Gwamnatin Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan gaza kuɓutar da ɗaliban makaranta 42 da aka sace a jihar Borno da har yanzu ke hannun ƴanbindiga.
Iyayen ɗaliban sun bayyana fargaba cewa kamar gwamnati ta manta da ƴaƴansu, saɓanin irin matakan da suke jin ana ɗauka a jihar Oyo na ƙoƙarin ceto ɗaliban da aka sace.
Sai dai tuni mai bai wa shugaban Najeriyar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya musanta zargin da iyayen ɗaliban jihar ta Borno suka yi.
Yaran dai sun shafe kwana 17 a hannun ƴanbindiga tun bayan sace su a garin Mussa a ƙaramar hukumar Askira Uba.
Dakta Chi Namke shugaban al'umma ne a yankin ya shaida wa BBC cewa suna cikin tashin hankali kasancewar yaran da aka sace ƙanana ne.
"Daga gwamnatin Borno, akwai kwamishinan ilimi da ya zo amma daga wajen gwamnatin tarayya ba mu ga ko mutum ɗaya ba," in ji Dakta Chi Namke.
A cewarsa, irin haka tana faruwa a wasu jihohin kuma gwamnatin tarayya tana aika tawaga domin jajanta musu.
Ambasada Ahmad Shehu, shugaban wata gamayyar ƙungiyar farar hula a yankin arewa maso gabas ya ce haƙƙin gwamnati ne ta gaggauta ceto ɗaliban.
"Da aka yi na Mussa, ya faru a jihar Oyo a lokaci ɗaya, namu ba abin da aka yi, sai wancan kuma gwamnati ta ɗauki mataki." in ji shi.
Ya ƙara da cewa "shugaban ƙasa ya buƙaci manyan jami'an tsaro da su tare a jihar Oyo domin ganin an kuɓutar da yaran da aka sace.
Fadar gwamnatin ta bakin Abdulaziz Abdulaziz dai ta danganta iƙirarin iyayen ɗaliban jihar ta Borno da shelar ƴan adawa saboda a cewarsa shugaba Bola Tinubu yana ƙoƙari ya ga an yi abin da ya dace domin kuɓutar da ɗaliban.
A yau Talata ne ƙungiyar ƙwadago ta malaman makaranta NUT za ta jagoranci zanga-zanga a sassan Najeriya domin tilasta wa gwamnati ɗaukar matakan gaggawa na ceto ɗaliban.