Chelsea na zawarcin Lopez, Fulham na son ta ci gaba da riƙe Bassey

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Kocin Chelsea, Xabi Alonso, na son yin musayar 'yan wasa da Barcelona, inda zai bayar da ɗan wasan Brazil, Estevao Willian, mai shekara 19, domin ya samu ɗan wasan Spain, Fermin Lopez, mai shekara 23. (El Nacional - in Catalan), external

Aston Villa na iya dawo da Alejandro Garnacho mai shekara 22 kafin ƙarshen kakar wasa wanda ta bada shi aro ga Chelsea.(Give Me Sport), external

Arsenal na zawarcin dan wasan Sporting Lisbon da ƙasar Spain, Ivan Fresneda, mai shekara 22, domin ya maye gurbin Ben White a nan gaba.(The Athletic - subscription required), external

AC Milan na son ɗaukar dan wasan Ingila Omari Hutchinson mai shekara 23 wanda aka ba da shi aro ga Nottingham Forest, kuma a shirye take ta kashe fam miliyan 40 saboda shi.(Gazzetta dello Sport via SportWitness), external

Besiktas na son ɗaukar ɗan wasan Newcastle United,Joe Willock, mai shekara 27. Ana sa ran ƙungiyar ta ƙara ƙaimi wajen neman sa a wata mai zuwa domin ta kammala ɗaukarsa a watan Janairu.(A Spor - in Turkish), external

Fulham na ƙoƙarin shawo kan ɗan wasan Najeriya,Calvin Bassey,mai shekara 26,domin ya ci gaba da zama a ƙungiyar na dogon lokaci. Sai dai albashin da ƙungiyar ke iya bayarwa bai kai na abin da Manchester United ke son ta biya shi ba.(TeamTalk), external

Juventus na da kwarin gwiwar mayar da yarjejeniyar aron ɗan wasan Jamus, Nick Woltemade, mai shekara 24, daga Newcastle United zuwa ta dindindin.(Football Insider), external

Watakil Liverpool ta sayar da ɗan wasan Netherlands, Ryan Gravenberch, mai shekara 24, duk da cewa har yanzu yana da kwantiragi da ƙungiyar zuwa shekarar 2032. Rahotanni sun ce ɗan wasan ya rasa tagomashi a wajen koci Andoni Iraola.(Football365), external

Manchester United na sa ido kan dan wasan Boca Juniors, Facundo Herrera, mai shekara 20, daga Argentina.(El Crack Deportivo - in Spanish), external

AC Milan na son ta ɗauko Endrick mai shekara 20 daga Real Madrid, kuma a shirye take ta bai wa Madrid damar sake sayensa a gaba.(Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Barcelona na sha'awar ɗaukar ɗan wasan Como, Nico Paz, mai shekara 22. Sai dai ƙoƙarin ɗaukarsa na fuskantar ƙalubale saboda Real Madrid na da damar sake sayen ɗan wasan kan fam miliyan 70 a shekarar 2027.(El Nacional - in Catalan), external