa Brentford a Premier League a kakar da ta gabata. Amma sai ya ji raunin da ya yi dogon jinya da zuwansa, sabuwar ƙungiyarsa Newcastle United, kuma da ya warke bai koma kan ganiya ba.
A wasanni 14 da ya buga wa Newcastle ya ci ƙwallo ɗaya kacal ba tare da ya bayar ba an zura a raga daga karawar. Har ma ya rasa gurbin ƴan wasa 11 da ake fara wasa da su a ƙungiyar, inda aka fi amfani da William Osula madadinsa. Ana ganin kuɗin da aka sayi mai shekara 29 kan fam miliyan 55 da aka kashe a kansa, da an yi amfani da su ta hanya mafi kyau.
Liam Delap Chelsea
Chelsea ta saba kashe kuɗi masu yawa wajen sayen ƴan wasa a wuraren da ba lallai suke bukatar ƙarin yan ƙwallon ba. A game da Liam Delap, har da rashin sa'a, saboda raunin da ya ji da ta kai ya yi doguwar jinya. Duk da haka bai taka rawar gani ba, koda lokacin da yake da laifiya bai ji raunin ba.
Ko da yake yana taka rawar gani a gurbin kai hare-hare a Chelsea fiye da kokarin, Joao Pedro, amma bai koma kan ganiya ba. A wasa 25, ya ci ƙwallo ɗaya kawai tare da bayar da ɗaya aka zura a raga. Ganin cewa an saya shi ne saboda rawar da ya taka a kakarsa ta farko a Ipswich Town, inda ya ci ƙwallaye 12 cikin wasa 37, har yanzu cinikin bai nuna alamar da an ci riba ba.
Anthony Elanga Newcastle United

Asalin hoton, Getty Images
Anthony Elanga ya zama ɗaya daga cikin mafi haɗarin ƴan wasan gefe a Premier League ƙarƙashin Nuno Espirito Santo a Nottingham Forest. Ya ci ƙwallaye shida tare da bayar da 11 aka zura a raga.
Sai dai rayuwarsa a St James Park bai fara ba da kafar dama. Duk da wasa 29 da ya buga, bai ci ko ƙwallo ɗaya ba a Premier League, kuma daya ya bayar aka zura a raga. Saboda haka ba abin mamaki ba ne yadda aka kwatanta wasanninsa da "marasa armashi." Bisa kuɗin da aka kashe a kansa, dole ne ya nuna wa Eddie Howe abin da ya fi haka idan yana son samun matsayin da za ake fara wasanni da shi a ƙungiyar.
Jamie Gittens Chelsea
Ba boyayyen abu ba ne cewa Chelsea na bukatar ɗan wasan gefe daga hagu ɓangaren gaba, bayan da Jadon Sancho ya kasa yin tasiri a wasannin aro, kuma aka dakatar da Mykhailo Mudryk saboda gwajin sinadarin da aka haramta da aka same shi ya sha. Saboda haka suka koma kan Jamie Gittens ya ke buga wasanni.
An sayo shi daga Borussia Dortmund a yarjejeniyar da za ta iya kaiwa fam miliyan 52, amma matashin ɗan wasan Ingila ya nuna cewa har yanzu bai gama gogewa ba. Bai ci ƙwallo ko ɗaya ba a wasa 16 a kakar farko a Premier League, kuma ya bayar da ƙwallo biyu aka zura a raga. Don haka dole ne ya inganta wasanninta idan yana son tabbatar da kuɗin da aka kashe a kansa ya dace.
Harvey Elliott Liverpool
Harvey Elliott ya koma Aston Villa daga Liverpool a matsayin buga wasannin aro domin samun damar buga wasa akai-akai. An yi tsammanin cewa zai zama muhimmin ɗan wasa ƙarƙashin Unai Emery a Villa Park, bayan namijin kokarin da Villa ta yi a kakar 2024/25.
Sai dai hakan bai faru ba. Elliott ya buga wasa biyar kacal a lig a Villa Park, kuma Emery ya nuna cewa ƙungiyar ba za ta saye shi kai tsaye ba, yayin da yake ci gaba da ajiye shi a benci. Wannan yarjejeniyar ba ta amfani kowane ɓangare ba.
Alejandro Garnacho Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta yanke shawarar rabuwa da Alejandro Garnacho bayan saɓaninsa da tsohon koci, Ruben Amorim. Chelsea ta ɗauki kasada wajen sayen ɗan wasan mai shekara 21 kan fam miliyan 40 domin ya ƙarfafa gefen hagu daga gaba.
Ko da yake ya ci ƙwallo ɗaya tare da bayar da huɗu aka zura a raga a kakarsa ta farko a Stamford Bridge, magoya bayan Chelsea sun nuna rashin jin daɗi da abin da suka gani daga gare shi. Rahotanni ma sun bayyana cewa Chelsea na iya sayar da shi a karshen kakar bana.
Xavi Simons Tottenham

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta sayi Xavi Simons kan fam miliyan 51.8 a matsayin madadin Eberechi Eze wanda daga baya ya koma Arsenal. Zuwa ranar ƙarshe ta kasuwar ciniki, magoya bayan Tottenham sun yi farin ciki sosai da zuwansa.
Sai dai har yanzu bai nuna gogewarsa ba. Yana fama da matsin lamba idan yana da ƙwallo a hannunsa hankalinsa a tashe yake, kuma bai saba da sa jiki ba kamar yadda ake a wasan Ingila. Duk da cewa ƴan gaba na Tottenham ba sa taimaka masa sosai, rashin tasirinsa a manyan wasanni ya sa mutane suna tambayar ko zai iya yin nasara a ƙungiyar.
Florian Wirtz Liverpool
Babu wanda ya taɓa shakkar ƙwarewar Florian Wirtz. Ya yi fice sosai a Bayer Leverkusen, kuma ya zama ɗaya daga cikin mafi kayatarwa a wasannin tsakiyar fili. Amma kakar 2025/26 ba zo masa yadda ake so ba ga ɗan wasan Liverpool da aka saya kan fam miliyan 116.
Ɗan wasan mai shekarA 22 ya fara kakar bana da wasa a hankali, yayin da yake ƙoƙarin fahimtar tsarin koci, Arne Slot, har ta kai da wasu ciki har da Jamie Carragher suka nemi a cire shi daga ƴan wasa 11 da ake fara wasa da su. Duk da haka, a hankali yana fara nuna alamun dawowa kan ganiya.
James McAtee Nottingham Forest

Asalin hoton, Getty Images
Magoya bayan Nottingham Forest sun yi fatan James McAtee zai zama sabon Cole Palmer a ƙungiyar, bayan da ya bar Manchester City, domin samun damar buga wasanni.
Sai dai bai nuna wani tasiri ba. Duk lokacin da aka ba shi dama, ba ya yin wani abin a zo a gani, kuma har yanzu bai ci ƙwallo ba, bai kuma bayar ba aka zura a raga Forest mai fama da barazanar faduwa daga lig, amma yanzu ta tsira za ta ci gaba da wasa a Premier league a baɗi.
Conor Gallagher Tottenham
Conor Gallagher ya koma Tottenham daga Atletico Madrid a watan Janairu domin taimakawa ƙungiyar ta fita daga matsin da take ciki a Premier League. Amma tun zuwansa abubuwa sun ƙara tabarbarewa.
A wasa 11 da ya buga wa Tottenham a lig, Tottenham ba ta yi nasara ba — inda ta sha kashi sau takwas tare da canjaras uku. Bai ci ƙwallo ko ɗaya ba.
James Trafford Manchester City
James Trafford ya samu tayi daga Newcastle da Manchester City kan fara kakar nan, amma ya zaɓi komawa City daga Burnley kan fam miliyan 27.
Sai dai watakila yanzu yana nadamar wannan shawara. Bayan wasu kurakurai a farkon kakar wasan bana, Pep Guardiola ya maye gurbinsa da Gianluigi Donnarumma. Yanzu Trafford ya zama mai zama a benci, abin da wataƙila bai yi tsammani ba lokacin da ya koma ƙungiyar ta Etihad.
Phil Foden Manchester City

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da wahala a iya yarda cewa Foden shi ne ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na shekara biyu da suka gabata.
Tun daga wannan lokacin, ƙoƙarinsa ya yi matuƙar raguwa kuma a yanzu ya sami kansa a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasan Manchester City da ba su taɓuka wani abin arziki ba a kakar wasan bana.
A kakar wasanni biyu da suka gabata, ciki har da na yanzu, Foden ya ci ƙwallaye 23 kacal a wasanni 98 da ya buga wa ƙungiyar, ciki har da 10 a wasanni 49 da ya buga a bana.
Galibi Guardiola ya yi amfani da shi ne a matsayin wanda ya ke shigowa daga benci a kakar wasa ta bana, inda ake fifita sanya Rayan Cherki daga farkon wasanni.
Babu shakka Foden yana da basirar da zai iya taka rawar gani a tsakiya, amma yanayin rashin ƙoƙarinsa na baya-bayan nan ya kasance abun damuwa, lamarin da ya kai ga har ya rasa gurbi a tawagar ingila da za ta halarci gasar cin kofin duniya ta 2026.
Yayin da Bernardo Silva ke Shirin tafiya a ƙarshen kakar wasan bana, ana tunanin Foden zai iya farfaɗowa domin ya iya maye gurbinsa yadda ya kamata a kakkanin wasu masu zuwa.
A takaice, kakar Premier League ta 2025/26 ta ga wasu manyan ƴan wasan da aka saya suka kasa taka rawar gani, lamarin da ya sa suka zama cikin manyan waɗanda suka fi gazawa a kakar nan. Duk da cewa wasu da aka saya suna da kwarewa, amma sun kasa bajintar da suka yi a tsoffin ƙungiyoyinsu da ka ɗauko su.
Daga cinikin da aka yi mai ɗan karen tsada da aka kafa tarihi zuwa sayayyar da aka yi da karancin kuɗi kadan, waɗannan ƴan wasan har yanzu sun kasance abin takaici ga ƙungiyoyinsu.
Kafin kakar ta kare, dole ne su inganta wasanninsu cikin gaggawa domin tabbatar da cewa kuɗin da aka kashe a kansu sun dace, tare da kauce wa a rika tuna su cikin mafi munin sayayyar ƴan wasa a Premier League ta bana.











