Dawo da Nijar cikin Ecowas da amfani da dakarun ECOMOG: Abubuwan da Atiku ya faɗa wa BBC

Atiku zai yi takara a kara na shida a 2027 a ƙoƙarin zama shugaban Najeriya
Bayanan hoto, Atiku zai yi takara a karo na shida a 2027 a ƙoƙarin zama shugaban Najeriya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Jagoran ƴan adawa a Najeriya Atiku Abubakar na ci gaba da tono abubuwan da suka gabata, yana suka tare da faɗin yadda nashi tsarin zai bambanta da na shugaban ƙasar mai ci Bola Tinubu, idan ya hau mulki.

A wata tattaunawa da BBC, Atiku ya ce matakin da Najeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirka suka ɗauka kan Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkin Faso bayan faruwar juyin mulki a ƙasashen bai dace ba.

Hakan na zuwa ne bayan alƙawarin da Atiku ya yi kan mayar da tallafin man fetur a ƙasar ya tayar da ƙura.

Tallafin man fetur na cikin mataki mafi girma da Bola Tinubu ya ɗauka bayan hawan shi kan mulki, lamarin da ya shafi kowane fanni na rayuwa da tattalin arziƙin al'ummar ƙasar.

Atiku na iƙirarin sauya wadannan muhimman manufofin gwamnati ne yayin da ake tunkarar babban zaɓen ƙasar na 2027, inda shugaba Tinubu ke neman wa'adi na biyu, yayin da Atiku wanda ya zo na biyu a zaɓen 2023 zai sake yin takara a jam'iyyar hamayya ta ADC.

'Zan dawo da Nijar cikin Ecowas'

Lokacin da aka tambayi ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC game da abin da zai yi wajen ganin an samu tsaro a Najeriya, ya nuna cewa hadin gwiwa tsakanin ƙasashen yammacin Afirka shi ne babban abin da zai mayar da hankali.

Matsalar tsaro ta shafe shekaru tana addabar Najeriya, inda ƙasar ke fama da matsalar Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.

Lamarin ya shafi ƙasashe masu maƙwaftaka kamar Nijar, Kamaru da kuma Chadi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Atiku ya ce: "Zan samu shugabannin Ecowas mu zauna mu yi shawara, inda za mu yi amfani da dakarun ECOMOG domin tabbatar da an samu zaman lafiya".

ECOMOG, wato 'Economic Community of West African States Monitoring Group', wata tawagar dakaru ne na ƙasashen yammacin Afirka da ake turawa domin aikin tabbatar da zaman lafiya a ƙasashen yankin yammacin Afirka da ke fama da rikici.

An kafa ta ne a shekarar 1990 lokacin yaƙin basasar Laberiya, inda dakarun suka taka rawa wajen tabbatar da tsagaita wuta da kuma shiga tsakani.

Haka nan dakarun sun yi aiki a ƙasashen Saliyo da kuma Guinea Bissau.

Sai dai kan ƙasashen yammacin Afirka ya rarrabu bayan juyin mulki da aka samu a ƙasashen Nijar (2023), Burkin Faso (2022) da kuma Mali (2021), lamarin da ya kai ga cewa ƙasashen uku sun ɓalle, inda suka kafa ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel (AES) bayan da ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar ɗaukar matakin soji idan sojoji ba su mayar wa fararen hula mulkin ba.

A tattaunawar da Atiku, jagoran adawar ya ɗora alhakin ficewar ƙasashen kan Shugaba Tinubu wanda shi ne shugaban ƙungiyar ta Ecowas a lokacin da aka yi taƙaddamar.

"Ban ga dalilin da ya sa Najeriya za ta ce ba za ta yi hulɗa da Nijar ba saboda an samu juyin mulki, Nijar da Najeriya al'umma ɗaya ne. Domin sojojin sun karɓi mulki bai kamata a sallami Nijar da Ecowas ba.

"Zan tabbatar da ganin an samu fahimtar juna an dawo da Nijar da Burkina Faso da Mali su dawo cikin Ecowas," in ji Atiku a tattaunawar tasa da BBC.

Haka nan Atiku ya ce yana sa ran magance matsalar tsaron Najeriya cikin shekara ɗaya.

"Abin da zan yi shi ne ƙara yawan jami'an tsaro da kayan aiki, bai wa matasa aikin yi...muna jin cikin dhekara ɗaya idan Allah ya yarda za mu yi maganin waɗannan abubuwa (matsalar tsaro)," in ji Atiku.

'Yadda zan cire tallafin man fetur'

Kusan mako biyu ke nan ana ta ce-ce-ku-ce tun bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana aniyarsa ta cire tallafin man fetur idan ya hau kan mulki a 2027.

Kamar mutane da dama a Najeriya, Atiku na ganin cewa cire tallafin man fetur shi ne silar matsalolin matsin tattalin arziƙi da al'ummar ƙasar ke ciki.

"Ana cikin ƙunci, ana cikin rashi da rashin aikin yi, wannan tallafin man fetur da aka janye shi ne babban abin da ya haifar da hakan. Ban taɓa ganin an sha wahala ba a ƙasar nan kamar wannan lokaci," in ji Atiku a tattaunawar da BBC.

Gwamnatin Najeriya ta mayar wa Atiku martani, inda ta bayyana cewa batun tamkar rashin fahimtar abin da ke faruwa ne da tattalin arziƙin ƙasar.

Sai dai a tattaunawar da BBC, Atiku ya ce cire tallafin man fetur da zai yi ya dogara ne da halin da ya tsinci ƙasar idan ya kama mulki.

Atiku ya ce: "Ko za ka cire tallafin man fetur, ba a lokaci ɗaya za ka yi shi ba , kuma sai ka kyautata rayuwar talakawa kafin ka fara cirewa a hankali".

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ƙasar.

Lamarin ya haifar da tashin farashin man fetur nan take, wani abu da ya shafi dukkanin fannonin rayuwa na al'ummar ƙasar.

Haka nan Najeriya na fama da tashin farashin kayan masarufi, wanda duk ake alaƙantawa da cire tallafin na man fetur.

Tun farko gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin samar da shirye-shirye da za su sauƙaƙa wa al'ummar ƙasar tsananin rayuwa, to amma sama da shekara uku bayan cire tallafin al'umma da dama a ƙasar na cewa ba su ga wannan tallafi ba.

Ministan Kuɗin Najeriya, Taiwo Oyedele ya ce an tara jimillar naira tiriliyan 15.8 daga kuɗaɗen tallafin man fetur ɗin tsakanin watan Yunin 2023 da Disamban 2025.

Ministan ya ce gwamnatin ta kashe kuɗaden ne ta hanyar raba wa jihohi da yin ƙarin albashi da alwus ɗin ma'aikata da biyan basukan da ake bin ƙasar da kuma gudanar da manyan ayyuka.

Wane ne Atiku Abubakar?

Atiku Abubakar gogaggen ɗan siyasa ne da ya shafe shekaru da dama yana jan zarensa. Hasalima yana daga cikin jiga-jigan mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP gabanin komawar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

An haifi Atiku Abubakar ranar 25 ga Nuwamban 1946 a Jihar Adamawa da ke Arewa Maso Gabas, kuma ya kasance jigon dan siyasa kuma hamshaƙin attajiri a Najeriya.

Ya mallaki katafariyar Jami'ar ABTI, wato American University of Nigeria a Jiharsa ta Adamawa.

Kamfaninsa na hada-hadar man fetur, mai suna Intels Nigeria Limited na hada-hada a kasashen Afirka da suka hada da Angola da Equatorial Guinea da Gabon da Sao Tome and Principe.

Atiku Abubakar ya tsunduma harkokin sisaya a 1989, kuma yana cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa na mulkin soji, Janar Shehu Musa Yar'adua.

Ya shiga jam'iyyu daban-daban tun da ya shiga harkokin siyasa.

Ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa a shekara ta 1999 ƙarƙashin jam'iyyar PDP, sai dai jim kaɗan bayan hakan wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na wancan lokaci Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Hakan ne ya sanya ya yi mataimakin shugaban ƙasa na shekara takwas, tare da Obasanjo, duk da cewa an samu saɓani tsakanin mutanen biyu kafin ƙarshen wa'adin mulkin.

Tun bayan sauka daga mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya tsaya takarar shugaban Najeriya sau biyar, inda a wasu lokutan ya fadi a zaɓen fitar da ɗan takara a 2011 da 2015, sannan ya fadi a babban zaɓen ƙasar a 2007, 2019 da kuma 2023.