Wane tasiri Atiku da Amaechi za su yi a zaɓen Najeriya na 2027?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta cimma matsayar tsaida tsohon ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi a matsayin ɗantakarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar ne zai yi wa jam'iyyar takarar shugaba ƙasa, bayan lashe zaɓen fitar da gwani da ADCn ta gudanar a ranar 25 ga watan Mayu, 2026.

Atiku ya samu ƙuri'u 1,846,370, inda Amaechi ya zo na biyu da ƙuri'u 504,117, sai Hayatu-Deen, da ya samu ƙuri'u 177,120.

Tun bayan zaɓen ne Atiku yake ta ƙoƙarin ganin ya samu goyon bayan ƴan jam'iyyar da suka yi takara tare, har ma ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Rivers ɗin Amaechi da Hayatu-Deen.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotu ta umurci hukumar zaɓen ƙasar INEC ta soke rijistar jam'iyyar ta ADC saboda gaza cika sharuɗɗan dokokin ƙasa na samun aƙalla kaso 25 na kujerun da aka yi takara a zaɓen 2023.

Tuni masu sharhi suka fara tsokaci kan tasirin da wannan tikitin na Atiku da Amaechi, musamman saboda ficewar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso daga jam'iyyar zuuwa NDC, matakin da ake ganin ya ƙara rage wa jam'iyyar karsashi.

Dalilin zaɓen Amaechi

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi ne ya sanar da matakin jam'iyyar a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce an zaɓi Amaechi ne bayan shawarwari masu zurfi da shugabannin jam'iyya da masu ruwa da tsaki.

Jam'iyyar ta bayyana haɗin nasu a matsayin "tikitin haɗin kai da ceto ƙasa."

Ya ƙara da cewa Amaechi ya samu goyon baya sosai a zaɓen fidda gwani inda ya zo na biyu, kuma yana da ƙwarewa a harkokin gwamnati.

Jam'iyyar ta ce gogewar Amaechi a fannoni daban-daban na sanya shi cikin sahun manyan 'yan siyasa masu cikakken ƙwarewa. Ta ce wannan gogewa za ta taimaka wajen ƙarfafa jagorancin Atiku da kuma faɗaɗa tasirin jam'iyyar a faɗin ƙasar.

ADC ta kuma bayyana cewa haɗin Atiku da Amaechi zai haɗa yankuna da al'umma daban-daban a Najeriya.

A tsawon shekara sama da 30 da suka gabata, tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar ya kasance dumu-dumu cikin harkokin siyasar ƙasar.

Ya daɗe yana fafutukar siyasar tare da yunkurin neman shugabancin kasar mai ɗimbin al'umma da tarin arziki.

Wane tasiri haɗin Atiku da Amaechi zai yi?

Masana harkokin siyasa na ganin Atiku ya zaɓi Amaechi ne domin guje wa abin da ya faru da shi a 2023 ya sake faruwa.

Wasu na ganin rashin nasarar Atiku a zaɓen 2023 na da alaƙa da ƙin zaɓar ministan Abuja na yanzu Nyesom Wike a matsayin abokin takararsa, duk da cewa shi ya zo na biyu a zaɓen fitar da gwani na PDP a 2022 - lamarin da ya fusata shi har ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa "don ganin Atikun bai yi nasara ba".

Dr Kabiru Sufi, masanin siyasa ya ce wannan matakin ne zaɓin da ya rage wa ADC idan har tana son samun goyon bayan kudancin ƙasar, idan aka yi la'akari da yankin da sauran ƴan takarar shugaban ƙasar suka fito.

"Zaɓin da suka rage ba su da yawa, duba da cewa shi da Amaechi suka yi takara...abin da ya rage masa shi ne ya ɗauko daga can yankin," in ji Sufi.

Masanin yana ganin ɗaukar mataimaki daga kudu maso kudu zai iya sa yankin su iya karkata ra'ayinsu kan tikitin, saboda sauran jam'iyyun ba su ba su wani muhimmanci ba a takarar 2027.

"ADC tana ganin idan tattare ƙarfinta a wannan yanki, za ta iya kai labari."

A baya dai Amaechi ya sha nanata cewa ba wai ya sayi tikitin takarar shugaban ƙasa a ADC ba ne domin yana nemi muƙamin mataimaki.

Abin da ya rage wa Atiku da Amaechi

A yanzu dai ana jiran ganin manufofin da ƴan takarar za su ɓullo da su domin jan ra'ayin ƴan Najeriya.

Masanin siyasa Farfesa Abubakar Kari ya ce ƴan takarar za su iya taɓuka abin kirki musamman wajen jan ra'ayin al'ummar Igbo a Kudu maso Kudancin ƙasar, ganin yadda Amaechi yake da gogewar siyasa na tsawon shekaru.

"Mai yiwuwa kuma saboda Amaechi ya zo biyu a zaɓen fidda gwani da aka yi... in kuma aka yi la'akari da gogewarsa a siyasa".

Farfesa Kari ya ce ƙabilar Amaechi za ta iya tasiri ga tikitin takarar tasu, musamman yadda yake nuna alfaharinsa da wannan ƙabilar.

Masanin ya ce abin da ƴan siyasar za su maida hankali yanzu shi ne ɓullo da tsarin da sai sa al'ummar Najeriya su aminta da su.

"Dole ne sannu a hankali su kakkafa tsari a lunguna da saƙo na ƙasar nan," in ji shi.

Kari ya ce yana da kyau su yi zawarcin wasu gogaggun ƴan siyasa na ƙasar domin samun goyon bayansu idan suna son takarar su ta yi tasiri.

Wane ne Atiku Abubakar?

Atiku Abubakar gogaggen ɗan siyasa ne da ya shafe shekaru da dama yana jan zarensa. Hasalima yana daga cikin jiga-jigan mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP.

An haifi Atiku Abubakar ranar 25 ga Nuwamban 1946 a Jihar Adamawa da ke Arewa Maso Gabas, kuma ya kasance jigon dan siyasa kuma hamshaƙin attajiri a Najeriya.

Ya mallaki katafariyar Jami'ar ABTI, wato American University of Nigeria a Jiharsa ta Adamawa.

Kamfaninsa na hada-hadar man fetur, mai suna Intels Nigeria Limited na hada-hada a kasashen Afirka da suka hada da Angola da Equatorial Guinea da Gabon da Sao Tome and Principe.

Atiku Abubakar ya tsunduma harkokin sisaya a 1989, kuma yana cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa na mulkin soji, Janar Shehu Musa Yar'adua.

Ya shiga jam'iyyu daban-daban tun da ya shiga harkokin siyasa.

Haka kuma yana goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.

Amaechi da muƙaman da ya riƙe

An haifi Rotimi Amaechi a ranar 27 ga Mayu, 1965 a garin Ubima da ke ƙaramar hukumar Ikwerre a Jihar Ribas da ke Kudu Maso Kudancin Najeriya.

Ya yi karatu a jami'ar Fatakwal, inda ya samu digiri a fannin Turanci a shekarar 1987

Fitaccen ɗan siyasa ne kuma ya yi gwamnan jihar Ribas da kuma riƙe muƙamin tsohon Ministan Sufuri na Najeriya a mulkin shugaba Buhari tsakanin 2015-2023.

Harkar siyasarsa ta fara ne tun a jamhuriyar Najeriya ta uku, inda ya zama sakataren jam'iyyar NRC a ƙaramar hukumar Ikwerre. Daga bisani ya zama babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Ribas, Dr. Peter Odili.

A shekarar 1999, aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dokokin Jihar Ribas mai wakiltar mazabar Ikwerre, inda har ya riƙe muƙamin kakakin majalisa, har zuwa shekarar 2007.

Ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP gabanin zaɓen 2027, amma jam'iyyar ta sauya sunansa da wani. Sai dai ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli, wacce ta yi watsi da matakin jam'iyyar kuma ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Kotun ta rantsar da shi a ranar 26 ga watan Oktoba, 2007.

Ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a APC a 2023 amma daga baya ya janye wa Tinubu.

Muƙaman da Atiku ya riƙe

Atiku Abubakar na daga cikin ƴan siyasar da suka fi daɗewa suna tashe a siyasar Najeriya.

Tun bayan da Najeriya ta dawo mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasar Najeriya na 11, a mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo a tsakanin 1999 zuwa 2007.

An zaɓi Atiku Abubakar a matsayin gwamnan jihar Adamawa a 1998, inda daga bisani Cif Obasanjo ya zabe shi domin kasancewa mataimakinsa.

Daga wancan lokacin zuwa yanzu, wannan ne karo na huɗu da Atiku Abubakar ke tsayawa takarar shugaban kasa, ko da yake ya tsaya zaben fitar da gwani sau da dama.

Tun bayan nan kuma ya ci gaba da kasancewa cikin manyan masu neman kujerar shugaban ƙasa.

Bai sake riƙe wani babban muƙamin gwamnati ba tun daga lokacin, ya ci gaba da kasancewa cikin manyan ƴan adawa da masu tasiri a siyasar Najeriya.