Sabbin dabarun da ƴanbindiga ke amfani da su don tara kuɗi a Najeriya

Cibiyar tattara bayanan sirri kan sha'anin kuɗi ta Najeriya, (NFIU) ta ce ƴanbindiga na ƙara mafani da sabbin hanyoyin samun kuɗi domin ci gaba da ayyukansu.
NFIU ta yi zargin cewa masu tara wa ƙungiyoyin kuɗi da ke zaune a ƙasashen waje na amfani da shafukan sada zumunta wajen neman wa ƙungiyoyin tallafi ta hanyar fakewa da ayyukan jin ƙai da tallafin ilimi, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Cibiyar ta ƙara da cewa ''ana amfani da hanyoyi daban-daban wajen tira kuɗaɗen ga ƙungiyoyin masu riƙe da makamai a Najeriya''.
Dama dai an jima ana zargin wasu mutane da taimaka wa ƙungiyoyin ƴanbindiga wajen ɗaukar nauyin kuɗaɗen gudanar da su, ta hanyar hanyoyi daban-daban
Waɗanne sabbin hanyoyi ne?
"Wasu daga cikin abubuwan da binciekn ya gano shi ne wasu na amfani da shafukan sada zumunta wajen neman tallafi a kafafen sada zumunta, kuma suna tara kuɗi ne domin ayyukan agajin jinƙai ko tallafin ilimi. Haka kuma yana amfani da manhajojin sadarwa masu ɓoye bayanai kamar Telegram da Signal wajen raba hanyoyin shiga wasu shafuka da aka tsara yadda za su gamsar da masu ba da gudunmawa, ko kuma asusun banki na yau da kullum'', kamar yadda NFIU ta yi ikirari.
''Daruruwan masu tausayawa sun riƙa bayar da gudunmawar kama daga dala 50 zuwa 500, adadin da bai kai yadda hukumomin sanya idanu kan hada-hadar kuɗi za su ankara da su shi'', a cewar NFIU.
Cibiyar ta ƙara da cewa ana tattara waɗannan kuɗaɗe ne a wani "babban asusu" da ake sarrafawa daga ƙasashen waje, sannan a tura su zuwa wasu wurare da zarar sun kai wani ƙayyadadden adadi.
A wani rahoto na daban kuma, shafin Jaridar Premium Times ya ruwaito cewa masu ɗaukar nauyin ta'addanci na amfani da asusun banki da aka buɗe da sunayen mata wajen hada-hadar kuɗaɗen.
Jaridar ta ambato rahoton NFIU na cewa kwamandojin ƴan ta'adda maza da masu kula da harkokin samar da kayan aiki da dabaru suna sarrafa asusun banki a ɓoye waɗanda aka buɗe da sunayen matansu da ƴan'uwansu mata.
Rahoton ya ce suna cin gajiyar yadda hukumomi ba su cika zargin mata da hannu wajen samar da kuɗaɗen da ake amfani da su wajen aikata laifuffuka ba.
NFIU ta ce maza ne ke amfani da waɗannan asusun da aka buɗe da sunayen mata, inda suke riƙe da katinan ATM da bayanan shiga asusun ta waya da lambobin sirri.
A cewar rahoton, sau da yawa matan ba sa ma sanin irin mu'amalolin da ake gudanarwa ko kuma yawan kuɗaɗen da ke ratsa ta asusun nasu.
Ya ake yi da kuɗaɗen idan an tara?
NFIU ta ce bayan an tara kuɗin an karkara kaɗan-kaɗan sannan a tura su a tura su ta hannun kamfanonin canjin kuɗi na ƙasashen waje da kuma manhajojin aika kuɗi zuwa wata hanyar sadarwa ta masu karɓa da tura kuɗi (money mules) a Najeriya.
Wasu daga cikin waɗannan mutane ɗalibai ne da masu ƙananan sana'o'i da kuma 'yan uwansu, wanda NFIU ta ce an yi hakan ne domin ɓoye asalin kuɗaɗen da kuma inda ake kai su.
Da zarar an tattara kuɗin, ana mayar da su tsabar kuɗi, ko kuma a yi amfani da su wajen sayen kayayyakin da za a iya amfani da su ta hanyoyi daban-daban kamar babura da takin zamani da na'urorin intanet na tauraron ɗan'adam (satellite internet equipment).
Haka kuma ana tura wasu daga cikin kuɗin ta hanyoyin manhajojin banki d ake amfani da shi ta wayar hannu zuwa ga masu kula da harkokin sufuri da kayan aiki da kuma jami'an da ke aiki a filin daga, kamar yadda NFIU ta yi ikirari.
Yadda lambobin waya ke kawo cikas ga bincike

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar rahoton na NFIU, masu amfani da asusun bankin kan haɗa wasu lambobin wayarsu da asusun da aka buɗe ba da sunayensu ba, ta yadda saƙonnin sanarwa da damar amfani da bankin ta waya za su riƙa zuwa gare su maimakon masu asusun.
Hukumar ta ƙara da cewa ana yi wa waɗannan layukan wayar rajista da sunayen mutanen da suka rasu ko kuma wasu da ake amfani da su a matsayin wakilai domin ɓoye ainihin masu amfani da su
"Sukan yi kutse wa tsaron da ke tsakanin banki da layukan waya da kuma lambobin BVN, ta hanyar amfani da layukan da ake sayarwa marasa rajista ko layukan da ake sayarwa da rajista da sunayen mutane na da suka mutu, ko layukan da aka yi wa rajista da sunayen mata.'', in ji rahoton.
Rahoton ya ƙara da cewa hakan na kawo cikas a binciken bibiya, domin a duk lokacin da aka ankare da wata hada-hadar kudi da ake zargi, idan aka bibiyi lambar wayar aka tarar ba ta da alaƙa da zargi, sai masu binciken su watsar da binciken, lamarin da zai sa mai aikata laifin ya ci gaba da gudanar da ayyukansu a ɓoye''.
NFIU ta bayar da misali da ƙungiyar ISWAP, wadda ta ce na amfani da "cikakkun bayanan hada-hadar kuɗi wajen ɓoye ainihin manufarsu.
NFIU ta ce ta kuma gano cewa masu gudanar da waɗannan hada-hada na amfani da kalmomin sirri da wasu haɗakar haruffa da lambobi a bayanan tura kuɗi.
A cewar rahoton, a wasu lokutan suna sauya harshe ko amfani da kalmomi da ba sa jawo hankali domin kauce wa tsarin sanya ido na atomatik da ke gano mu'amalolin da ka iya kasancewa masu alaƙa da ta'addanci.
Rahotannin amfani da tara kuɗi daga jama'a don aikata laifuffuka sun fara fitowa ne daga kuɗaɗen fansa da ake biyan ƴan bindiga a jihohin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa iyalai da makusantan mutanen da aka yi garkuwa da su na amfani da hanyoyin tara kuɗi daga jama'a domin samun kuɗaɗen fansa, lamarin da ke ɗauke da haɗarin ƙarfafa ci gaba da wannan mummunar ɗabi'a.











