'Yan sandan tarzoma a Albania sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sandan tarzoma a Albania sun yi amfani da motocin fesa ruwa da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati a harabar Ma’aikatar Ilimi da kuma Kotun Ƙoli ta Ƙara a babban birnin ƙasar, Tirana.
Daga bisani, 'yan sanda sun sake fuskantar dandazon masu zanga-zanga, mafi yawansu ɗalibai ne, a wani babban wurin shakatawa da ke tsakiyar birnin, yayin da zanga-zangar ta shiga rana ta bakwai a jere.
Masu zanga-zangar na neman Firaministan ƙasar, Edi Rama, ya yi murabus daga mukaminsa.
Sai dai Mista Rama ya yi watsi da wannan buƙata, yana mai jaddada cewa ba zai sauka daga mulki ba.
Ya kuma ce "Da zarar ƙasa ta fara tattaunawa da masu tayar da tarzoma da amfani da tashin hankali, to ƙasar ta faɗi."
Wannan rikici na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun manyan zanga-zangar adawa da gwamnati a sassa daban-daban na Albania, inda masu zanga-zanga ke matsa lamba ga gwamnati kan batutuwan siyasa da tattalin arziki.





































