Yadda matsalolin tsaro ke raunata 'yancin addini a Najeriya - MDD

Asalin hoton, BBC/Getty
Majalisar dinkin duniya ta bayyana damuwarta kan yadda matsalolin tsaro da rashin daukar matakai daga gwamnati ke taimakawa wajen raunata 'yancin yin addinai ga 'yan Najeriya.
A wani bincike da Majalisar ta yi a jihohin Filato da Kano, ta ce ta gano cewa ba duka 'yan Najeriya ne ke cin moriyar 'yancin yin addini dai-dai da kowa ba, duk kuwa da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar kan 'yancin yin addinin.
Majalisar ta kuma ce ta gudanar da binciken ne da hadin gwiwar hukumar kare hakkin bil'adama ta Najeriya.
Wakiliya ta musamman a Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakkin bil'adama, da ta kawo ziyara Najeriya, Nazila Ghanea, ta ce Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kowanne dan'adam ya gudanar da addininsa ba tare da fargaba ko tilastawa ba.
Ta ce," Yin addinin da mutum ke so a Najeriya na fuskantar matsaloli daban-daban a Najeriya."
" Dokokin da ke samar da 'yancin mutunta dan'adam da hana nuna wariya da kuma 'yancin yin addinai na da karfi a kundin tsarin mulkin Najeriya, to amma mutane ba sa amfana da su yadda ya kamata saboda mabambantan tsarin shari'oi da kasar ke amfani da su da kuma yadda al'adun wasu yankuna ke danni wadannan 'yancin."In ji ta.
Jami'ar Majalisar Dinkin Duniyar, ta ce," Mutane da dama na nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kawo tarnaki ga 'yancin yin addini."
Cikin shawarwarin data gabatar, Ms Ghanea, ta ce akwai bukatar a rinka amfani da hukunci da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta tanada kan cin zarafi da kisan kare dangi a kotunan Najeriya.











