Zafin kaye ne ya sa wasu ke zargin rashin adalci a tsayar da ni takara - MA Abubakar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, kuma dan takarar gwamnan jihar a zaben 2027 da ke tafe Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya musanta zargin da wasu da suka nemi takaraR da shi ke yi na cewa ba a gudanar da zaben cikin gida ba aka tsayar da shi takara.

A cewar tsohon gwamnan abubuwan da ake fada ko kadan ba gaskiya be, domin an gudanar da zaben cikin gida bayan kasa cimma maslaha a tsakanin wadanda ke takara.

''Bayan da an amince a sasantawa shugaban jam'iyya ya kira mu, sai biyu daga cikinmu suka bijire suka ce su basu yadda da wannan sasancin ba, don haka sai aka ce a je Bauchi a gudanar da zaben cikin gida''

Ya kara da cewa duk wani abu da za a ji daga bakin wani sabanin abun da shi ya fadi, to kila yana fada ne saboda zafin rashin nasara, da kuma cimma wata manufa ta kashin kansa.

''Ko gobe ka tafi shalkwatar APC ka ce a ba ka sakamakon zaben Bauchi za a baka, tsakanina da wanda ya zo na biyu ni ina da kuri'a sama da wani abu, shi kuma yana da kuri'a dubu ashirin da wani abu'' inji shi.

Cikin wadanda suka shiga neman tikitin takarar akwai ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tugga, da Sanata mai ci Sanata Umaru Shehu Buba, da jagoran yakin neman zaben shugaba Tinubu a Jihar Bauchi a 2023,Nuru Mani Soro, sai kuma Bala Mai Jama'a Wunti, wanda tsohon shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC ne.

Amma a karshe tsohon gwamnan jihar da ya yi jagoranci tsakanin 2015 zuwa 2019 Barista Muhammed Abdullahi Abubakar, ne ya samu, wanda ya yi shekara hudu a baya ya fadi zabe yanzu kuma ya samu tikitin takarar domin kammala shekara hudun da suka rage masa.

Wannan abu dai bai yi wa abokan burmin Baristan dadi ba.

Jihar Bauchi dai na daga cikin jihohin da za a samu sabon gwamna a babban zaben 2027, sai dai tun daga gudanar da zabukan fidda gwani da aka gudanar rikici ya dabaibaye jam'iyyun siyasa a jihar.

Zabukan fidda gwani a kusan duka jam'iyyun Najeriya na barin baya da kura tamkar dai wannan, wasu masana na ganin tsarin sulhu da jam'iyyar APC ta runguma, na daya daga cikin matakan da suke yi wa dimokradiyya dabai-bayi.