Abu 4 da suka hana Najeriya magance matsalar garkuwa da mutane - C.G. Musa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Najeriya ta dade tana fama da matsalar satar dalibai daga makarantu, wani abu da ya samo asalin tun a watan Afrilun 2014, lokacin da mayakan Boko Haram suka sace kimanin dalibai 276 daga makarantar ‘yanmata ta Chibok a jihar Borno, wadanda har yanzu wasunsu ba su koma gida ba.

A halin da ake ciki yanzu ma akwai dalibai da dama da ke hannun ‘yanbindiga wadanda aka sace su daga cikin azuzuwansu a makarantar da suka je daukar darasi. misali shi ne yaran da aka dauke daga kauyen Mussa a jihar Borno, cikinsu har da yara ‘yan kasa da shekara uku, kamar yadda iyaye suka tabbatar.

Wannan lamari ya dade yana ci wa al’ummar Najeriya tuwo a kwarya, sai dai har yanzu hukumomin kasar sun kasa gano hanyar magance lamarin, domin kuwa ana ci gaba da samun irin wannan matsala akai-akai.

Shirin sashen Ingilishi na BBC ya zanta da tsohon babban hafsan sojin Najeriya kuma ministan taro na kasar, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, wanda ya lissafa wasu abubuwa da ya ce na daga cikin dalilan da suka sa aka kasa magance matslaar garkuwa da mutane a ƙasar.

To amma ministan tsaron ƙasar ya ce yanayin dazukan ƙasar da kuma faɗin kan iyakokinta na daga cikin abubuwan da ke kawo cikas wajen yaƙi da masu garkuwa da mutane.

Dazuka masu girma

''Najeriya na da dazuka masu faɗi da duhu, ga rashin netwok (sadarwar waya), wani abu da ke kawo cikas wajen samun bayanai a kan lokaci'', in ji tsohon babban hafsan sojin Najeriyar.

Ya ce ƙasar na da faɗin kusan murabba'in kilomita 923,000, sannan akwai matsalolin sadarwa da rashin samun bayanai cikin gaggawa a wasu yankuna.

Saboda haka ne gwamnatin ke neman taimakon ƙasashen da suka ci gaba a fannin fasahar tsaro, tare da sayen kayan aiki na zamani domin gano motsin masu aikata laifuka a ko'ina suke.

Dadaddun matsaloli da rikicin yankin Sahel

C.G. Musa ya kuma ce wasu matsalolin na gado ne kamar rikicin manoma da makiyaya da na ƙabilanci, waɗanda ya ce na daga cikin abubuwan da ke rura wutar rashin tsaro a ƙasar.

Ministan ya kuma ce matsalolin tsaron da ke addabar ƙasashen yankin Sahel na shafar Najeriya kai tsaye.

Ya ce wasu daga cikin mayaƙan da ke aikata ta'addanci a yankin suna shiga Najeriya, lamarin da ke ƙara wa hukumomin tsaro ƙalubale.

'Wata matsalar tsaron siyasa ce'

Ministan tsaron na Najeriya ya ce siyasa na taka rawa wajen ƙaruwar matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

Da aka tambaye shi game da abin da ke janyo matsalar rashin tsaro a Najeriya, ministan ya danganta wani ɓangare da siyasa.

''Abin da gwamnati ta lura da shi, a duk lokacin da ake gab da zaɓe ana samun ƙaruwar matsalolin tsaro'', in ji shi.

A cewarsa, wasu 'yan hamayya kan yi ƙoƙarin amfani da matsalolin tsaro wajen nuna gazawar gwamnati.

'Alfanun da Najeriya ta samu daga sojojin Amurka'

Ministan tsaron ya ce haɗin gwiwar da ƙasar ke yi da sojojin Amurka ya haifar da gagarumar nasara a yaƙi da matsalar tsaro da Najeriya ke yi.

A baya-bayan nan ne dai Amurka ta bayyana janye sojojinta daga Najeriya, wani abu da masana tsaro da yan ƙasar ke ganin bai dace ba a wannan lokaci da kasar ke ci gaba da fama da matsalar tsaro.

Sai dai ministan ya ce a sanadiyyar zuwan sojojin Amurkan Najeriya an kashe mutum na biyu mafi girman muƙami a ƙungiyar ISIS ta duniya, Abu-Bilal al-Mainuki tare da mayaƙansa kusan 200.

''Wannan aiki na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka samu sakamakon haɗin gwiwar da ke tsakanin sojojin Najeriya da na Amurka, musamman a fannin tattara bayanan sirri da horar da dakaru'', kamar yadda ya yi karin haske.

Ya ce wannan nasara ce da Najeriya za ta iya "bugun ƙirji" da ita a yaƙin da take yi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Duka sojojin Amurka ne za su fice daga Najeriya?

Dangane da ficewar sojojin Amurka daga Najeriya, ministan tsaron ya ce ba duka sojojin Amurka ba ne za su fice daga ƙasar.

Ya bayyana cewa dakarun Amurka kusan 200 da ake maganar ficewarsu, tawaga ce ta musamman da aka turo domin gudanar da aikin da ya kai ga kashe babban jagoran ISIS.

Ya ce waɗannan sojoji sun kammala aikinsu ne, shi ya sa za su koma ƙasarsu.

A cewar ministan, sojojin Amurka da ke Najeriya domin horar da dakarun ƙasar da kuma musayar bayanan sirri ba za su fice ba.

"Masu horo da tattara bayanan sirri za su ci gaba da zama"

Ya ce haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen biyu na ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

Kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

A farkon shekarar 2026 ne Amurka ta sanar da tura kimanin sojoji 200 zuwa ƙasar domin tallafa wa ƙoƙarin Najeriya na yaƙi da masu tayar da ƙayar baya ta hanyar horaswa da musayar bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar soji, tare da jaddada cewa sojojinta ba za su shiga filin daga ba.

Hakan ya zo ne bayan zargin da Amurka ta yi na cewa ana “yi wa kiristoci kisan-gilla” a kasar.

Sai dai a watan Yumi kasar ta Amurka ta tabbatar da janye wasu daga cikin sojojin nata, inda ta ce akwai saura wadanda za su ci gaba da zama a kasar domin ci gaba da bai wa sojojin Najeroya horo.

Ko Najeriya ta ci ribar zuwan sojojin na Amurka yadda ya kamata?

Dr Audu Bulama Bukarti, mai sharhi kan lamuran tsaro a nahiyar Afirka, ya shaida wa BBC cewa, ya na ganin kai tsaye ba za a ce kwalliya ta biya kuɗin sabulu ba a game da zaman sojojin a Najeriya.

Ya ce, "A gaskiya na dauka sojojin za su dauki lokaci mai tsayi a Najeriya, saboda sun ce sun zo domin taya Najeriya yaki da kungiyar Boko Haram, to amma mu a iya abin da muka sani babban aikin da suka yi a game da yaki da Boko Haram, kwalli daya daya ne tal, shi ne kashe Abu Bilal al Mainoki tare da wasu mukarrabansa."

"Kisan da aka yi wa wadannan 'yan Boko Haram din babban ci gaba ne kuma koma baya ne ga 'yan kungiyar," in ji shi.

Bukarti, ya ce,"mu a zatonmu shi ne su waɗannan sojoji na Amurka za su ci gaba da irin wadannan ayyuka har sai an gurgunta kungiyar Boko Haram kafin su ce sun janye."

Ya ce "a gaskiya daga mahangar Najeriya za a iya cewa kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba, to amma da an ce sun ci gaba da zama har sai an ci karfin 'yan Boko Haram da 'yan bindiga, to za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu."

"To amma daga bangaren Amurka fa, kwalliya ta biya kudin sabulu, domin tun daga lokacin da suka ce za su shigo, muka ce dama a wajen shugaban kasar siyasa ce don bukatarsa ta biya," in ji shi.

Masanin tsaron ya ce, "Yanzu ni ina ganin tun da sojojin na Amurka za su fice daga Najeriya, to abin da ya kamata shi ne, shi ne ita Amurkan da kawayen Najeriya wato kasashen yamma su sayar wa da Najeriya kayan aikin da ta ke bukata wajen yakar ta'addancin, sannankuma idan akwai wata kwarewa da suke da ita wadda babu a Najeriya to su taimaka."

Tun a watan Fabrairun 2026 ne, Amurka ta sanar da shirin tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horas da dakarun ƙasar dabarun yaƙi da ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya.

Matsalar tsaron da Najeriya ke fuskanta galibi hare-hare ne na sari-ka-noƙe ko yaƙin sunƙuru.

Galibi ƙungiyoyin ƴanbindigar da ke addabar Najeriya na da mafaka ne cikin dazuka ko tsaunuka ko ma cikin tafki, kamar Tafkin Chadi da ake tunanin Boko Haram da ISWAP na ciki.

Ita kuwa rundunar sojin Amurka na da ƙwarewa sosai a wannan fanni, domin suna shiga wurare masu sarƙaƙiya su kuma yi nasara.