Napoli za ta kammala ɗaukar Hojlund, Chelsea na zawarcin Xavi

Rasmus Højlund

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .
Lokacin karatu: Minti 2

Napoli ta ce za ta sayi ɗan wasan gaban Manchester United Rasmus Hojlund mai shekara 23 da ke zaman aro kan yarjejeniyar dindindin, a cinikin da zai fam miliyan 38. Ƙungiyar ta gasar Serie A tana daf da samun gurbin shiga gasar zakarun Turai na kaka mai zuwa. (Mirror)

Tsohon kocin Barcelona, ​​Xavi Hernandez, na cikin jerin sunayen waɗanda Chelsea ke nazari don zama sabon kocinta. (Independent)

Ƙungiyoyi da dama na Turai suna sa ido kan ɗan wasan West Ham Crysencio Summerville, mai shekara 24, inda ake ganin farashin ɗan wasan na ƙasar Holland zai karye idan Hammers ta faɗo daga gasar Premier zuwa Championship. (Telegraph)

Golan Tottenham da Italiya Guglielmo Vicario, mai shekara 29, da kuma ɗan wasan Liverpool da Ingila Curtis Jones, mai shekara 25, na cikin jerin ƴan wasan da Inter Milan ke hari a bazara mai zuwa. (Gazzetta dello Sport)

Kocin Liverpool Arne Slot na shirin ci gaba da zama a kulob ɗin, duk da cewa Ajax na zawarcin kocin ɗan ƙasar Holland. (Mirror)

Liverpool na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan bayan Bournemouth da Argentina Marco Senesi, mai shekara 28, wanda ke da yarjejeniyar fatar baki na komawa Tottenham idan suka kaucewa faɗuwa daga gasar Premier. (Talksport)

Barcelona na zawarcin ɗan wasan gaban Bournemouth, Junior Kroupi, mai shekara 19, amma za su fuskanci hamayya daga Manchester City da wasu ƙungiyoyin Premier da dama kan ɗan wasan na Faransa na ƴan ƙasa da shekara 21. (Sky Sports)

Kocin Newcastle United Eddie Howe zai samu damar jagorantar sake gina ƙungiyar tun bayan karɓar ragamar ta a shekarar 2021, inda ake sa ran samun gagarumin sauyi a St James' Park a wannan bazarar. (i sport)

Ƙungiyoyin Premier da dama ne ke sanya ido kan ɗan wasan gaban Portugal da Juventus Francisco Conceicao, mai shekara 23. (Gazzetta dello Sport)

Ƙungiyoyin gasar Major League Soccer, LA Galaxy da Inter Miami ne ke kan gaba wajen neman ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Manchester United ɗan ƙasar Brazil Casemiro, mai shekara 34, a lokacin da kwantiraginsa ya ƙare a Old Trafford, duk da sha'awar da ƙungiyoyi a Saudi Arabiya da Turkiyya ke nunawa kan ɗan wasan. (Talksport)

Ɗan wasan gaban Real Madrid da Brazil Vinicius Jr, mai shekara 25, yana son wasu abubuwa su sauya a Bernabeu - ba wai albashinsa kaɗai ba - kafin ya ƙulla sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar. (Radio Marca)