Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan takaran da za su tsaya wa manyan jam'iyyun Najeriya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
A yanzu da kusan dukkan manyan jam'iyyun Najeriya sun kammala zabukan fitar da 'yantakara, hankali ya fara komawa kan yadda babban zaben na 2027 zai wakana.
Tuni shirye-shiryen zaben suka kankama, duk da cewa zaben mai zuwa ya zo da sauye-sauye da dama da salo na daban.
A yanzu manyan jam'iyyun hamayya a kasar za a iya cewa su ne ADC da NDC da kuma PDP - duk da cewa har yanzu akwai tsagi biyu da ke ikirarin jagorancinta.
Yanzu dai kallo ya koma a sama, inda 'yan kasa suka fara lissafe-lissafen yadda za su gudanar da zabe, sannan su kuma 'yan takara suke tunanin yadda za su gwada kwanji.
Ganin yadda INEC ta fara nata shirye-shiryen, mun daddale fitattun 'yan takarar da kuma hasashen yadda za ta kaya a babbban zaben mai zuwa
Bola Tinubu - APC
Bola Ahmed Tinubu shi ne shugaban Najeriya mai ci a yanzu kuma jagoran jam’iyyar APC. Tsohon gwamnan jihar Legas ne wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa APC da kuma nasararta a zaɓuɓɓukan baya.
Tinubu ya zama dan takarar ne bayan samun kusan kuri’a sama da miliyan 10, inda ya kayar da abokin karawarsa Stanley Osifo wanda ya samu kuri’a 16,504.
Duk da cewa har yanzu APC ko Tinubu ba su ce komai kan mataimaki ba, amma ana hasashen Sanata Kashim Shettima zai ci gaba da kasancewa mataimakinsa
Atiku Abubakar- ADC
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar ADC domin neman shugabancin ƙasa karo na bakwai.
A zaɓen fitar da gwani na ADC da aka gudanar, Atiku ya samu kuri'a 1,846,370, inda ya kayar da Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri'a 504,117, sai Mohammed Hayatu-Deen wanda ya zo na uku.
Har yanzu dai Atiku bai sanar da wanda zai mara masa baya ba, amma ana hasashen zai iya zabar Rotimi Amaechi.
Peter Obi - NDC
Peter Obi tsohon gwamnan jihar Anambra ne wanda a zaben 2023 ya samu karbuwa sosai a takararsa a jam’iyyar Labour.
Bayan ya koma jam’iyyar NDC, shugabannin jam’iyyar sun amince da shi a matsayin wanda zai musu takara ta hanyar maslaha.
Sannan a ranar tabbatar da takarar ya sanar da tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin wanda zai mara masa baya.
Goodluck Jonathan – PDP
Goodluck Jonathan tsohon shugaban Najeriya ne a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.
Bayan daina jin duiyarsa a harkokin siyasa, ya sake komawa inda ake ambatonsa a matsayin wanda tsagin Kabiru Turaki na PDP ya tsayar a matsayin wanda zai mata takara, duk da cewa har yanzu akwai sauran rikici kan shugabancin jam’iyyar.
'Yadda za ta kaya'
Dr Kabiru Sufi, masanin siyasa kuma mai sharhi kan harkokin siyasa ya ce dama abin da ake so ke nan a samu 'yantakara masu kyau daga bangaren hamayya.
Ya ce abin da ake gudu a baya shi ne ya zama an dakile jam'iyyun hamayya daga tsayar da 'yantakara.
"Kuma hakan yanzu ya kai ga abin da ake hasashe cewa bayan sun yi zaɓen cikin gida kowacce za ta fitar da ɗan takara kuma ana ganin waɗannan da suka fitar din su ne masu ƙarfin da idan aka haɗa za a iya cewa an yi ƙoƙari."
Ya ce a baya da ake hasashen za a iya samun daƙile jam'iyyun hamayya masu karfine sai ya kasance jam'iyyun da za su rage marasa ƙarfi ne.
'Amma a halin yanzu wannan din ya sa mutane da yawa suna jiran su ga me zai kasance a wajen zaɓen da za a shiga musamman tunda a baya an yi ƙoƙarin jiran samun hadaka daga bangarorin hamayya guda biyu, amma ba a samu ba."
Sai dai ya ce duk da haka ana ganin wadanda suka fito ɗin musamman daga jam'iyyu guda uku manya akwai yiwuwar a samu karawa a wurare daban-daban, ''wanda hakan na iya ba da dama a ce dimokuraɗiyya ta yi aikinta"
Sufi ya ce an yi ta tunanin ganin samun haɗewar ko dunƙulewar ɓangarorin hamayya a wuri guda amma hakan ya gagara.
'Saboda haka wannan ne ya sa ake ganin cewa duk da haka dai akwai damarmaki da ya rage wa su ɓangarorin hamayya din, duba da kowanne yana da nasa abin da zai ba shi fifiko a kan ɗan’uwansa," in ji shi.
Masanin harkokin siyasar ya yi misali da cewa idan aka duba wanda yake takara a jam’iyyar ADC za a ce shi kaɗai ne ya fito daga yankin arewa a manyan jam'iyyun.
"To ka ga wannan ya ba shi fifiko a kan sauran. Sannan shi ma kuma idan ka duba kamar na jam'iyyar NDC, yana da fifiko ta ɓangarori guda biyu. Yana da fifiko ta da ma can shi ya ɗauki mataimakinsa wanda ake ganin haɗin ya yi sosai, amma zai ba su tagomashi a wurare da dama, musamman yankin kudu maso gabas da kuma jihar Legas watakila har ma da kuma da jihohin arewa, saboda mataimakin nasa."
Sufi ya ce wannan ya sa ana ganin cewa duk da ba a samu wancan haɗakar ba kowanne a cikinsu yana da wuraren da yake da fifiko samu wani advantage wanda yake yana da damar yin tasiri a kan ita jam'iyya mai mulki ɗin.
Masanin harkokin siyasar ya kara da cewa ya danganta ga yanayin da zaɓen ya zo da kuma irin yadda al'umma suka karɓi su kansu 'yan takarar.
"Saboda haka, za a iya cewa an kusa samun daidaito tsakanin ita jam'iyya mai mulki da su waɗannan jam'iyyun hamayya guda biyu ta fuskar gogayya, duk da dai saboda karfin mulkin za a iya cewa musamman yawan gwamnoni da jam'iyyar take da shi za a iya cewa ta ɗara su amma dai fifikon ya ragu sosai," in ji shi.
Kabiru ya ce rabuwar 'yan hamayya ya dan raba wa jama'a hankali musamman a cewarsa waɗanda ba su gamsu da salon mulki na ita jam'iyya mai mulki ba.
"Amma kuma yanayin da aka samu kai da kuma yanayin fitowar tasu ya danganta ga wane irin salon yaƙin neman zaɓe aka yi da kuma neman ƙuri’un al'umma da kuma ƙokarin jawo hankulan jama'a wajen jam'iyyar da ta fi dacewa su zaba."
Ya ce daga cikin abubuwan da za su taka rawa a zaben akwai rashin gamsuwa da APC a wasu bangaren, "akwai kuma wataƙila salon shi kansa kamfe ɗin da su jam'iyyun hamayyar za su bi. Da kuma kowanne wane ƙoƙari a yankunan da yake yana da ƙarfi da kuma yankunan da yake ba shi da ƙarfi. Duka waɗannan abubuwa ne da ka iya taimakawa."
'Alal misali, a jam'iyyun hamayya ɗin ana ganin fitowar Seyi Makinde daga APM na iya rage ƙuri'in ita jam'iyya mai mulki ɗin daga yankin kudu maso yamma, musamman daga ita jihar da yake mulki ta Oyo. To wannan ka ga ana ganin yana iya taimakon sauran jam'iyyun hamayya ɗin wajen ganin cewa inda da suke da rauni a yanzu su ma kuma ga shi sun ƙara samun ƙarfi," in ji Kabiru Sufi.