Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Juma'a 27/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. Kwankwaso ya zargi Abba da amfani da EFCC don ɓata masa suna, Aminu Kutama, BBC News Abuja

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin ɓata masa suna da kuma raunana damar jam'iyyarsa ta NDC a zaɓen 2027.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Jumaʼa, Sanata Kwankwaso ya ce yana zargin gwamnan da ƙoƙarin shigar da shi da iyalansa cikin ce-ce-ku-ce ta hanyar amfani da Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa, EFCC.

    Tsohon ministan ya kuma ce Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya taɓa aiki a ƙarƙashinsa a matsayin mataimaki na musamman, babban sakataren sirri da kwamishina, ya yi amfani da amincewar da ya samu a tsakaninsu wajen samun bayanan da yake zargin ana amfani da su wajen ɓata masa suna.

    Duk da dai ba a fito da wata shaida ta fili ba, Sanata Kwankwaso ya kuma yi zargin cewa gwamnan ya gabatar da wata buƙata ga EFCC watanni da suka gabata domin hukumar ta bincike shi, amma bayan abin da ya bayyana a matsayin rashin nasarar wannan yunƙuri, sai aka yi amfani da wata ƙungiya mai suna Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative, wato SACGGI, wajen matsa wa hukumar lamba.

    Karanta cikakken labarin a nan...

  2. Uganda na shirin janye dakarunta daga Kongo

    Uganda ta sanar da cewa za ta janye dakarunta daga wani gari da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) yayin da ake samun takun-tsaka tsakanin ƙasashen.

    Rundunar sojin Uganda ba ta bayyana dalilin janye dakarun daga garin Lubero ba, inda suke taimakawa sojojin Kongo wajen yaƙar ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta ADF.

    A ranar Alhamis, an gayyaci babban jami'in diflomasiyyar Uganda da ke birnin Kinshasa, bayan babban hafsan sojin ƙasar Muhoozi Kainerugaba ya bayyana goyon bayansa ga 'yan tawayen da ke yankin.

    Mista Kainerugaba ɗa ne ga shugaban Uganda Yoweri Museveni.

    Rundunar sojin Uganda ta ce za ta ci gaba da aikin hadin gwiwa da sojin Kwango a wani ɓangaren ƙasar.

  3. Wane ne ya gaji Sheikh Dahiru Bauchi shekara ɗaya bayan rasuwarsa?, Imam Saleh, Senior Journalist BBC World News

    A ranar 26 ga watan Nuwamban 2025 ne Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, rasuwa, bayan shafe kusan shekara ɗari yana rayuwa, koyarwa da yaɗa ilimin addinin Musulunci.

    Yanzu shekara guda ke nan da rasuwarsa, amma tasirinsa na ci gaba da bayyana a tsakanin dubban almajiransa da mabiyansa, musamman a Najeriya da wasu sassan Afirka ta Yamma.

    Sheikh Dahiru Bauchi ya shafe fiye da shekaru saba'in yana koyar da Alƙur'ani, tafsiri da sauran ilimomin addinin Musulunci, tare da taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya.

    Rasuwarsa ta bar babban gibi, ba kawai a cikin iyalinsa da dubban almajiransa ba, har ma a fagen ilimin addini da jagorancin Tijjaniyya, inda ya kasance ɗaya daga cikin manyan jagororin da suka yi tasiri.

    Yayin da ake cika shekara guda da rasuwarsa, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: Su waye suka karɓi nauyin ci gaba da ayyukan da ya assasa? Wa ke ci gaba da koyar da iliminsa, bayar da fatawowi da jagorantar mabiyansa a harkokin addini da na ɗarikar Tijjaniyya?

    Domin amsa waɗannan tambayoyi, BBC ta tattauna da Malam Aminu Sheikh Dahiru Bauchi, ɗaya daga cikin 'ya'yan marigayin, domin jin yadda iyalinsa da almajiransa ke ci gaba da tafiyar da gadon da ya bari.

    Danna nan don karanta cikakken labarin...

  4. Najeriya da wasu ƙasashe 15 na cikin barazanar fuskantar yunwa

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa matsalar yunwa za ta ƙara tsananta sosai a wurare 16 da ke fuskantar matsalar abinci a faɗin duniya cikin watanni shida masu zuwa, a daidai lokacin da wasu sassan Afrika ke fuskantar barazanar fari.

    Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da Shirin Samar da Abinci ta Duniya (WFP) sun bayyana a yau Juma'a cewa ƙasashen Sudan, Sudan ta Kudu, Somaliya, arewacin Najeriya da kuma Yemen - su ne ƙasashen da suka fi fuskantar babbar barazanar yunwa.

    Sun ce hakan zai faru ne sakamakon rikice-rikice, ɗaiɗaita mutane, matsin tattalin arziki da kuma sauyin yanayi.

    Adadin wuraren da za su fuskanci barazanar yunwa ya ƙaru daga 13 zuwa 16 a yanzu, idan aka kwatanta da rahoton da aka fitar a watan Yuni, inda aka ƙara Chadi, Uganda da wasu sassan kudancin Afirka da Amurka ta Tsakiya cikin jerin, yayin da aka cire Lebanon.

    A sabon rahoton daga watan Disambar 2026 zuwa Mayu 2027, hukumomin sun yi gargaɗin cewa raguwar kuɗaɗen tallafin jin ƙai na kawo cikas ga ƙoƙarin hana faɗa wa cikin matsalar yunwa.

    Conor Elliott, wani babban jami'i a sashen ayyukan gaggawa hukumar abincin da aikin gona ta duniya FAO, ya bayyana cewa tallafin da ƙasashe biyar da ke fuskantar babbar barazanar yunwa ke samu ya ragu da kashi biyu bisa uku tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025.

    "Waɗannan sauye-sauye ne masu matuƙar girma a fannin tallafin ƙasashen duniya," in ji shi.

    Ya kuma yi gargaɗin cewa rage tallafin na kawo cikas ga tattara bayanan da ake buƙata domin tantance ainihin girman matsalar yunwar.

  5. Ƴanbindiga sun kashe mutum 16 a Plateau

    Aƙalla mutum 16 ne suka mutu a wani hari da ƴanbindinga suka kai garin Jebbu Miango da ke karamar hukumar Bassa na jihar Plateau.

    Harin wanda aka kai ranar Laraba 25 ga Nuwamba da misalin karfe 11 na dare, ya kuma jawo jikkata wasu mutum huɗu waɗanda ke samun kula a yanzu.

    Wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Cigaban Al'ummar Irigwe, Sam Jugo ya fitar, ta ce maharan sun kutsa garin ne ɗauke da muggan makamai da kuma harsasai.

    A cewar ƙungiyar, lamarin ya jefa mazauna garin cikin fargaba, bayan samun gawawwaki 16 yashe da safe.

    Basaraken yankin, Nggwe Gado Dama, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka tura jami'an tsaro zuwa yankin.

    Ƙungiyar ta Irigwe ta yi Alla-wadai da kashe-kashen sannan ta buƙaci mazauna garin da kada su ɗauki doka a hannunsu, inda ta buƙace su da su bar jami'an tsaro su yi bincike don tabbatar da kama waɗanda suka kai harin.

    Ita ma rundunar ƴansanda a jihar ta Plateau ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ta ce alkaluman waɗanda suka mutu ya kai 17.

  6. 'Muna sa ido kan ruwan teku bayan kifewar jirgin dakon mai'

    Firaministan Sifaniya, Pedro Sánchez, ya ce gwamnatinsa na sanya ido sosai kan ruwan tekun da ke kusa da tsibirin Ibiza bayan da wani jirgin dakon mai ɗauke da man dizal ya kife a kusa da tsibirin a ranar Alhamis.

    Da farko jami'ai sun bayyana cewa jirgin ya nutse, sai dai yanzu sun ce yana saman ruwa, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin dakile duk wata barazana da ka iya shafar tekun da ke da matuƙar muhimmanci a yankin.

    Ana sa ran a gudanar da bincike kan jirgin a yau Juma'a, kafin a kwaso jirgin. An ceto ma’aikatan jirgin guda 17, amma daga baya ɗaya daga cikinsu ya rasu a asibiti.

    Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin wannan hatsari ba.

  7. Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara ɗaya da rasuwa yau Juma'a

    A yau Juma'a 27 ga Nuwamban 2026, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara ɗaya da rasuwa.

    Fitaccen malamin ya rasu ne ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025.

    Shehin malamin ya rasu ne a asibitin sojojin sama da ke jihar Bauchi bayan gajeriyar jinya.

    Ya kuma rasu yana da shekaru 98 a duniya.

    Shiekh Dahiru Usman Bauchi babban malamin darikar Tijjaniyya ne da ake ji da shi a nahiyar Afirka, sannan malami ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da al'kur'ani, littafin Musulmi mafi girma.

    Shehin malamin na ɗaya daga cikin malamai a Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addinin Musulunci hidima.

  8. Ina fatan Putin zai halarci taron ƙasashen G20 - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana fatan takwaransa na Rasha Vladimir Putin zai halarci taron ƙasashen 20 masu karfin tattalin arziki wato G20 da za a gudanar a watan gobe a jihar Florida.

    Sai dai Trump ya amince cewa mai yiyuwa ne Putin ba zai halarta ba, yana mai cewa akwai wasu da ba za su so ganin shugaban na Rasha a wajen taron ba.

    Putin ya halarci tarukan ƙasa da ƙasa da dama a shekarar nan, ciki har da na ƙungiyar APEC da aka yi kwanan nan a China.

    Duk da haka, har yanzu akwai sammacin kama Putin da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta bayar, bisa zargin aikata laifukan yaƙi.

  9. Zelensky ya nuna takaicinsa ga Amurka kan jinkirin kai makamai

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya nuna matuƙar takaicinsa ga Amurka, yana mai cewa jinkirin isar da muhimman makaman kariya daga hare-haren makamai masu linzami na ci gaba da janyo asarar rayuka a Ukraine.

    A wata hira da BBC, Mista Zelensky ya kuma zargi Washington da rashin matsa wa Rasha lamba a yayin tattaunawar samar da zaman lafiya.

    Haka kuma ya ce ya ji mamaki ganin Shugaba Donald Trump ya bayyana Vladimir Putin a matsayin aboki.

    Zelensky ya ce duk da cewa Trump ne ke da ƴancin yanke shawara kan ra'ayoyinsa da matakan da zai ɗauka, a fili yake cewa Shugaba Putin “mai kai hari ne da kashe mutane.

  10. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi barkan mu da safiyar Juma'a.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafukan mu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa muku.